Saturday, December 6
Shadow
Kalli Bidiyon: Wata Mata Mijinta ya sake ta ya bata kyautar Naira Miliyan 7 da Mota amma ta kirani tace bata so, Dan Allah a mayar masa da kudinsa da motarsa, ita dai ya mayar da ita, tana son zama dashi>>Inji Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa, akwai wata mata da mijinta ya saketa ya bata Naira Miliyan 7 da Mota amma tace bata so. Malam ya kara da cewa, Matar tace ya taimaka ya roki mijinta ya mayar da ita ya karbi kudinsa da motar daya bata ita dai tana son ci gaba da zama dashi ta mutu a gidansa. Malam ya bayyana hakane a daya daga cikin karatuttukan da yake yi. https://www.tiktok.com/@nurasara531/video/7565809192498367752?_t=ZS-90taIXPgUfB&_r=1
Kalli Bidiyo: Zan mayar da matatar man fetur dina me fitar da ganga Miliyan 1.4 na man fetur kullun maimakon ganga 650,000>>Inji Dangote

Kalli Bidiyo: Zan mayar da matatar man fetur dina me fitar da ganga Miliyan 1.4 na man fetur kullun maimakon ganga 650,000>>Inji Dangote

Duk Labarai
Attajirin Africa, Aliko Dangote a hukumance ya sanar da mayar da matatar man fetur dinsa ta rika fitar da ganga Miliyan 1.4 kullun Maimakon Ganga 650,000 da yake fitarawa a yanzu. Yace hakan zai sa matatar tasa ta zama ta Daya a Duniya wajan yawan fitar da man fetur. Dangi ya sanar da hakane a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai. Ya godewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kuma 'yan Najeriya bisa hadin gwiwar da suka bashi.
Duk da matatar Dangote na samar da man fetur, Babban Bankin Najeriya, CBN ya baiwa ‘yan kasuwar mai daloli suka siyo man fetur daga kasashen waje zuwa Najeriya

Duk da matatar Dangote na samar da man fetur, Babban Bankin Najeriya, CBN ya baiwa ‘yan kasuwar mai daloli suka siyo man fetur daga kasashen waje zuwa Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, babban Bankin Najeriya, CBN ya bayar da dala Biliyan $1.259 dan a shigo da man fetur da sauran wasu abubuwa masu alaka dashi zuwa cikin Najeriya. An saki kudadenne a watanni 3 na farko na shekarar 2025 da muke ciki. Hakan na zuwane yayin da rikici ke ci gaba da ruruwa tsakanin 'yan kasuwar da Dangote inda yake cewa a hanasu shigo da man fetur daga kasashen waje su kuma suna cewa basu yadda ba saboda ba zai iya wadata Najeriya da man fetur din da yake samarwa ba. Sannan suna zargin Dangoten da kokarin mamaye harkar man gaba daya a Najeriya.
Manyan Sojoji sama da 500 ne aka tursasawa yin ritaya a tsakanin Gwamnatocin Buhari dana Tinubu

Manyan Sojoji sama da 500 ne aka tursasawa yin ritaya a tsakanin Gwamnatocin Buhari dana Tinubu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Manyan Sojoji sama da 500 ne aka yiwa ritaya a tsakanin gwamnatocin Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Rahoton yace Sojojin sun Hada da janarori manya da kanana. Wata majiya daga gidan soji ta shaidawa jaridar Punchng cewa, yawan manyan sojojin da akawa ritayar dole sun kai 900. Lamarin ritayar dole na faruwane idan aka nada sabbin shuwagabannin sojoji, dan haka wadanda ke gaba da sabbin shuwagabannin sojojin dole su yi ritaya dan a samu aiki ya daidaita.
Ina Matukar Tausayawa me mace daya>>Inji Sanata Ned Nwoko

Ina Matukar Tausayawa me mace daya>>Inji Sanata Ned Nwoko

Duk Labarai
Sanata Ned Nwoko ya bayyana cewa, yana tausayawa maza masu mace daya. Ya bayyana hakane a wata ganawa da aka yi dashi a Channels TV inda yace mace daya kamar mutum na tsayene akan kafa daya, da ta samu matsala shikenan. Yace amma idan mutum na da mata da yawa, zai fi samun nutsuwa. Game da maganar matarsa, Regina Daniels yace ba gaskiya bane da ake yada cewa ya ci zarafinta ta hanyar duka, yace shi yana ganin girman mata.
Kalli Bidiyon yanda Maiwushirya ya fita hayyacinsa, Yace Dubu 3 ce kawai ta rage a account dinsa, inda yace Abba El-Mustapha ya ja masa asarar Miliyoyin Naira

Kalli Bidiyon yanda Maiwushirya ya fita hayyacinsa, Yace Dubu 3 ce kawai ta rage a account dinsa, inda yace Abba El-Mustapha ya ja masa asarar Miliyoyin Naira

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Idris Maiwushirya ya ci gaba da caccakar shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, Abba El-Mustapha inda yake cewa ba zai taba yadda ya dakileshi ba. Yace ba zai taba amincewa da hukuncin Abba El-Mustapha ba, saboda dan fim ne dan Nanaye. Yace da alkaliyace ko Malam Aminu Ibrahim Daurawa suka masa hukunci zai iya yadda dashi amma ba zai taba amincewa da Hukuncin Abba El-Mustapha ba. Yace ya tara kudi sama da Naira Miliyan 1 a Facebook amma saboda tsarewar da aka masa tasa ya kasa fiddosu har suka lalace. https://www.tiktok.com/@maiwushiryabackup/video/7565605083686194439?_t=ZS-90sk7hvb50b&_r=1
Kalli Ya cika Alkawarin da ya dauka na Yin kwalkwali idan Real Madrid ta yi nasara akan Barcelona

Kalli Ya cika Alkawarin da ya dauka na Yin kwalkwali idan Real Madrid ta yi nasara akan Barcelona

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wannan wani matashi ne daga Arewa da ya cika alkawarin da ya dauka na yin kwalkwali idan Real Madrid ta yi nasara akan Barcelona a wasan Elclasico da aka buga. Madrid Dai tawa Barcelona ci 2-1 A alkawarin da matashin yayi, yace zai aske Gashin kansa da Gemu ne amma yanzu yace na kai kawai ya aske, a hakan ma yayi kokari. https://twitter.com/jibreelKhalil/status/1982534847647174866?t=c3f6LcOzEd_iEM3509nMNw&s=19