Saturday, December 6
Shadow
Kalli Bidiyon yanda Maiwushirya ya fita hayyacinsa, Yace Dubu 3 ce kawai ta rage a account dinsa, inda yace Abba El-Mustapha ya ja masa asarar Miliyoyin Naira

Kalli Bidiyon yanda Maiwushirya ya fita hayyacinsa, Yace Dubu 3 ce kawai ta rage a account dinsa, inda yace Abba El-Mustapha ya ja masa asarar Miliyoyin Naira

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Idris Maiwushirya ya ci gaba da caccakar shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, Abba El-Mustapha inda yake cewa ba zai taba yadda ya dakileshi ba. Yace ba zai taba amincewa da hukuncin Abba El-Mustapha ba, saboda dan fim ne dan Nanaye. Yace da alkaliyace ko Malam Aminu Ibrahim Daurawa suka masa hukunci zai iya yadda dashi amma ba zai taba amincewa da Hukuncin Abba El-Mustapha ba. Yace ya tara kudi sama da Naira Miliyan 1 a Facebook amma saboda tsarewar da aka masa tasa ya kasa fiddosu har suka lalace. https://www.tiktok.com/@maiwushiryabackup/video/7565605083686194439?_t=ZS-90sk7hvb50b&_r=1
Kalli Ya cika Alkawarin da ya dauka na Yin kwalkwali idan Real Madrid ta yi nasara akan Barcelona

Kalli Ya cika Alkawarin da ya dauka na Yin kwalkwali idan Real Madrid ta yi nasara akan Barcelona

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wannan wani matashi ne daga Arewa da ya cika alkawarin da ya dauka na yin kwalkwali idan Real Madrid ta yi nasara akan Barcelona a wasan Elclasico da aka buga. Madrid Dai tawa Barcelona ci 2-1 A alkawarin da matashin yayi, yace zai aske Gashin kansa da Gemu ne amma yanzu yace na kai kawai ya aske, a hakan ma yayi kokari. https://twitter.com/jibreelKhalil/status/1982534847647174866?t=c3f6LcOzEd_iEM3509nMNw&s=19
Labari ne cike da Darasi: Ji irin whulakanchin akawa Sabon Shugaban sojojin Ruwa da shugaba Tinubu ya nada Rear Admiral Idi Abbas a mahaifarsa ta garin Jos a lokacin yana kokarin shiga aikin soja

Rahotanni sunce sabon shugaban sojijin Ruwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nada watau Rear Admiral Idi Abbas, dan Asalin Jihar Filato ne domin a can aka haifeshi. A lokacin da ya so shiga makarantar Horas da sojoji ta NDA dake Kaduna, ya je karamar hukumar sa inda ya nemi a bashi takardar shaidar zamansa dan karamar hukumar. Amma sai aka ki bashi saboda Addininsa da kuma kabilarsa ta Hausa. Sai ya tafi garin mahaifinsa, watau Kano kuma a can aka bashi takardar ya kai aka daukeshi aikin sojan. Yau gashi ya zama shugaban sojojin Ruwa na Najeriya. Zakaran da Allah ya nuna da chara....
Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda Hassan Make-Up ke kuka saboda kama kawarsa, Khadija MaiNumfashi

Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda Hassan Make-Up ke kuka saboda kama kawarsa, Khadija MaiNumfashi

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Hassan Make-Up ya bayyana a Bidiyo yana kuka saboda kama kawarsa Khadija MaiNumfashi. An ji hassan na cewa yanzu a Ina Khadija tasan wasu 'yan daba? https://www.tiktok.com/@officielhassanmakeup227/video/7565558701084380428?_t=ZS-90sQtSa6Op7&_r=1 A jiya ne dai 'yansanda suka kama Khadija MaiNumfashi suka wuce da ita zuwa Legas inda ake zarginta da batawa wani me suna Kabiru Lagos suna. Daga cikin karin zarge-zargen da ake mata hadda cewa ta nemi halakashi ta hanyar daukar 'yan daba su farmaki rayuwarsa.
Kalli Bidiyon: Mun Barkune kunata hauka amma babu maganar aure tsakanina da Maiwushirya, Taimakon Rayuwata yake>>Inji ‘YarGuda

Kalli Bidiyon: Mun Barkune kunata hauka amma babu maganar aure tsakanina da Maiwushirya, Taimakon Rayuwata yake>>Inji ‘YarGuda

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok Abasiya 'YarGuda itama ta fito ta tabbatar da maganar cewa babu aure tsakaninta da Maiwushirya. Ta bayyana hakane a wani Bidiyo inda take cewa Maiwushirya taimakonta yake. Tace Ko da ta amsa a Kotu cewa zata aureshi ba da gaske take ba. https://www.tiktok.com/@pharooq_/video/7565550522065767701?_t=ZS-90sPvJMyw1A&_r=1
Kalli Bidiyon Gwanin Ban Tausai: Yanda ‘Yan Uwan Habasiyya ‘YarGuda suka je Kano daga Zamfara zasu mayar da ita Gida

Kalli Bidiyon Gwanin Ban Tausai: Yanda ‘Yan Uwan Habasiyya ‘YarGuda suka je Kano daga Zamfara zasu mayar da ita Gida

Duk Labarai
Bayan hukuncin kotu da kuma tsayawar shirin da suke yi ita da Idris Maiwushirya, 'yan uwan Habasiyya 'YarGuda sun je Kano daga jihar Zamfara dan mayar da ita Gida. A Bidiyon an ga daya daga cikin 'yan uwan nata na bayyana cewa, Bakin ciki ake musu saboda Maiwushirya yana taimakon rayuwarta ne da abubuwan da ba'a rasa ba. Ta bayyana cewa matsalar 'yan Bindiga ta damesu a garinsu. Saurarin jawabinta a Bidiyon kasa: https://www.tiktok.com/@pharooq_/video/7565543245309152533?_t=ZS-90sOSmk9WC1&_r=1
Kalli Bidiyon: Asarar Naira Miliyan 3 Abba El-Mustapha yasa na yi kuma Allah ya isa, Sannan bai isa yamin Auren Dole ba>>Inji Maiwushirya

Kalli Bidiyon: Asarar Naira Miliyan 3 Abba El-Mustapha yasa na yi kuma Allah ya isa, Sannan bai isa yamin Auren Dole ba>>Inji Maiwushirya

Duk Labarai
Idris Maiwushirya ya bayyana bacin ransa kan abinda yace Abba EL-Mustapha ya masa inda yace ya shirya abinshi amma saboda bakin ciki aka sa yayi sarar Naira Miliyan 3. Maiwushirya yace Abba El-Mustapha bai isa yasa a masa auren dole be sannan kuma shi da ya kama Chairlady a ni sai ka goyani wa yace sai ya aureta? Ya kuma bayyana magungunan da ya saya saboda rashin lafiyar da ya kwanta duk saboda wannan matsalar. Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya watsu sosai inda aka ganshi a kwance. Ya kara da cewa da yana so ya auri 'YarGuda ai da ba sai an tursasa shi ba. https://www.tiktok.com/@pharooq_/video/7565543951642496277?_t=ZS-90sKFJ5TOmv&_r=1
Ba zan tsaya takara a shekarar 2027 ba, na hakura haka, a samu wani matashi da bai kaini Shekaru ba shima ya zo ya gwada>>Inji Dan majalisar wakilai daga jihar Sokoto, Hon. Abdussamad Dasuki

Dan majalisar Wakilai, Hon. Abdussamad Dasuki me wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal daga jihar Sokoto ya bayyana cewa ba zai tsaya takara a shekarar 2027 ba. Yace ya barwa matasa 'yan kasa da shekaru 40 su tsaya takarar dan kawo sauyi da ci gaba a mazabar tashi. Yace yayi hakanne ba dan ya gaji ko gazawa ba inda yace har yanzu shi matashi ne amma ya haura shekaru 40. Yayi godiya ga mutanen mazabatarsa da iyayen gidansa a siyasa da suka bashi dama a shekaru 14 da yayi yana siyasar.
Hukumar Hisbah ta Kano ta kama mutane 25 inda namiji ke shirin auren Namiji a Kano

Hukumar Hisbah ta Kano ta kama mutane 25 inda namiji ke shirin auren Namiji a Kano

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta kama mutane 25 dake shirin kulla auren Namiji da Namiji. An kamasu ne a Fatima Event Center dake Hotoro ranar Lahadi. Mataimakin Kwamanda na Hisbah, Mujahedeen Aminudeen ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Yace daga cikin wadanda aka kama akwai maza 18, mata 7. Yace sun samu bayanan sirri ne kan daura auren 'yan Luwadin.