Friday, January 16
Shadow
Da Duminsa: Kakakin Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya halarci zaman majalisar na yau yayin da ake rade-radin cewa ya yanke Jiki ya Fhàdì an garzaya dashi Asibiti

Da Duminsa: Kakakin Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya halarci zaman majalisar na yau yayin da ake rade-radin cewa ya yanke Jiki ya Fhàdì an garzaya dashi Asibiti

Duk Labarai
Rahotanni daga majalisar Dattijai sun tabbatar da cewa, kakakin majalisar, Godswill Akpabio ya halarci zaman majalisar na yau. Hakan na zuwane bayan da rahotanni suka watsu cewa ya yanke jiki ya fadi an garzaya dashi asibitin kasar Landan. Akpabio ya koka da matsalar watsuwar labaran karya inda yace suna da wahalar magancewa. Majalisar dai ta nemi hukumar ofishin me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, NSA su binciki yanda aka yi labarin ya yadu.
Kalli Bidiyon: A karin Farko an hango Jirgin saman sojojin Najeriya, C-130 dake ajiye a filin jirgin kasar Burkina Faso

Kalli Bidiyon: A karin Farko an hango Jirgin saman sojojin Najeriya, C-130 dake ajiye a filin jirgin kasar Burkina Faso

Duk Labarai
An Hango jirgin saman sojojin Najeriya C-130 dake ajiye a filin jiragen saman kasar Burkina Faso. Jirgin dai na dauke da sojoji 11 ne na Najeriya da hukumomin Najeriya suka ce ya samu tangarda a hanyarsa ta zuwa kasar Portugal ya sauka a kasar ta Burkina Faso. Saidai hukumomin kasar Burkina Faso sun zargi akwai wata maqarqashiya game da saukar jirgin a kasarsu. https://twitter.com/GallantDaletian/status/2000892186674528536?t=yxeUTLLX9UFobJ9bdyftuw&s=19
Ji yanda na kusa da Buhari suka so a tsayar da Sanata Ahmad Lawal takarar shugaban kasa a APC

Ji yanda na kusa da Buhari suka so a tsayar da Sanata Ahmad Lawal takarar shugaban kasa a APC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, na kusa da Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari sun yi kokarin ganin an tsayar da Sanata Ahmad Lawal takarar shugaban kasa a jam'iyyar ba Tinubu ba. Rahoton yace wadannan mutane sun rubuta takardar Boge inda suka ce daga shugaban kasa ne suka mikawa shugaban 'yansanda da shugaban DSS suka basu Umarnin su tabbatar Sanata Sanata Ahmad Lawal ne ya zama dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC. Saidai shugaban 'yansandan a wancan lokacin ya nemi tabbatar da wannan umarni kai tsaye daga wajan shugaba Buhari inda Buharin yace ba gaskiya bane. Hakan ya bayyana ne a sabon Littafin da aka rubuta da ya kunshi tarihin rayuwar tsohon shugaban kasar wanda aka kaddamar a fadar shugaban kasa jiya.
Nasan Comedy(Wasan Barkwanci) Hàràmùn ne amma ba zan daija yi ba>>Sale Naci

Nasan Comedy(Wasan Barkwanci) Hàràmùn ne amma ba zan daija yi ba>>Sale Naci

Duk Labarai
Dan wasan barkwanci, Sale Naci ya bayyana cewa yasan abinda yake yi Haramun ne amma ba zai taba dainawa ba. Yace hakane bayan da wani Boka yace zai bashi tallar bokancin da yake ya tayashi tallatawa zai biyashi daga Miliyan 10 zuwa sama. Saidai Sale Yace ba zai karbi wannan tallar ba. https://www.tiktok.com/@sulenaci_/video/7584114589726559496?_t=ZS-92GY12TS1s9&_r=1
Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda wani Ladani ya rika nina Maqogoronsa yayin da yake Alhinin Abinda ya faru da ladanin Hotoro

Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda wani Ladani ya rika nina Maqogoronsa yayin da yake Alhinin Abinda ya faru da ladanin Hotoro

Duk Labarai
Wannan wani Ladani ne da ya nuna Makogoronsa a yayin da yake Alhinin rasuwar Ladanin Hotoro wanda aka cirewa Makogoro. Ladanin ya baiwa 'yan uwansa Ladanai shawarar su rika shiga Masallaci da makami yayin da suka je kiran Sallah. Hakanan kuma ya Yace Ladanai su rika kulle kofofin Masallaci yayin da suke kiran Salah. https://www.tiktok.com/@shugaba_tv1/video/7584208558418398485?_t=ZS-92GRMDQt7Vg&_r=1