Talauci na karuwa a Najeriya, Musamman a kauyuka>>Inji Bankin Duniya
Bankin Duniya ya bayyana cewa, Talauci na karuwa a Najeriya musamman a cikin kauyukan Kasar.
Bankin yace kaso 75.5 na mazauna kauyuka na fama da Talauci inda suke rayuwa a kasa da layin Talauci na Duniya.
Bankin ya bayyana hakane a rahoton da ya fitar na watan Afrilun shekaar 2025.
A watan da ya gabata ne dama bankin ya bayyana cewa, 'Yan Najeriya da yawa zasu fada cikin matsanancin Talauci nan da shekaru 5 masu zuwa.
Rahotan yace a biranen Najeriya kuma kaso 41.3 cikin 100 ne na mutane ke rayuwa a kasa da layin Talauci.
Layin Talauci dai an dorashi ne akan Mutum ya rika rayuwa akan dala akalla $2.15 kwatankwacin Naira Dubu 3440 kullun, duk wanda yake rayuwa a kasa da wannan kudi a kullun to yana cikin wanda ake kallo a matsayin Matalauta.
Rahoton yace Talaucin yafi yawa ...








