Monday, December 23
Shadow

Author: Auwal Abubakar

Jimullar Bashin da ake bin Najeriya ya nuna kowane dan Najeriya ana binshi bashin Naira dubu dari shida(600,000)

Jimullar Bashin da ake bin Najeriya ya nuna kowane dan Najeriya ana binshi bashin Naira dubu dari shida(600,000)

Duk Labarai
Rahotanni sun nuna cewa jimullar bashin da ake bin Najeriya ya nuna cewa kowane dan kasa ana binshi bashin Naira N619,501. Bayanai daga ofishin dake kula da bashin Najeriya sun nuna cewa ana bin Najeriya jimullar bashin Naira Tiriliyan N134.297. Bashi dai na daya daga cikin hanyoyin da gwamnati ke bi dan samun kudin shiga wanda ake gudanar da ayyukan raya kasa dasu.
Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya dakatar da shigo da man fetur daga kasar waje inda ya amince ya saya daga wajan Dangote

Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya dakatar da shigo da man fetur daga kasar waje inda ya amince ya saya daga wajan Dangote

Duk Labarai
Kamfanin Man fetur na kasa,NNPCL ya dakatar da sayo man fetur daga kasar waje inda ya amince ya sayi man fetur din daga wajan Matatar man fetur din Dangote da sauran matatun man fetur masu zaman kansu. Shugaban kamfanin, Mele Kyari ya bayyana haka a wajan wani taro da ya faru a Legas ranar Litinin. Hakan na zuwane yayin da 'yan kasuwar man fetur suka nace saidai su sayo man fetur din daga kasar waje maimakon sayowa daga hannun matatar man Dangote saboda a cewarsu,man fetur din da suke kawowa daga wajen ya fi na Dangote sauki. Kyari ya kuma musanta cewa suna yiwa matatar man fetur ta Dangote zagon kasa inda yace suma suna da hannun jari a matatar.
EFCC Ta gayyaci wani dan kasar Nijar saboda liken kudi da aka yi a wajan bikinsa

EFCC Ta gayyaci wani dan kasar Nijar saboda liken kudi da aka yi a wajan bikinsa

Duk Labarai
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta kasa, EFCC ta gayyaci wani dan kasar Nijar me suna Ibrahim Mohammad saboda yanda aka yi liken kudi a wajan bikinsa. Hakan ya biyo bayan watsuwar Bidiyon bikin a kafafen sada zumunta inda aka rika kiran EFCC da ta dauki mataki akan lamarin. Kakakin hukumar, Dele Oyewale ya fitar da sanarwa akan lamarin inda yace da farko an danganta bikin da diyar Danjuma Goje me suna Fauziyya amma daga baya da aka yi bincike an gano bikin na Hajara Seidu Haruna ne wadda ke harkar GwalaGwalai a Kano, Abuja da Dubai. Yace wadanda ake zargin sun amsa laifinsu.
Akwai dalibina dake da digiri na 3, PhD amma baya iya rubuta sunansa da kyau>>Inji Shugaba NTI

Akwai dalibina dake da digiri na 3, PhD amma baya iya rubuta sunansa da kyau>>Inji Shugaba NTI

Duk Labarai
Shugaban makarantar horas da dalibai ta NTI Professor Garba Maitafsir ya bayyana cewa a cikin daliban karatun digiri na 3, PhD da yake koyarwa akwai wanda bai iya rubuta sunansa ba. Malamin ya bayyana cewa, a ko da yaushe ya kamata ana duba ingancin ilimin malamai dan samun ilimi a wajan dalibai me kyau. Ya bayyana hakane a wajan taro karawa juna sani a Kaduna kan aikin lamunta a jihar Kaduna.
Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira Biliyan 19 wajan kula da jiragen shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a cikin watanni 15 da suka gabata

Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira Biliyan 19 wajan kula da jiragen shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a cikin watanni 15 da suka gabata

Duk Labarai
An kashe akalla Naira N19.43bn wajan kula da jiragen sama na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a tsakanin watan July 2023 zuwa September 2024. Shafin GovSpend ne dake saka ido kan yanda gwamnati ke kashe kudadenta ya wallafa wadannan bayanai. Hakanan shafin yace a shekarar 2024, gwamnati ta ware Naira N13.55bn dan kula da jiragen na shugaban kasa. Hakan na zuwane dai a yayin da mutane da yawa a Najeriya ke fama da wahala wajan samawa kansu abinci.
Nasan Ana shan wahala kuma ina kokarin kawo gyara amma ba yanzu-yanzu ne Al’amura zasu canja ba>>Shugaba Tinubu

Nasan Ana shan wahala kuma ina kokarin kawo gyara amma ba yanzu-yanzu ne Al’amura zasu canja ba>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa yana sane da ana shan wahala a Najeriya kuma yana kokarin kawo sauyi amma sai an yi hakuri dan ba za'a ga wannan sau yi da gaggawa ba. Shugaban ya bayyana hakane ta bakin sakataren Gwamnatin tarayya, Senator George Akume a wajan taron zagayowar ranar haihuwar Pastor Tunde Bakare inda ya cika shekaru 70 da haihuwa. Shugaban ya kuma bayyana Fasto Tunde Bakare a matsayin gwarzo wanda ya bar tarihi me kyau wanda ba za'a manta dashi ba.
Kalli Bidiyo da hotuna yanda motar Dangote ta buge mutane 3 suka mùtù a Jihar Legas

Kalli Bidiyo da hotuna yanda motar Dangote ta buge mutane 3 suka mùtù a Jihar Legas

Duk Labarai
Hukumar kula da ababen hawa ta jihar Legas, LASTMA ta tabbatar da mutuwar mutane 3 bayan da motar Dangote ta bugesu. Rahoton Daily Post yace motar Dangoten dake tafiya akan titin Ita-Opo, Epe ta samu matsalar birki ne inda hakan yasa ta yi taho mu gama da wasu motocin. https://twitter.com/Lagosreporters_/status/1855938771633533145?t=wGaRJiBP-OFQUcO5-BlCNw&s=19 Shugaban hukumar ta LASTMA, Olalekan Bakare-Oki ya tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakin hukumar Taofiq Adebayo, yace motar ta Dangote ta buge Keke Napep da wata mota dake ajiye a gefe. https://twitter.com/adewaleJMO/status/1855957712321773616?t=fn1mEjTIZyObnJoUM-_CEw&s=19 https://twitter.com/Onsogbu/status/1855973272296591750?t=JNXlLjjnGAXnnLp6mzFP5Q&s=19 Yace direban keke Napep din da...