Tuesday, December 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Shugaban kasar Kamaru me shekaru 92 Paul Biya ya sake lashe zaben shugaban kasa a karo na 8

Shugaban kasar Kamaru me shekaru 92 Paul Biya ya sake lashe zaben shugaban kasa a karo na 8

Duk Labarai
Shugaban ƙasar Kamaru mai shekara 92 a duniya ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasar a karo na takwas, bayan da Majalisar Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen na ranar 12 ga watan Oktoba. Biya ya lashe zaɓen ne bayan ya samu kashi 53.66% na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da babban abokin hamayyarsa Issa Tchiroma Bakary ya zo na biyu da kashi 35.19%, kamar yadda Majalisar ta bayyana. "Paul Biya ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, bayan ya samu mafi yawa na ƙuri'un da aka kaɗa," in ji Clement Aatanga, shugaban Majalisar Kundin Tsarin Mulki ta ƙasar. Kashi 57.76% ne na waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a suka fita domin yin zaɓen, inda kashi 42.24% suka ƙaurace.
Sule Lamido Yayi Barzanar kai PDP kotu saboda an ki sayar masa da Fom din tsayawa takarar shugaban jam’iyyar

Sule Lamido Yayi Barzanar kai PDP kotu saboda an ki sayar masa da Fom din tsayawa takarar shugaban jam’iyyar

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido yayi barzanar Kai jami'iyyarsa ta PDP kara kotu. Sule Lamido ya bayyana hakane bayan kasa sayen Fom din tsayawa takarar shugaban jam'iyyar a ranar Litinin Yace idan bai samu damar sayar fom din ba zai iya garzayawa kotu dan jin dalilin da yasa aka hanashi. A baya dai, Sule Lamido ya bayyana aniyarsa ta son tsayawa takarar shugaban jam'iyyar PDP a shafinsa na Facebook. Saidai wasu manya a jam'iyyar sun bayyana cewa, Kabiru Tanimu Turaki suke son tsayarwa a matsayin shugaban jam'iyyar
Kalli Bidiyo: Na gano Mutane ‘yan Iyska ne kuma suna son Iskanchi shiyasa nake Iyskanchi a wakokina>>Inji Soja Boy

Kalli Bidiyo: Na gano Mutane ‘yan Iyska ne kuma suna son Iskanchi shiyasa nake Iyskanchi a wakokina>>Inji Soja Boy

Duk Labarai
Tauraron mawakin Batsa, Soja Boy ya bayyana cewa yana sane cewa akwai iskanchi a wakokonsa. Saidai yace dalilinsa na saka Iskanchi a wakokinsa shine, ya ga abinda mutane ke so kenan. Yace kuma idan Babu Iyskanchi a waka mutane basa kallo. https://www.tiktok.com/@maaunipodcast/video/7557035389358312722?_t=ZS-90th9EZljZg&_r=1
Kalli Bidiyo: Rashida Mai Sa’a ta fito ta baiwa Kabiru Legas da ya kama Khadija MaiNumfashi hakuri ya sake ta

Kalli Bidiyo: Rashida Mai Sa’a ta fito ta baiwa Kabiru Legas da ya kama Khadija MaiNumfashi hakuri ya sake ta

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Wadda ta bayyana kanta a matsayin shugabar matan Kannywood Rashida Mai Sa'a ta fito ta baiwa kabiru Legas Hakuri kan sawa da yayi 'yansanda suka kama Jarumar Kannywood, Khadija MaiNumfashi. Rashida ta yi kira ga Kabiru da cewa, ya tuna da cewa soyayya ce ta hadashi da Khadija MaiNumfashi dan haka bai kamata ya wulakantata ba. Tace ta yi magana da mahaifiyar Khadija dan a nemo mata lambar Kabiru Legas din amma duk da haka taga ya kamata ta yi Bidiyo dan ya gani. https://www.tiktok.com/@backup_rashida_mai_saa/video/7565707358228319496?_t=ZS-90teTfTWgE5&_r=1
Kalli Bidiyon: Wata Mata Mijinta ya sake ta ya bata kyautar Naira Miliyan 7 da Mota amma ta kirani tace bata so, Dan Allah a mayar masa da kudinsa da motarsa, ita dai ya mayar da ita, tana son zama dashi>>Inji Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Malamin Addinin Islama, Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa, akwai wata mata da mijinta ya saketa ya bata Naira Miliyan 7 da Mota amma tace bata so. Malam ya kara da cewa, Matar tace ya taimaka ya roki mijinta ya mayar da ita ya karbi kudinsa da motar daya bata ita dai tana son ci gaba da zama dashi ta mutu a gidansa. Malam ya bayyana hakane a daya daga cikin karatuttukan da yake yi. https://www.tiktok.com/@nurasara531/video/7565809192498367752?_t=ZS-90taIXPgUfB&_r=1
Kalli Bidiyo: Zan mayar da matatar man fetur dina me fitar da ganga Miliyan 1.4 na man fetur kullun maimakon ganga 650,000>>Inji Dangote

Kalli Bidiyo: Zan mayar da matatar man fetur dina me fitar da ganga Miliyan 1.4 na man fetur kullun maimakon ganga 650,000>>Inji Dangote

Duk Labarai
Attajirin Africa, Aliko Dangote a hukumance ya sanar da mayar da matatar man fetur dinsa ta rika fitar da ganga Miliyan 1.4 kullun Maimakon Ganga 650,000 da yake fitarawa a yanzu. Yace hakan zai sa matatar tasa ta zama ta Daya a Duniya wajan yawan fitar da man fetur. Dangi ya sanar da hakane a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai. Ya godewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kuma 'yan Najeriya bisa hadin gwiwar da suka bashi.
Duk da matatar Dangote na samar da man fetur, Babban Bankin Najeriya, CBN ya baiwa ‘yan kasuwar mai daloli suka siyo man fetur daga kasashen waje zuwa Najeriya

Duk da matatar Dangote na samar da man fetur, Babban Bankin Najeriya, CBN ya baiwa ‘yan kasuwar mai daloli suka siyo man fetur daga kasashen waje zuwa Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, babban Bankin Najeriya, CBN ya bayar da dala Biliyan $1.259 dan a shigo da man fetur da sauran wasu abubuwa masu alaka dashi zuwa cikin Najeriya. An saki kudadenne a watanni 3 na farko na shekarar 2025 da muke ciki. Hakan na zuwane yayin da rikici ke ci gaba da ruruwa tsakanin 'yan kasuwar da Dangote inda yake cewa a hanasu shigo da man fetur daga kasashen waje su kuma suna cewa basu yadda ba saboda ba zai iya wadata Najeriya da man fetur din da yake samarwa ba. Sannan suna zargin Dangoten da kokarin mamaye harkar man gaba daya a Najeriya.
Manyan Sojoji sama da 500 ne aka tursasawa yin ritaya a tsakanin Gwamnatocin Buhari dana Tinubu

Manyan Sojoji sama da 500 ne aka tursasawa yin ritaya a tsakanin Gwamnatocin Buhari dana Tinubu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Manyan Sojoji sama da 500 ne aka yiwa ritaya a tsakanin gwamnatocin Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Rahoton yace Sojojin sun Hada da janarori manya da kanana. Wata majiya daga gidan soji ta shaidawa jaridar Punchng cewa, yawan manyan sojojin da akawa ritayar dole sun kai 900. Lamarin ritayar dole na faruwane idan aka nada sabbin shuwagabannin sojoji, dan haka wadanda ke gaba da sabbin shuwagabannin sojojin dole su yi ritaya dan a samu aiki ya daidaita.
Ina Matukar Tausayawa me mace daya>>Inji Sanata Ned Nwoko

Ina Matukar Tausayawa me mace daya>>Inji Sanata Ned Nwoko

Duk Labarai
Sanata Ned Nwoko ya bayyana cewa, yana tausayawa maza masu mace daya. Ya bayyana hakane a wata ganawa da aka yi dashi a Channels TV inda yace mace daya kamar mutum na tsayene akan kafa daya, da ta samu matsala shikenan. Yace amma idan mutum na da mata da yawa, zai fi samun nutsuwa. Game da maganar matarsa, Regina Daniels yace ba gaskiya bane da ake yada cewa ya ci zarafinta ta hanyar duka, yace shi yana ganin girman mata.