Da Duminsa: An bayyana sunayen sojoji 16 da suka yi yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin Mulki, Duk ‘yan Arewa ne
Rahotanni daga Sahara Reporters sun bayyana sunayen sojojin da ake zargi da yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Juyin Mulki.
Sojojin dai guda 16 ne duk da yake sabon rahoto daga Daily Trust yace an samu karin sojoji 26 da aka kama.
Ga jadawalin sunayen sojojin da jihohin da suka fito:
Akwai Lieutenant Commander B Abdullahi.
Sai Brigadier General Musa Abubakar Sadiq (N/10321) wanda shine ake zargin shugaban tawagar Yunkurin Juyin Mulkin.
Sai Colonel M.A. Ma’aji (N/10668). Banufe ne daga jihar Naija.
Lieutenant Colonel S. Bappah (N/13036). Dan asalin Jihar Bauchi ne.
Lieutenant Colonel A.A. Hayatu (N/13038). Dan jihar Kadunane.
Sai Lieutenant Colonel P. Dangnap (N/13025) dan jihar Filato ne.
Lieutenant Colonel M. Almakura (N/12983). Dan jihar Nasarawa ne...








