Hukumar raba arziƙin ƙasa ta nemi sake duba ƴancin kashe kuɗin ƙananan hukumomi a Najeriya
Hukumar rarraba arziƙin ƙasa (RMAFC) ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba ƴancin kashe kuɗin ƙananan hukumomi 774 da yadda ake aiwatar da sabuwar dokar man fetur (PIA).
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ɗauke da sa hannun shugaban hukumar, Dr. Muhammed Shehu, da Sakatarenta, Injiniya Joseph Okechukwu Nwazeb.
hukumar ta fitar da sanarwar ne bayan taron horarwar kwana uku da aka gudanar a Uyo, Jihar Akwa Ibom inda taron ya mayar da hankali kan inganta tsarin kuɗi da rarraba albarkatu a Najeriya.
Sanarwar ta ce "Ya zama dole a riƙa biyan kuɗaɗen kananan hukumomi kai tsaye daga asusun tarayya ba tare da tsoma bakin gwamnatocin jihohi ba."
Haka kuma, hukumar ta buƙaci a sauya Sashe na 162(2) na kundin tsarin mulki domin sanya lokaci na musamman da s...








