Friday, July 31
Shadow

Gyaran fuska da tumatir

Gyaran Fuska, Kwalliya
Bayan Amfani a Miya, Tumatir na da wani amfani musamman a wajan gyaran fata da fuska: Ga amfanin da yakewa fuska kamar haka: Tumatur na daidaita man fuska. Idan ya kasance fuskarki me yawan samar da maski ne ko mai wanda bata barin kwalliya ta dade a jikin fuskar, kina iya amfani da tumatur wajan maganin wannan matsala. Yanda ake yi shine: Zaki dauki tumatur ki yankashi gida biyu. Sai ki shafashi akan fuskarki. Ki barshi yayi mintuna 10 akai sannan ki wanke da ruwa. Yin hakan akai-akai zai yi miki maganin yawan maikon fuska. Za'a iya yin Amfani da Tumatur dan kawar da dattin da ya makale a fuska wanda wanki da sabulu baya masa. Akwai abubuwa da yawa irin su dattin masana'antu da sauransu wanda idan suka hau kan fata ko fuska, dan wanka ko wankewa da ruwa baya ...

Gyaran fuska da manja

Gyaran Fuska, Kwalliya
Akwai hanyoyi da yawa da ake gyaran fuska da man ja. Ga wasu daga ciki kamar haka: A wanke fuska dan fitar da duk wani datti, a saka tsumma a tsane fuskar. Daga nan sai a shafa man ja, a bari ya dan jiku a fuskar sai a goge. Hakan yana kawar da duk wani duhun fata. Ana kuma iya diga man ja a cikin man shafawa ko man wanka da sauransu. A wani kaulin, an ruwaito man ja na kawar da tabon kuna wanda bai yi zurfi ba sosai, sannan yana kawar da tabon kurajen fuska da yankewa wadda bata yi zurfi ba sosai. Hakanan wani kaulin ya bayyana manja na maganin tattarewar fuska ta tsufa, fuskar mutum ba zata tattare sosai ba.
Shugaba Tinubu ya saka jiragensa 3 a kasuwa

Shugaba Tinubu ya saka jiragensa 3 a kasuwa

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta sanar da saka jiragen shugaban kasar guda 3 a kasuwa dan sayarwa. Jiragen dai sun tsufane shine aka tattara za'a sayar dan samun kudaden da za'a siyo sabbi. Wannan mataki kuma zai rage kudaden da ake kashewa wajan kula da jiragen wanda ba duka Shugaban kasar ke amfani dasu ba. Hakan na zuwane yayin da majalisar tarayya ta bada shawarar saiwa shugaban kasar da mataimakinsa sabbin jirage.
Hotuna: An kamasu sun sàci mota a masallacin Abuja

Hotuna: An kamasu sun sàci mota a masallacin Abuja

Duk Labarai
'Yansanda a babban birnin tarayya, Abuja sun kama wasu mutane 2 da ake zargi da satar mota kirar Toyota Corolla. Kakakin 'yansandan na Abuja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da lamarin inda yace an kamasu ne ranar Juma'a. Yace an kamasu ne a yayin da suke kokarin sayar da Motar a kan Naira Miliyan 6.5 a Minna. Wadanda aka kama din sune, Gwaza Bulus san kimanin shekaru 41 da kuma Yahya Amodu dan kimanin shekaru 45. Ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Abin Kunyane hukuncin da kotu ta yanke a Kano>>Inji Babban Lauya, Femi Falana

Siyasa
Babban kauya, Femi Falana ya bayyana cewa, abin munyane hukuncin da kotu ta yanke a Kano. Yace babbar kotun tarayya dake Kano bata da hurumin shiga harkar siyasar sarauta, hurumin kotun jiha ne. Yace kuma hukuncin da kotun ta yanke ya kawo rudani dan bai fito da hukuncin da kotun ke nufi ba baro-baro. Ya kara da cewa kotun daukaka kara ce dama dai take warware irin wannan matsala kuma yana da kyau ganin cewa yanzu an aikawa kotun daukaka kara shari'ar.

Kuka a daren farko

Auratayya, Soyayya
Mafi yawanci bisa al'ada amare na kuka a daren farko da suka shiga dakin mijinsu bayan an daura aure. Saidai basu kadai ne ke wannan kukan ba. Da yawa ciki hadda iyayen amarya, uba da uwa dukan akan samu wadanda ke yin wannan kuka. Yawanci iyaye kan yi kukane bayan an daura aure a lokacin da ake tafiya da amarya zuwa gidan mijinta tana musu bankwana ko kuma suka gama yi mata nasiha. A daidai wannan lokaci hawaye yakan kwacewa iyayen amarya. Saidai wasu ba'a ganin nasu, suna yin na zuci ne kawai, ko kuma sai dare yayi sun ga gurbin diyarsu anan ne hawaye ko kukan zuci zasu fara bayyana a fuskar iyaye. Ita kuwa amarya a mafi yawan lokuta tana fara kukanta ne a yayin da aka kamota za'a sakata cikin mota dan zuwa gidan miji daga gidansu. Za'a tafi da ita tana kuka har zuwa...