Friday, July 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon: Ahmad XM ya bayyana wanda yayi nasarar samun kyautarsa ta Naira Miliyan 1

Kalli Bidiyon: Ahmad XM ya bayyana wanda yayi nasarar samun kyautarsa ta Naira Miliyan 1

Duk Labarai
Ahmad XM ya sanar da wanda ya lashe kyautar Miliyan 1da yace zai baiwa daya daga cikin mutanen dake comment dinsa. Wanda ya lashe wannan kudi shine Uzaifa Sabitu wanda ya bayyana cewa, ya dade yana son canja rayuwarsa inda yace idan ya samu kudin zai karfafa kasuwancinsa dasu. Ahmad XM yace masa ya tura masa da account dinsa kuma tuni ya saka masa kudin. https://twitter.com/i/status/2071194877916811543 Daga baya matashin ya bayyana a wani Bidiyo inda yakewa Ahmad XM Godiya. https://twitter.com/i/status/2071212241718755720
Kalli Bidiyon: Kikace kin tuba? Kwana biyu bayan da aka sakota daga ofishin HISBAH, Gorgeous ta saki sabon Bidiyo da ya jawo cece-kuce

Kalli Bidiyon: Kikace kin tuba? Kwana biyu bayan da aka sakota daga ofishin HISBAH, Gorgeous ta saki sabon Bidiyo da ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
A kwana biyu da suka gabata ne dai muka ga Gorgeous a ofishin Hisbah inda ta bayyana nadamar abubuwan da ta yi a baya. Ta kuma roki masu tsaffin Bidiyon ta da su goge inda tace duk wanda bai goge ba, bata yafe masa ba. Saidai duk da haka sai gashi an ganta a wani Bidiyo tana rawa wadda wasu ke cewa bata dace ba. Wasu sun rika tambayarta a comment cewa, ba itace tace ta tubaba? https://www.tiktok.com/@gorgeous_ghurl/video/7656479168506481938?_r=1&_t=ZS-97bytxtaIo1
Wadanda suka je kallon wasannin kofin Duniya a kasar Amurka na kokawa da cewa Amurkawa sun cika roko

Wadanda suka je kallon wasannin kofin Duniya a kasar Amurka na kokawa da cewa Amurkawa sun cika roko

Duk Labarai
Wadanda suka je kallon wasannin kofin Duniya a kasar Amurka sun bayyana cewa, Amurkawa sun cika rokon kudi. Sun bayyana cewa ko ruwa mutum ya siyasa a shago sai kaji mutum yace wai a bashi kudi. A kasar Amurka, al'adar rokon Kwastoma kudi kyauta idan yayi siyayya ba sabuwar abu bace, da yawa zaka ga albashin da ake biyan ma'aikata babu yawa amma ta wajan kyautukan da ake basu anan suke samun kudade masu yawa da zasu iya rike kansu. Wasu sun yi bayanin cewa, su sunfi gane a gaya musu ainahin farashin kaya su saya maimakon a basu kaya da sauki amma kuma a rika rokonsu kudi.
Kalli Bidiyon: Bayan Na farko, Sabon Bidiyon Amal Umar Yafito inda aka ga Abokin yin fim dinta ya rungumeta

Kalli Bidiyon: Bayan Na farko, Sabon Bidiyon Amal Umar Yafito inda aka ga Abokin yin fim dinta ya rungumeta

Duk Labarai
A yayin kwanaki kadan da suka gabata, aka ga Tauraruwar fina-finan Hausa, Amal Umar a wani fim din kudancin Najeriya suka wasanni irin na ma'auarata suna kama hannu ita da Usman Uzee. A karo na biyu, Amal Umar ta sake yin wani abu da ya dauki hankula. An kuma sake ganinta inda Usman Uzee ya rungumeta. Lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa da suna mata kallon me hankali a cikin sabbin jaruman fina-finan Hausa. https://www.tiktok.com/@uzee_usman/video/7655611280719498518?_r=1&_t=ZS-97buEvKKoLs
Kalli Bidiyon: A karshe dai, Aminu Warkal ya bayyana laifin da matarsa ta mai ya saketa

Kalli Bidiyon: A karshe dai, Aminu Warkal ya bayyana laifin da matarsa ta mai ya saketa

Duk Labarai
Bayan da matarsa ta fito kafafen sada zumunta ta bayyana cewa ya saketa tsakar dare ya kuma ce ta fitar masa daga gida, Aminu Warkal ya bayyana dalilin da yasa ya mata hakan. A martaninsa, Aminu Warkal yace matarsa da suna zaune lafiya, kawai sai ta fito da wani sabon hali na rashin godiya kan dukkan abinda ya mata. Yace sannan babu wata magana me dadi dake shiga tsakaninsu. Yace hakanne da abu yayi kamari shine suka rabu. Yace babban abinda ya kawo rabuwar shine dabbobinsa da ta dauka ta sayar ba da izininsa ba, sannan ya kulle mata gida yace ta je ta dawo dasu amma taki. Saidai yace duk da wannan abu da ya faru tsakaninsu, har yanzu da zata kirashi tace yayi hakuri, da zai mayar da ita dakinta.