Monday, January 12
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Da Duminsa: Matatar Man Dangote ta dakatar da aiki

Da Duminsa: Matatar Man Dangote ta dakatar da aiki

Duk Labarai
Rahotanni daga matatar man Dangote tace an dakatar da aiki a bangaren tace man fetur na matatar. Hakan na zuwane daga bakin mataimakin shugaban kamfanonin Dangote me suna Devakumar Edwin wanda yace an dakatar da aikinne dan wasu 'yan Gyare-Gyare. Yace idan aka kammala gyaran yawan man fetur din da matatar ke tacewa zai karu daga ganga 650,000 kullun zuwa ganga 700,000 kullun. Wannan dalili yasa tuni Depot dake sayarwa da 'yan kasuwa man fetur suka kara farashin man su zuwa Naira 800 akan kowace lita.
Allah Sarki: Tauraruwar fina-finan Hausa cikin sheshekar tace ta bar harkar Film saboda ba riba

Allah Sarki: Tauraruwar fina-finan Hausa cikin sheshekar tace ta bar harkar Film saboda ba riba

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, ta bayyana cewa, ta bar harkar film saboda ba riba. Tace shekarunta 20 tana harkar film amma bata ajiye komai ba. Ta bayyana cewa yawanci dubu 5 ake biyansu idan suka yi fim. Ta kara da cewa, yanzu haka bata da inda zata zauna sannan bata da sutura kuma abinci ma yana musu wahala. Tace da zata samu Mijin aure, zata yi aure ta huta. https://www.tiktok.com/@officielhassanmakeup227/video/7590881103548894476?_t=ZS-92l4dwPER04&_r=1
Direban Motar su Anthony Joshua yace da Anthony Joshua ne ke zaune a gaban Motar amma yace yana kare masa Madubi ya koma baya, abokinsa ya koma zama gaban motar

Direban Motar su Anthony Joshua yace da Anthony Joshua ne ke zaune a gaban Motar amma yace yana kare masa Madubi ya koma baya, abokinsa ya koma zama gaban motar

Duk Labarai
Direban motar da ta yi hadari da dan damben Najeriya, Anthony Joshua inda har abokansa 2 suka rasu yace da Anthony Joshua ne ya zauna a gaban motar. Yace amma daga baya sai yace yana kare masa madubin gefe ya koma baya abokinsa ya dawo gaban motar. Abokan Anthony Joshua biyu dai duka sun rasu a hadarin inda shi kuma ciwuka ba masu tsanani ba yaji.
An yi min wahayin cewa, Tinubu ko shine da kansa zai zama shugaban INEC ba zai ci zaben 2027 ba muddin ya dage sai ya karbi Haraji a hannun ‘yan Najeriya>>Inji Fasto Ayodele

An yi min wahayin cewa, Tinubu ko shine da kansa zai zama shugaban INEC ba zai ci zaben 2027 ba muddin ya dage sai ya karbi Haraji a hannun ‘yan Najeriya>>Inji Fasto Ayodele

Duk Labarai
Fasto Ayodele ya bayyana cewa, ko Tinubu ne zai zama shugaban INEC, ba zai ci zaben shekarar 2027 ba muddin ya dage akan sai ya karbi kudin Haraji a hannun 'yan Najeriya. Ya bayyana hakane a cocinsa ga mabiyansa. https://twitter.com/i/status/2007162007884313013 Hakan na zuwane yayin da shugaba Tinubu yace maganar karbar Haraji ba gudu ba ja da baya.
Sabbin Bayanai sun fito game da jirgi marar Matuki da ya fadi a jihar Naija

Sabbin Bayanai sun fito game da jirgi marar Matuki da ya fadi a jihar Naija

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Wani Jirgi marar Matuki ya fadi a dajin jihar Naija. Lamarin ya dauki hankula da saka fargaba a zukatan mutane. Musamman ma saboda harin da kasar Amurka ta kawo Najeriya a jihar Sokoto a kwanakin baya. Saidai sabbin bayanan da ake samu game da jirgin shine cewa, na sojojin saman Najeriya ne dake tattara bayanai daga Tshàgyèràn Dhàjì. Me magana da yawun hukumar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame ya tabbatar da hakan. Yace jirgin yana tattara bayanai ne daga Tshàgyèràn Dhàjì a yayin da ya fadi inda yace amma bai kashe kowa ba ko jikkata kowa ba. Yace amma cikin hadin gwiwa da sauran abokan aikinsu, an dauko jirgin daga inda ya fadi.
Da Duminsa: Bayan Khàdàrìn da ya faru da Anthony Joshua inda abokansa 2 suka rasa ransu, Wani cikin wanda suka taru dan taimaka musu ya sace wayar Anthony Joshua

Da Duminsa: Bayan Khàdàrìn da ya faru da Anthony Joshua inda abokansa 2 suka rasa ransu, Wani cikin wanda suka taru dan taimaka musu ya sace wayar Anthony Joshua

Duk Labarai
Rahotanni sun kara fitowa game da hadarin mota da dan Damben Najeriya, Anthony Joshua yayi da abokansa 2 Wanda abokan suka rasu. Kawun Anthony Joshua yace bayan faruwar Hadarin, wadanda suka taru dan taimakawa Anthony Joshua an samu wani ya sace masa waya. Lamarin ya baiwa mutane mamaki musamman ganin cewa, Mutum na cikin halin tashin hankali irin wannan a samu wani ya masa sata?
An dauke Wuta a wani sashe na kasar Amurka inda sama da mutane 300,000 suka fada Duhu

An dauke Wuta a wani sashe na kasar Amurka inda sama da mutane 300,000 suka fada Duhu

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, an dauke wutar lantarki a kasar wanda ya jefa mutane 350,000 cikin Duhu. Lamarin ya farune dalilin ruwa me tsanani da iska da aka yi a yankin Michigan. Mahukunta sun yi gargadin cewa, mutane su kiyaye akwai yiyuwar ci gaba da ruwan da kankara. Saidai wannan labarin yasa hukumar kula da wutar lantarki mamaki, inda har suka saka alamar ido a bude sosai a kafar X, watau Alamar abin ya basu mamaki kenan. Da yawan 'yan Najeriya sun ji haushin wannan lamarin inda suke cewa ai dauke wutar ba irin na Najeriya bane da ake yi kullun. https://twitter.com/i/status/2007087923242443090
Da Duminsa: Sabbin Bayanai sun fito game da shirin komawar Gwamna Abba Jam’iyyar APC

Da Duminsa: Sabbin Bayanai sun fito game da shirin komawar Gwamna Abba Jam’iyyar APC

Duk Labarai
Rahotonni nata kara karfi kan shirin komawar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf jam'iyyar APC. Sabbin Rahotannin da ake samu shine cewa nan da ranar Litinin in Allah ya kaimu, Gwamna Abba Kabir Yusuf a hukumance zai koma jam'iyyar APC. Hakan na zuwane yayin da siyasar Kano ke ci gaba da daukar Dumi. Ana ganin wannan komawar ta Gwamna Abba jam'iyyar APC zata iya kawo baraka tsakaninsa da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
Kalli Bidiyon abinda wani dan Kungiyar Kwallon Kafa ta Al Ahli yawa Ronaldo a filin wasa da ya baiwa Ronaldon Haushi

Kalli Bidiyon abinda wani dan Kungiyar Kwallon Kafa ta Al Ahli yawa Ronaldo a filin wasa da ya baiwa Ronaldon Haushi

Duk Labarai
Bayan wasan da aka buga tsakanin Al Ahli da Alnasr da aka tashi Al Ahli ta yi nasara da 3-2, wani abu ya faru tsakanin Ronaldo da wani ma'aikacin Kungiyar ta Al Ahli. Yayin da Ronaldo ya ke fita daga filin wasan, ma'aikacin kungiyar Al Ahli, ya zo ya wuceshi yana fadar Messi, Messi. Abin yawa Ronaldo Haushi, har sai da Ronaldon ya je ya sameshi. Lamarin ya dauki hankula sosai. https://twitter.com/i/status/2007178627436437564