Thursday, March 5
Shadow
Tsadar rayuwa tasa yanzu da yawan ‘yan Najeriya basa iya sayen magunguna>>Kungiyar masu Hada magunguna ta Najeriya

Tsadar rayuwa tasa yanzu da yawan ‘yan Najeriya basa iya sayen magunguna>>Kungiyar masu Hada magunguna ta Najeriya

Duk Labarai
Kungiyar masu hada magunguna ta koka da cewa tsadar rayuwa tasa yanzu mutane da yawa basa iya sayen magunguna. Kungiyar ta alakanta hakan da tashin farashin magunguna da kayan hadasu da karyewar farashin dala da dogaro da shigo da kayan hada magunguna da shigo da magungunan daga kasashen waje. Kungiyar ta bayyana hakane a wajan wani taro da aka yi a A Legas na masu ruwa da tsaki a cikinta.
ALHAMDULILLAH: Sojojin Nijeriye Sun Aika Da Rikakken Dan Ta’àďďan Da Ya Addabi Jihar Katsina, Sani Wala Burki Zuwa Barzahu

ALHAMDULILLAH: Sojojin Nijeriye Sun Aika Da Rikakken Dan Ta’àďďan Da Ya Addabi Jihar Katsina, Sani Wala Burki Zuwa Barzahu

Duk Labarai
ALHAMDULILLAH: Sojojin Nijeriye Sun Aika Da Rikakken Dan Ta'àďďan Da Ya Addabi Jihar Katsina, Sani Wala Burki Zuwa Barzahu. Jami'an sojojin Nijeriya sun samu nasara haĺaķa Sani Wala Burki daya daga cikin manyan 'ýan ta'aďďan da suka addabi jihar katsina. Wala Burki ya gamu da ajalin sa ne a yau Asabar a wajen jami'an tsaro na haɗin guiwa a yayin wata arangama da suka yi. Wala Burki shine ya addabi ƙananan hukumomin Safana da Batsari dake jihar Katsina. Me za ku ce?
Hotuna: Wannan matashiyar ta samu tallafi daga mutane da yawa bayan da ambaliyar ruwa ta shafeta a jihar Borno

Hotuna: Wannan matashiyar ta samu tallafi daga mutane da yawa bayan da ambaliyar ruwa ta shafeta a jihar Borno

Duk Labarai
Wannan matashiyar daga jihar Borno ta samu tallafi daga mutane da yawa bayan da ambaliyar ruwa ta shafeta daga jihar Borno. A wani faifan bidiyonta daya watsu sosai a kafafen sada zumunta, an ga matashiyar tana kokawa da irin illar da ambaliyar ruwan ta musu. Hakan yawa mutane da yawa suka sha Alwashin tallafa mata inda tuni wasu suka bayyana cewa sun fara aika mata da tallafin kudi. Ambaliyar ruwan dai ta jefa mutane cikin halin rashin tabbas inda wasu dole suka bar gidajensu suka koma kodai wajan 'yan uwa ko suka shiga halin rayuwar rashin tabbas.
Ba Gaskiya Ba Ne Maganar Da Sheíkh Sani Yahaya Jingir Yayi, Saboda Bamu Wallafa Labarin Dake Cewa Tinubu Bai San An Ƙara Farashin Man Fetur Ba, Idan Kuwa Mun Wallafa Ya Bamu Hujja, Martanin Jaridar Daily Trust Ga Shiekh Jingir

Ba Gaskiya Ba Ne Maganar Da Sheíkh Sani Yahaya Jingir Yayi, Saboda Bamu Wallafa Labarin Dake Cewa Tinubu Bai San An Ƙara Farashin Man Fetur Ba, Idan Kuwa Mun Wallafa Ya Bamu Hujja, Martanin Jaridar Daily Trust Ga Shiekh Jingir. A baya dai malam ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima basu sani ba aka kara kudin man fetur. Inda malamin yayi ikirarin cewa, jaridarta Daily Trust ce ta ruwaito hakan. Lamarin ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sadarwa. Inda da yawa suke ganin cewa bai kamata malamin yayi wannan magana ba. Me zaku ce ?
‘Yan kasuwar man fetur sun ce man fetur dina yayi arha da yawa basa samun ribar da suke so>>Dangote

‘Yan kasuwar man fetur sun ce man fetur dina yayi arha da yawa basa samun ribar da suke so>>Dangote

Duk Labarai
Aliko Dangote ya koka da cewa, 'yan kasuwar man fetur sun koka da cewa man fetur dinsa yayi arha da yawa. Dangote ya bayyana hakane ta bakin wakilin kamfaninsa,me suna Devakumar Edwin. Ya kara da cewa,tuni 'yan kasuwar suka aikawa da shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu korafi akan wannan lamari. Yace da kyar suke samun suna sayar da tankar Gas 29 saboda 'yan kasuwar basa son saye, yace dan haka dole suke fitar da sauran zuwa kasashen waje. Kamfanin dai na Dangote ya rage farashi daga Naira 1200 zuwa Naira 1000 zuwa Naira 900 akan kowace lita.