Tsageran ESN Sun kashe sojojin Najeria biyu daya ya bace, sun kuma tsere da makaman sojojin
Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojojin ta 2 bayan harin da kungiyar ESN dake karkashin kungiyar IPOB ta kai mata.
A sanarwar data fitar ranar Asabar, Hukumar sojojin ta bayyana cewa, lamarin ya farune a garin Osina dake karamar hukumar Ideator ta Arewa dake jihar Imo a yayin da wata tawagar sojojin ke dawowa daga wani dauki da suka kai a yankin Osina bayan kiran da aka musu cewa kungiyar ta ESN ta kai hari garin.
Hakanan sanarwar tace sojojin sun fafata da ESN a yankin Nkwachi inda suka kashe mutum daya daga ciki sauran suka tsere sannan kuma an kwato bindiga daya aga hannunsu.