Tuesday, January 13
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon: Dan jam’iyyar APC daga jihar Katsina, Bashir ‘yandoma ya roki Gwamna Radda ya samar musu hular kwano

Kalli Bidiyon: Dan jam’iyyar APC daga jihar Katsina, Bashir ‘yandoma ya roki Gwamna Radda ya samar musu hular kwano

Duk Labarai
Dan jam'iyyar APC a jihar Katsina, Bashir 'Yandoma ya roki Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya samar musu hulunan Kwano. Yace dalili kuwa idan ba'a yi gyara ba, mutane zasu jefesu da duwatsu. https://twitter.com/jrnaib2/status/2005566799954272541?t=DjgBwMTjvdP2oPaV3mTM6g&s=19 A baya dai an jefi 'yan majalisa a jihohin Zamfara, Kaduna, da jihar Kebbi.
Kalli Bidiyon: Trump ne ke mulkin mu ba Tinubu ba>>Inji Naja’atu Muhammad

Kalli Bidiyon: Trump ne ke mulkin mu ba Tinubu ba>>Inji Naja’atu Muhammad

Duk Labarai
'Yar Siyasa daga yankin Arewa, Naja'atu Muhammad ta yi zargin cewa Donald Trump na America ne ke mulkin Najeriya ba shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba. Ta bayyana hakane a wata hira da DCL Hausa ta yi da ita. Tace tunda Najeriya ta samu 'yancin kanta Najeriya bata taba yadda sojojin wata kasa sun shigo cikinta sun kawo hari ba sai lokacin Tinubu. Tace a yanzu Turawa na kara yi mana Mulkin mallaka ne da aka yi a shekarun baya. https://twitter.com/Arewa_Source/status/2005562060768501999?t=NMvj60w3oaEW40g2Ad9GPg&s=19
Duk wayonnan nawa da Allah ya bani ace in kare a mataimakin shugaban kasa? Bazan yadda ba, shugaban kasa zan nema>>Inji Peter Obi

Duk wayonnan nawa da Allah ya bani ace in kare a mataimakin shugaban kasa? Bazan yadda ba, shugaban kasa zan nema>>Inji Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa, ba zai yadda yawa kowa takarar mataimakin shugaban kasa ba a 2027. Yace dalili kuwa yana da wayau sosai kuma ba zai yadda duk wayonnan da Allah ya bashi ba ya kare da mataimakin shugaban kasa. Yace yasan yanda zai gyara Najeriya dan haka takarar shugaban kasa zai nema. Peter Obi ya kara da cewa har Tinubu yafi wayau.
Sarauta Sai Arewa: Bidiyon wani basaraken Kudu sanye da sarkar Gwal yana rawa da ‘yanmata ya dauki hankula

Sarauta Sai Arewa: Bidiyon wani basaraken Kudu sanye da sarkar Gwal yana rawa da ‘yanmata ya dauki hankula

Duk Labarai
An ga Bidiyon wani basaraken Yarbawa sanye da sarkar Gwal yana rawa tare da wasu mata. Bidiyon ya jawo muhawara da yawa inda wasu ke cewa, bai kamata a matsayinsa na basarake hakan bai dace ba. Wasu kuma na tambayar ina ya samu kudin sayen Sarkar Gwal. https://twitter.com/1RitaSunshine/status/2005549299430752395?t=gF5Tucd-GJy750yqYWeidQ&s=19
Wata Sabuwa: An gano cewa Naira Biliyan 200 da EFCC ke zargin Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami da sacewa, ya samesu ne daga Bashin Manoma da CBN suka bayar Lokacin Buhari, da Kudaden Abacha da aka dawo dasu da kuma Paris Club

Rahotanni sun bayyana cewa, Naira Biliyan 200 da EFCC ke zargin Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami da sacewa, ya samesu ne daga kudaden bashin da babban bankin Najeriya, CBN ya baiwa manoma bashi lokacin Buhari. Da kuma kudin Abacaha da aka dawo dasu Najeriya da kuma kudin Paris Club watau bashin da Gwamnatin Tarayya da gwamnoni suka ciwo. Kafar The Cable tace ta samu cewa Abubakar Malami ya sa matarsa me suna Hajiya Bashir Asabe ta ci bashin na manoma har Naira Biliyan 4 wanda kuma bata biya ba. A yanzu dai EFCC sun sakata cikin wadanda za'a gurfanar dasu a gaban kotun tare, a baya dai Hutudole ya kawo muku cewa akwai dan Abubakar Malami da shima yanzu EFCC ke tuhuma. A bangaren Kudaden Abacha da aka karbo, lauyoyi turawa aka dauka suka yi aiki, amma rahotan yace Abubaka...
Shugaban kasa Bola Tinubu ya yafewa kamfanin mai na kasa, NNPCL bashin dala Biliyan $1.42 da Naira Tiriliyan 5.57 daya kamata su biya Gwamnatin Tarayya

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yafewa kamfanin mai na kasa, NNPCL bashin dala Biliyan $1.42 da Naira Tiriliyan 5.57 daya kamata su biya Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yafewa Kamfanin mai na kasa, NNPCL bashin dala Biliyan $1.42 da Naira Tiriliyan 5.57 da ya kamata NNPCL din su biya a asusun Gwamnatin tarayya. Hakan na kunshene a cikin bayanan da hukumar kula da man fetur ta kasa, Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission suka futar. Rahoton yace fadar shugaban kasa ta bayar da umarnin yafe bashin da kuma gogeshi daga cikin takardun da aka rubutashi.
Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda wannan Inyamurar Musulma ke kokawa da irin abinda Inyamurai Kiristoci ke mata

Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda wannan Inyamurar Musulma ke kokawa da irin abinda Inyamurai Kiristoci ke mata

Duk Labarai
Wannan wata inyamura musulma ce da a dauki hankula a kafafen sadarwa saboda abinda tace Inyamurai Kiristoci na mata. Ta bayana cewa, suna mata Bhàràzànà inda tace da tana kawar da kai ama abin sai karuwa yake. Ta bayyana cewa tana a garin Nsukka ne kuma garinsu akwai zaman lafiya amma wasu na son kawo matsala. Tace kiristanci bai koya abinda Kiristocin ke mata ba dan haka bata san inda suka samo irin abinda suke mata ba. Tace kuma me ya shafesu da addinin da take yi? Da yawa dai sun yi kira ga hukumomi da su dauki matakan da suka dace dan baiwa wannan matashiya kariya kada wani abu ya sameta. https://twitter.com/muslimnews_NG/status/2005394522042425410?t=7dOqfLtTUE8YtGbNytmUcQ&s=19
Wannan Bidiyon na Tauraruwar fina-finan Hausa, Asma Wakili tana Rawa tare da Rùngùmàr wani ya dauki hankula

Wannan Bidiyon na Tauraruwar fina-finan Hausa, Asma Wakili tana Rawa tare da Rùngùmàr wani ya dauki hankula

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Asma Wakili ta dauki hankula bayan da aka ganta tana rawa tare da rungumar wani a Bidiyo. Wasu dai sun rika cewa danta ne inda wasu ke cewa kaninta ne saboda yanda suka yi kama dashi. Bidiyon ya jawo muhawara sosai. https://www.tiktok.com/@asmee.wakili286/video/7588808148765658389?_t=ZS-92cX8MbQt85&_r=1
Sowore Wanda Kirista ne yace bai yadda da ikirarin shugaban kasar Amurka, Donald Trump ba na cewa yana son ceton Kiristocin Najeriya ba

Sowore Wanda Kirista ne yace bai yadda da ikirarin shugaban kasar Amurka, Donald Trump ba na cewa yana son ceton Kiristocin Najeriya ba

Duk Labarai
Mawallafin Jaridar Sahara reporters kuma dan fafutuka, Omoyele Sowore ya bayyana cewa, bai yadda da ikirarin shugaban kasar Amurka, Donald Trump ba na cewa, wai yana son ceton Kiristocin Najeriya ba. Yace ta yaya Trump zai ce yana son ceton Kiristocin Najeriya amma ya hanasu shiga kasar Amurka? Shugaba Donald Trump dai ya saka tsatstsauran mataki kan 'yan Najeriya dake son shiga kasar Amurka ba tare da banbance musulmi ko Kirista ba. https://twitter.com/sowore/status/2005397646861607248?t=QYuZlJd_H9UzyTcFGdQJ8g&s=19