Sunday, April 12
Shadow
Majalisar Dattawa ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Majalisar Dattawa ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Duk Labarai
Majalsiar Dattawa ta amince da dokar ta-ɓaci da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ayyana a kan jihar Rivers a ranar Talata. Majalisar dai ta shiga tattaunawar sirri bayan da shugaban majalisar Godswill Akpabio ya karantar wasiƙar a zauren. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ne ya karanta buƙatar shiga tattaunawar ta sirri bisa dogaro da doka mai 135 ta kundin majalisar. Shugaban marasa rinjaye, Sanata Abba Moro ne ya amince da shiga ganawar sirrin. Da ma dai majalisar wakilai ta amince da wannan dokar ta ta-ɓaci a ranar Alhamis.
Hukumar Nimet ta gargaɗi kan ɓullar cutar sanƙarau a Najeriya

Hukumar Nimet ta gargaɗi kan ɓullar cutar sanƙarau a Najeriya

Duk Labarai
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya Nimet ta yi gargaɗin cewa wasu jihohin arewacin ƙasar na ƙara fuskantar barazanar ɓarkewar cutar sanƙarau. Nimet a cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, ta ce jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara da Katsina da Kano da Jigawa da Bauchi da Yobe da Gombe da kuma Borno su ne suka fi fuskantar barazanar. Hukumar ta kuma ce alamomin cutar sanƙarau sun haɗa da zazzaɓi mai zafi da ciwon kai mai tsanani da riƙewar wuya da amai, sai rashin son kallon haske da ruɗewa da kuma ƙuraje. Nimet ta kuma ƙara da cewa ana iya kamuwa da cutar da hanyar mu'amula da masu ɗauke da cutar da kuma shiga cunkoso, inda ta buƙaci alumma su yi rigakafi su wanke hannu su kuma gujewa kusantar masu cutar su kuma rufe bakinsu da hanci. Hukumar ta kuma yi kira ga alumma da...
Har yanzu Hoton Gwamna Fubara na rataye a fadar Gwamnatin jihar Rivers duk da dakatar dashi da shugaba Tinubu yayi

Har yanzu Hoton Gwamna Fubara na rataye a fadar Gwamnatin jihar Rivers duk da dakatar dashi da shugaba Tinubu yayi

Duk Labarai
Wanda shugaban kasa, Bola Ahmad ya baiwa rikon kwaryar gwamnan jihar Rivers, Vice Admiral Ibokette Ibas ya koma jihar ya shiga gidan gwamnatin jihar bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya rantsar dashi a Abuja. Saidai wani abu da aka lura dashi shine har yanzu hoton Fubara na nan a sagale a matsayin gwamnan jihar a Ofishin gwamnan.
Kuma Dai: Sanata Natasha Akpoti ta je kafar Skynews ta kasar Ingila tawa Sanata Godswill Akpabio tonon silili

Kuma Dai: Sanata Natasha Akpoti ta je kafar Skynews ta kasar Ingila tawa Sanata Godswill Akpabio tonon silili

Duk Labarai
Sanata Natasha Akpoti ta je kafar Skynews ta kasar Ingila inda ta yiwa Sanata Godswill Akpabio tonon silili. A can ma dai ta sake bayyana yanda Sanata Godswill Akpabio ya nemeta da lalata. Ta musanta ikirarin Majalisar Dattijai na cewa an dakatar da itane saboda rashin biyayya ga dokokin majalisar inda tace me yasa sai da ta gabatar da korafi akan sanata Godswill Akpabio ne sannan za'a dakatar da ita? Sanata Natasha ta bayyana cewa ta yi ta kai korafi dan neman yiwa mutanenta aiki amma sai sanata Godswill Akpabio yaki amincewa. Tace har mijinta saboda abokin Sanata Godswill Akpabio ne ya rika rokonsa akan ya amince da wasu kudirori data kai majalisar amma ya kiya sai yace sai nan gaba.
Kalli Hotuna:Yanda Wani dan Siyasa a jihar Kogi ya rabawa mutanen mazabarsa tayar mashin dan su dogara da kansu

Kalli Hotuna:Yanda Wani dan Siyasa a jihar Kogi ya rabawa mutanen mazabarsa tayar mashin dan su dogara da kansu

Duk Labarai
Wani Dan siyasa a jihar Kogi wanda dan majalisa ne me suna, Hon. Idowu ibikunle ya dauki hankalin Duniya bayan da aka ga yana rabawa mutanen mazabarsa Tayar mashin dan su dogara da kansu. https://www.youtube.com/watch?v=GRU9hUEaYq8&pp=0gcJCfcAhR29_xXO Abin dai ya baiwa mutane da yawa mamaki inda suke tambayar ta yaya tayar mashin zata taimaki mutum.
Da Duminsa: A karshe dai majalisar Wakilai ta amince da dakatarwar da Shugaba Tinubu yawa Gwamnan jihar Rivers

Da Duminsa: A karshe dai majalisar Wakilai ta amince da dakatarwar da Shugaba Tinubu yawa Gwamnan jihar Rivers

Duk Labarai
Rahotanni daga majalisar tarayya na cewa, majalisar Dattijai ta amince da dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yawa gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara. Majalisar data samu zaman 'yan majalisar su 243 ta yiwa dokar garambawul. Ta bayar da shawarar a kafa kwamiti wanda zai tabbatar da samun zaman lafiya a jihar ta Rivers. Sannan kuma a baiwa majalisar ta tarayya karbar aikin gudanar da majalisar jihar Rivers na tsawon watanni 6 da aka dakatar da ita.
Da Duminsa:Atiku, El-Rufai, Peter Obi, Rotimi Amaechi sun hada kai dan yakar Tinubu a zaben 2027

Da Duminsa:Atiku, El-Rufai, Peter Obi, Rotimi Amaechi sun hada kai dan yakar Tinubu a zaben 2027

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Rahotannin da muke samu na cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da sauran manyan mutane na APC sun hada kai dan ganin sun kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 me zuwa. A cikin hadakar akwai kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, wanda Yunusa Tanko ya wakilta, akwai kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal. Wadand...
Wasu na ta tambayar wai Ina Kwankwasone, kowane babban dan Adawa yayi Allah wadai da dakatar a Gwamnan Rivers amma har yanzu shi bai ce komai akai ba

Wasu na ta tambayar wai Ina Kwankwasone, kowane babban dan Adawa yayi Allah wadai da dakatar a Gwamnan Rivers amma har yanzu shi bai ce komai akai ba

Duk Labarai
A yayin da siyasar Najeriya ta mayar da hankali kan dakatar da gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara, manyan 'yan Adawa na ta Allah wadai da wannan mataki na shugaban kasa. Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasiru El-Rufai, da sauran manyan 'yan Adawa duk sun fito suna ta Allah wadai da wannan mataki, saidai ba'a ji duriyar Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ba. Daya daga cikin wadanda suka bayyana irin wannan ra'ayi shine Comrade Adnan. Ya bayyana cewa, duk da shirun Kwankwaso akan lamari irin wannan amma haka mutane ke kiransa da Jagora. Abin dai jira a gani shine ko Kwankwaso zai yi magana akan lamarin.
Karuwanci ya kaita jihar Legas>>Hadimin Shugaban kasa ya zargi matashiya ‘yar Bautar kasa data soki Shugaba Tinubu

Karuwanci ya kaita jihar Legas>>Hadimin Shugaban kasa ya zargi matashiya ‘yar Bautar kasa data soki Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Hadimin shugaban kasa, Tope Fasua ya zargi matashiya me bautar kasa,  ‘Raye’ Uguamaye da cewa Karuwancine ya kaita jihar Legas. Wannan zargi nashi na zuwane bayan da sunan matashiyar ya yadu sosai a kafafen sadarwa bayan da ta soki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. A sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Tope yace matashiyar ta je legas ne dan samun rabonta na Naira Biliyan N661. Kwanannan ne aka bayyana cewa mazan Legas sun kashe Naira Biliyan N661 wajan biyan bukatarsu da karuwai. A baya dai, wani hadimin shugaban kasar me suna Temitope Ajayi ya nemi a kaddamarwa matashiya Raye da hukuncin kisa saboda sukar shugaban kasar. Saidai daga baya ya fito ya bayyana cewa, shi ba haka yake nufi ba.