Friday, July 10
Shadow
Kalli Bidiyo: Rawar da Ali Nuhu ya tika da Rahama Sadau ta sa ana ta cece-kuce inda wasu ke cewa, wai yaushe zai girma?

Kalli Bidiyo: Rawar da Ali Nuhu ya tika da Rahama Sadau ta sa ana ta cece-kuce inda wasu ke cewa, wai yaushe zai girma?

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu Sarki ya dauki hankula sosai a wajan bikin Arewa Turnup da Rahama Sadau ta shirya. Babban abinda ya dauki hankalin mutane shine yanda Ali Nuhu da Rahama Sadau suka rika rawa tare da Umar M. Shariff. Ali Nuhu ya saki jikinsa sosai yayi rawa ba tare da shakka ba. Hakan yasa mutane ke cewa wai yaushe zai girma ne? https://www.tiktok.com/@goldenbackup1/video/7474538141509078277?_t=ZM-8u9bdVISxtd&_r=1 Ali Nuhu dai ya saba rawa irin haka, saidai mutane sun kasa sabawa da ganinsa yana rawar inda a duk sanda yayi sai an yi magana.
Wani mùtùm ya mùtù a kokarin dakko wayarsa data fada rijiya

Wani mùtùm ya mùtù a kokarin dakko wayarsa data fada rijiya

Duk Labarai
Wani mutum me suna Sunday Jimoh a jihar Ogun ya mutu a kokarin dakko wayarsa data fada rijiya. Mutumin me shekaru 31 na zaunene a Laditan dake yankin Oja-Odan na jihar, kuma lamarin ya farune ranar 22 ga watan Fabrairu da misalin karfe 10: 00 na safe. Kakakin 'yansandan jihar, CSP Omolola Odutola ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi. Wata mata Kabiru Aladeshayi Ayigbere ce ta kaiwa 'Yansandan korafi akan lamarin inda tace an yi kokarin hana Jimoh shiga rijiyar amma ya nace sai ya shiga. Omolola yace sun je wajan inda aka ciro gawar mamacin kuma an yi bincike babu wata alamar duka a jikinsa wanda hakan ya tabbatar da cewa mutuwa yayi ta Allah da Annabi. Danginsa sun bukaci a basu gawarsa su binneshi kamar yanda addinin musulunci ya tanada kuma an...
Wata Sabuwa: Masanin Kimiyya yace mafi yawan mutane zasu so yin Luwadi da Madigo idan suka samu damar yin hakan a bincikensa

Wata Sabuwa: Masanin Kimiyya yace mafi yawan mutane zasu so yin Luwadi da Madigo idan suka samu damar yin hakan a bincikensa

Duk Labarai
Wani masanin kimiyya a kasar Ingila me suna Dr Jason Hodgson ya yi ikirarin cewa, mafi yawan mutane na da son aikata luwadi da madigo idan suka samu damar yin hakan. Ya bayyanawa jaridar mailonline cewa duk da yake wadanda suka fito suka bayyana cewa su 'yan Luwadi da madigo ne basu da yawa amma akwai masu irin wannan dabi'ar da yawa dake boyewa. A cewarsa, idan wasu suka samu dama, suma zasu so aikata irin waccan masha'a. Yana bayyana cewa, wannan dabi'a ce ta mafi yawan mutane tsakanin maza da mata wadda ke cewa bisexual watau mace tana son namiji sannan tana son mace 'yar uwarta, hakanan namiji yana son mace amma kuma yana son namiji dan uwansa. Saidai da yawa ko da a cikin Turawan sun karyata wannan masanin kimiyya inda suka ce kawai yana son yada badala ne kuma abinda ya f...
Shari’ar da ake min yaudarace, Gara ma in mùtù a daure kawai, ba zan kara zuwa kotu ba>>Nnamdi Kanu ya magantu

Shari’ar da ake min yaudarace, Gara ma in mùtù a daure kawai, ba zan kara zuwa kotu ba>>Nnamdi Kanu ya magantu

Duk Labarai
Shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu dake daure ake zarginsa da cin amanar kasa ya sha Alwashin ba zai kara zuwa kotu ba. Kanu ya bayyana hakane inda yace shari'ar da ake masa yaudara ce kawai. Kanu yace dalili daya zai sashi ya ci gaba da zuwa kotu shine idan za'a gurfanar dashi a gaban kotun dake da cikkakken ikon a kudin tsarin mulkin Najeriya. Kanu ya kawo dalilai da yawa da yace yana ga kotunan da ake kaishi a yanzu ba zasu iya masa hukuncin da ya dace ba.
Shugaba Tinubu ya kaddamar da titin Legas zuwa Ibadan da aka kammala

Shugaba Tinubu ya kaddamar da titin Legas zuwa Ibadan da aka kammala

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar da titin Legas zuwa Ibadan da aka kammala wani sashe inda ake ci gaba da aiki a wani sashe na titin. A yayin kaddamarwar, Shugaba Tinubu ya bayyana muhimmancin Titi wajan karfafa tattalin arzikin kasa. Ya bayyana cewa, Gwamnatinsa zata yi kaimi wajan tabbatar da samar da tituna da zasu hada birane da karkara dan ci gaban tattalin arzikin kasa. Shugaban kasar wanda gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya wakilta ya bayyana cewa, yana kuma jinjinawa ministan ayyuka, Dave Umahi kan jajircewarsa.
Hukumar ‘yansandan Najeriya zata hukunta ‘yansanda masu cin zalin Direbobi suna karbar musu kudi a jihohin Inyamurai

Hukumar ‘yansandan Najeriya zata hukunta ‘yansanda masu cin zalin Direbobi suna karbar musu kudi a jihohin Inyamurai

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya zata hukunta 'yansanda da aka samu da cin zalin direbobi ta hanyar karbar musu kudi a yankunan jihohin Inyamurai. Shugaban hukumar 'yansanda ta PSC, DIG Hashimu Argungu rtd ne ya bayyana hakan inda yace ba zasu yadda da take hakkin bil'ada da ake zargin 'yansandan da aikatawa ba. DIG Hashimu Argungu rtd yace zasu fara aiwatar da hukuncin da aka tanadar akan irin wannan laifi na korar duk dansandan da aka samu da aikata laifin. Argungu yayi maganane a wajan taron da ake yi akan lamarin tsaro da kare hakkin bil'adama a jihar Enugu. Argungu wanda Mr. Ikechukwu Ani ya wakilceshi yace sun jima suna gargadin 'yansanda da su daina aikata irin wannan laifi amma sun kiya. Yace dan haka zasu fara daukar mataki.
Kalli Hotunan Ango da Amarya da suka jawo cece-kuce

Kalli Hotunan Ango da Amarya da suka jawo cece-kuce

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wadannan hotunan wasu sabbin ma'aurata ne da suka jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta musamman saboda karamin jiki da amaryar ke dashi. Saidai Binciken da hutudole.com yayi, ya fahimci cewa matar shekarunta 30 kuma har ma ta kammala jami'a, kawai dai bata da jikin girma ne. Muna musu fatan zaman lafiya da zuri'a dayyiba.
Dalilin da yasa na kkàshè babban abokina kuma aminina wanda muka taso tare tun muna yara watau Mamman Batsa>>IBB ya magantu

Dalilin da yasa na kkàshè babban abokina kuma aminina wanda muka taso tare tun muna yara watau Mamman Batsa>>IBB ya magantu

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasar mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida yayi bayanin dalilin da yasa ya kashe babban abokinsa da suka taso tare watau Mamman Batsa. Babbangida yace yana sane da cewa, Mamman Batsa tun suna yara yana kishi da ci gaban da yake samu, yace amma duk da haka ko da ya zama shugaban kasa, sai da ya bashi ministan babban birnin tarayya Abuja, duk da yake cewa ba tare dashi akawa Buhari juyin mulki ba. Babangida yace ko da suna makaranta da aka bashi Shugaban dalibai, Mamman Batsa bayawa umarninsa biyayya inda yakan rika ce masa ai ba wani abun azo a gani bane dan mutum ya zama shugaban dalibai. Yace hakanan da suka shiga aikin soja ma ya rika masa hassada. Yace A lokacin da yake shugaban kasa, bincike ya tabbatar da cewa Mamman Batsa ya shirya kifar da gwamna...
Farashin Giya, dana taba sun kara tsada fiye komai a Najeriya>>NBS

Farashin Giya, dana taba sun kara tsada fiye komai a Najeriya>>NBS

Duk Labarai
Hukumar Kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana cewa, farashin lemun kwalba, dana giya, dana taba dana sauran kwayoyi ne yafi kowane tashi a cikin kayan da ake amfani dasu a Najeriya. Farashin wadannan kayayyaki kamar yanda NBS ta bayyana ya tashi da kaso 14.80 a cikin watan Janairu da ya gabata. NBS tace kayan da suka fi tsada na biyu shine farashin kudin haya da na cin abinci a gidajen cin abinci a fadin kasarnan wanda ya tashi da kaso 14.14. Abinda ke biye musu shine farashin kayan sawa, da tafiye-Tafiye, da takalma, wanda suma suka yi tashi sama.
Watanni 7 bayan da Kotun koli tace a rika baiwa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye ba tare da sun bi ta hannun gwamnoni ba har yanzu ba’a aiwatar da hukuncin ba

Watanni 7 bayan da Kotun koli tace a rika baiwa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye ba tare da sun bi ta hannun gwamnoni ba har yanzu ba’a aiwatar da hukuncin ba

Duk Labarai
Watanni 7 kenan tun bayan da kotun koli ta yi hukunci inda tace a daina baiwa gwamnoni kudaden kananan hukumomi inda tace a rika baiwa kananan hukumomin kudadensu kai tsaye. Saidai har yanzu gwamnatin tarayya bata fara aiwatar da wannan hukunci ba, wanda wasu masana na ganin hakan kin girmama bangaren shari'a ne ganin cewa kotun koli itace kotu mafi girma a kasarnan. Dama dai tun a wancan lokaci, Gwamnoni sun shigar kara inda suka nemi dakatar da hukuncin amma basu yi nasara ba. A ranar July 11, 2024 ne kotun kolin karkashin jagorancin me shari'a Lateef Fagbemi SAN ta yi wannan hukunci. Gwamnatin tarayya a kokarin kawo tsaiko wajan aiwatar da wannan hukunci ta baiwa gwamnatocin jihohi watanni 3 su gudanar da zabukan kananan hukumomi dan fara aiwatar da wannan doka amma shiru ka...