Tuesday, December 16
Shadow
Kasar Saudiyya ta zuciya akan Israela inda tace Israelan na aikatawa Falas-dinawa kisan kare dangi

Kasar Saudiyya ta zuciya akan Israela inda tace Israelan na aikatawa Falas-dinawa kisan kare dangi

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Kasar Saudiyya ta yi Allah wadai da kisan da kasar Israela kewa Falas-dinawa. Ta bayyana cewa Israelan nawa Falas-dinawan kisan kare dangi. Israela ta kashe mutane akalla 21 a harin data kai kan al-Mawasi dake Rafah. Hakan ya zo ne bayan da ta kashe mutane sama da 40 a harin data kai kan wani sansanin a Rafah ranar Labadi. Ma'aikatar harkokin waje ta Kasar Saudiyya tace Israela ce ke da alhakin koma menene ke faruwa a Rafah. Kuma ta yi kiran kasashen Duniya da su dauki matakin hana wannan kisa da Israela kewa Falasdinawan.
An kashe jimullar Mutane 4,416 sannan an yi garkuwa da 4,334 a shekara 1 da Tinubu yayi yana mulkin Najeriya

An kashe jimullar Mutane 4,416 sannan an yi garkuwa da 4,334 a shekara 1 da Tinubu yayi yana mulkin Najeriya

Siyasa
Rahotanni sun bayyana cewa, an kashe jimullar mutane 4,416 da yin garkuwa da guda 4,334 a shekara 1 da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi yana mulki. Wata gamayyar masu fafutukar kasa da kasa da kuma Najeriya su 84 ne suka fitar da wannan rahoto. Rahoton yace kungiyoyin basu saka abubuwan dake faruwa na fashi da makami da sauran laifuka ba. Sunce wannan lamari ya sanya 'yan Najeriya sun rasa 'yancin rayuwa me inganci da kuma rayuwa cikin walwala. Kungiyar tace ci gaba da wannan lamari ya jefawa 'yan Najeriya tsoro da fargaba da rashin tabbas. Kuma sun ce idan gwamnatin Tinubu bata dauki mataki kan lamarin ba, suna daf da fitar da rahoton yanke tsammani akanta. Sunce suna jawo hankalin gwamnatin Tinubu data yi kokari wajan sauke nauyin dake kanta na kare rayuwa da dukiy...
Kamin ka samu mutum 1 da baya son mahaifina sai ka samu 10 masu sonsa>>Inji Dan Sarki Muhammad Sanusi II, Ashraf Sanusi

Kamin ka samu mutum 1 da baya son mahaifina sai ka samu 10 masu sonsa>>Inji Dan Sarki Muhammad Sanusi II, Ashraf Sanusi

Kano
Dan gidan me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, Ashraf Sanusi ya bayyana cewa kamin ka samu wanda baya son mahaifinsa guda daya, sai ka samu mutum 10 dake sonsa. Dan haka yace wanda ke son mahaifinsa sun fi wanda basa sonshi yawa. Ya rubuta hakane a shafinsa na sada zumunta. Saidai an jawo hankalinshi kan cewa, ya daina biyewa makiya, kuma ya amsa da ya gode. "You hate him if he talks, you hate him if he’s silent, you hate him if he’s happy, you hate him if he’s asleep. It’s only God that can help you and your hate. But for every one of you there’s 10 of us supporting and loving him, you’re outnumbered and sadly you’ve already lost."
Kuma Dai:EFCC ta sake kama wani matashi saboda lika Kudin Naira a wajan biki a jihar Gombe

Kuma Dai:EFCC ta sake kama wani matashi saboda lika Kudin Naira a wajan biki a jihar Gombe

Gombe
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta EFCC ta sake kama wani matashi a jihar Gombe me suna Zachariyya Muhammad saboda yin likin kudin Naira a wajan wani biki. An kama shine ranar Asabar, 24 ga watan Mayu bayan ya lika kudin Naira dari 200 a wajan wani bikin G-Connect. Ko da aka nuna masa bidiyonsa yana likin, ya amsa cewa lallai shine, hukumar zata gurfanar dashi a gaban kotu. A baya dai EFCC ta kama mutane da yawa a jihar Gombe shima.
Hoton Sojan Najeriya da aka kama ya saci harsasai

Hoton Sojan Najeriya da aka kama ya saci harsasai

Tsaro
Hukumomin soji dana CJTF a jihar Borno sun kama wani soja da laifin satar harsasai. An kama sojan ne me suna Corporal Francis Bako a tashar motar Kano dake Maiduguri. An kamashi ne bayan samun bayanan sirri akan satar harsasan da yayi. Sojan dai na kan hanyar zuwa Kadunane bayan da aka kamashi da harsasan guda 602 kuma yana tsare yanzu haka.
Matar aure ta dirkawa mijinta harsashi ya mutu har lahira bayan data kamashi yana cin amanarta da makwabciyarsu yayin da yake shirin tserewa

Matar aure ta dirkawa mijinta harsashi ya mutu har lahira bayan data kamashi yana cin amanarta da makwabciyarsu yayin da yake shirin tserewa

Auratayya
18665874 - a closeup of the lock of a jail cell with iron bars and a bunch of key in the locking mechanism with the door open Wata mata me shekaru 33 a kasar Afrika ta kudu ta dirkawa mijinta harsashi ya mutu har lahira bayan data kamashi yana lalata da wata. Tuni dai hukumomi suka kama matar bisa zargin kisan kai. Suna zaune gida dayane dai da matar da mijin yayi lalata da ita. Kuma da matar tasa ta fuskanceshi da maganar, sai yayi yunkurin tserewa, saidai ta yi amfani da bindigarsa ta harbeshi ya mutu. Kakakin 'yansanda na yankin Limpopo, Col Malesela Ledwaba ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace auna bincike.
Karanta Jadawalin yawan likitocin da kowace jiha ke dasu a fadin Najeriya

Karanta Jadawalin yawan likitocin da kowace jiha ke dasu a fadin Najeriya

Kiwon Lafiya
Wannan jadawalin yawan likitocin da kowace jiha ke dasu ne a Fadin Najeriya: Lagos: 7,385 FCT: 4,453 Rivers: 2,194 Enugu: 2,070 Oyo: 1,996 Edo: 1,777 Kaduna: 1,524 Anambra: 1,518 Ogun: 1,511 Kano: 1,477 Delta: 1,456 Osun: 1,294 Plateau: 1,200 Imo: 1,110 Kwara: 1,016 Ebonyi: 899 Akwa Ibom: 888 Abia: 829 Cross River: 826 Ondo: 743 Borno: 736 Bayelsa: 727 Ekiti: 695 Benue: 621 Sokoto: 602 Katsina: 562 Nassarawa: 552 Niger: 494 Gombe: 485 Bauchi: 443 Kogi: 418 Adamawa: 280 Yobe: 275 Kebbi: 273 Zamfara: 267 Jigawa: 255 Taraba: 201