GWAMNATIN JIHAR KEBBI TA AURARDA ‘YA’YA MATA 300 (DA MAZAJENSU) KARO NA 2 !
A jiya Alhamis ne (27/02/2025) Gwamnatin Jihar Kebbi karkashin jagorancin zababben Gwamnan Jihar (Comr. Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu) ta sake daurawa mata 300 aure da mazajensu , tareda duk abinda ya dace ayi musu na karramawa (auren gata kenan).
Wannan kudurin (na shirin auren gata) mai girma Gwamnan Jihar Kebbi ya sanya shi a ransa , cewa da ikon Allah zai yi iya na shi kokari don ganin gwamnatinsa ta ci gaba da bada irin wannan gudummuwa musamman ga marasa karfi , don taimakawa al'umma wajen rage yawan gwagware da kuma rage yaduwar alfasha a cikin al'umma.
Ko shakka babu wannan ba karamin alkhairi bane a cikin al'umma musamman idan sun gano hadarin da ke cikin yawaitar mabukata aure mata/maza kuma ba suda halin yin auren , a irin wannan lokacin komai na iya faruwa a kowane bangar...








