NNPC Ta Sanar Da Kammala Biyan Bashin Dala Bilyan 2.4, Tare Da Albishirin Samar Da Manyan Tashoshin CNG 12 A Shekara Mai Zuwa
Shugaban rukunin Kamfanin Mai Na NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana nasarar kammala biyan bashin da ake bin kamfanin da ga kamfanonin mai na kasashen ƙetare inda ya ce a yanzu, babu mai bin kamfanin bashin sisin kwabo.Kyari ya ce, wannan babban nasara ce da aka cimma biyo bayan cire tallafin mai a Gwamnatin Shugaba Tinubu.
“Mun rika karkatar da kudadenmu da dukiyoyinmu don tabbatar da komai na tafiya daidai a bangaren mai na PMS mai wuyar sha'ani, abinda ya rika janye hankalin NNPC daga biyan basussuka"
Mele ya ci gaba da cewa“ Sai dai yanzu wannan matsala ta kau, za ku ga cewa ba mu da wani bashin da ake bin mu, kuma don mu tabbatar da dorewar hakan, ya zama wajibi a kawar da duk wata matsala don masana'antar ta iya samar da makamashi mai dorewa da arha da ake buƙata a ƙasar nan."
Sh...