Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Gwamnati ta kwace gidan dala Miliyan $2.5 da tsohon ma’aikacin kamfanin mai na kasa, NNPCL, Paulinus Iheanacho Okoronkwo ya siya da kudin sata a kasar Amurka

Gwamnati ta kwace gidan dala Miliyan $2.5 da tsohon ma’aikacin kamfanin mai na kasa, NNPCL, Paulinus Iheanacho Okoronkwo ya siya da kudin sata a kasar Amurka

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta kwace gidan Dala Miliyan $2.5 da tsohon ma'aikacin kamfanin mai na kasa, NNPCL, Paulinus Iheanacho Okoronkwo ya siya a kasar Amurka da kudin sata. A watan Augusta ne aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari bayan samunsa da laifin rashawa da cin hanci. An sameshi da laifin karbar cin hanci har dala Miliyan $2.1 daga wani kamfanin mai me suna Addax Petroleum da zummar cewa zai samarwa da kamfanin lasisin hakar danyen man fetur a Najeriya. Kuma ya sayi gidanne a Valencia dake California kasar Amurka.
Kalli Bidiyon mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yana cewa, ‘Yan Najeriya kun yi sa’a da Allah ya baku ni a matsayin mataimakin shugaban kasa

Kalli Bidiyon mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yana cewa, ‘Yan Najeriya kun yi sa’a da Allah ya baku ni a matsayin mataimakin shugaban kasa

Duk Labarai
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun taki sa'a da Allah ya basu shi a matsayin mataimakin shugaban kasa. Ya bayyana hakane a ziyarar da ya kai jihar Katsina. Da yake jawabi, Kashim Shettima yace Katsinawa sun yi dace da Allah ya basu Dikko Raddah a matsayin gwamnan, yace a tafa masa. Sannan yace 'yan Najeriya kuma sun yi dace da Allah ya basu shi a matsayin mataimakin shugaban kasa. https://www.tiktok.com/@kashiimshettima/video/7563681781183040776?_t=ZS-90js9tRs0Zd&_r=1
An tsingi Jariyriyah Sabuwar Haihuwa Mahaifiyarta ta Yaddah ta a Birnin New York City na kasar Amurka

An tsingi Jariyriyah Sabuwar Haihuwa Mahaifiyarta ta Yaddah ta a Birnin New York City na kasar Amurka

Duk Labarai
Rahotanni daga birnin New York City dake kasar Amurka yace an tsinci jaririya sabuwar haihuwa a birnin da ake zargin mahaifiyartace ta yadda ta. An tsinci jaririyar ne a matattaqalar shiga tashar jirgin kasa ta karkashin kasa an nannadeta da tawul a Midtown Manhattan da misalin karfe 9:30 na safe. Tuni 'yansanda suka je suka dauketa aka kaita Asibiti inda likitoci suka tabbatar tana cikin koshin Lafiya.
A bayyana mana sunayen Maqiya Dimokradiyya da suka so yiwa Gwamnatin Tinubu juhyin Mulki>>Mahdi Shehu ya roki Gwamnatin Tarayya

A bayyana mana sunayen Maqiya Dimokradiyya da suka so yiwa Gwamnatin Tinubu juhyin Mulki>>Mahdi Shehu ya roki Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Dan Gwagwarmaya, Mahdi Shehu ya bayyana cewa, 'yan Najeriya suna nema kuma suna da 'yancin a sanar dasu sunayen sojojin da suka shirya yiwa Gwamnatin Tinubu juyin Mulki. Ya bayyana hakane a shafinsa na X inda yace sati uku kenan ana ta rade-radin cewa an yi yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki. Yace magana dai tun ana jita-jita har ta zama gaskiya inda yace ya kamata a daina boye-boye a fito a gayawa 'yan Najeriya su waye suka shirya wannan juyin Mulki?
Ji yanda magidanci ya fashe da kuka a Asibiti bayan da matarsa ta haifi ‘yan Shida rigis a lokaci guda

Ji yanda magidanci ya fashe da kuka a Asibiti bayan da matarsa ta haifi ‘yan Shida rigis a lokaci guda

Duk Labarai
Wani magidanci dake tsakanin shekaru 30 ya fashe da kuka bayan da matarsa ta haifi 'yan 6. Bidiyon lamarin ya watsu a kafafen sada zumunta inda akai ta zazzafar muhawara akai. Mutumin ya tsaya kan matarsa inda ya rika fadin lallai kina da karfin hali da kika iya haifar 'yan shida. Rahotanni sun ce mutumin na tunanin kudin kula da yaran ne shiyasa shi kuka. !An dai ga Ma'aikaciyar jinya tana bashi baki kan lamarin.
Sabon Umarni: Daga yanzu duk sojan da aka kai daji ya tabbata ya shekye akalla guda daya kamin ya dawo, idan kuwa ka dawo baka sheke ko guda ba aikinka bai cika ba>>Inji Shugaban Sojoji Janar Christopher Musa

Shugaban tsaro, Janar Christopher Musa ya baiwa jami'an tsaron sabon Umarni inda yace duk sojan da aka kai daji ba zai rika wuce shekara 2 ba za'a canja masa wajan aiki. Ya bayyana hakane a yayin da ya kaiwa sojojin ziyara. Yace kuma duk sojan da aka kai yaki da B0K0 Hàràm ya tabbata ta Kqshe akalla guda daya. Yace idan aka aika soja daji ya koma bai kashe ko da B0k0 Hàràm guda ba to lallai aikinsa bai cika ba. https://twitter.com/DejiAdesogan/status/1980287403668431098?t=cAQNQk9fgmhODjgBTn3XOg&s=19 Sannan yace sojojin su daina zama suna jiran sai an kawo musu hari su mayar da martani, su rika fita suma suna farautar abokan gaba.
Wata Sabuwa: Abin Sheikh Maqari ya fara yawa, yanzu ya wuce cewa Hadisai na taba mutuncin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya fara cewa Har ayoyin Qur’ani na taba janabin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)>>Inji Sheikh Lawal Triumph

Malam Lawal Triumph ya mayarwa da Sheikh Ibrahim Maqari da martanin cewa, yanzu ya wuce cewa, Hadisai na taba Janabin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yanzu yana cewa har Ayoyin Qur'ani suna taba mutuncin Annabi. Malam Lawal ya saka muryar Sheikh Ibrahim Maqari inda yake cewa, Sayyidna Umar(RA) yana dukan wani saboda yana yawan karanta Abasa watawallah. Saurari martanin anan: https://www.tiktok.com/@alkeeblahtv/video/7563306173932539144?_t=ZS-90jCtXhsiVl&_r=1