Saturday, April 25
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Allah Sarki Kalli Bidiyon: Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana abinda zai fara yi idan ICPC suka sakeshi

Allah Sarki Kalli Bidiyon: Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana abinda zai fara yi idan ICPC suka sakeshi

Duk Labarai
Bayan zaman kotun da aka yi dashi a Jihar Kaduna jiya, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya zanta da 'yan Jarida. Inda ya gayawa jaridar Daily Trust cewa, idan ya fito, sune na farko da zai yi hira dasu. https://www.tiktok.com/@luperasom/video/7620960315328564487?_r=1&_t=ZS-94yZA08QohV&sp_source=7537614245375297080 A jiya ne dai ICPC ta gurfanar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai a kotu inda aka zargeshi da almundahanar kudade wanda ya karyata.
Kalli Bidiyon: Wannan wulakancin da ake mana, wataran ba za’a yi ba>>inji Matar ElRufai, Asia yayin da aa hanata shiga cikin kotun da ake masa shari’a

Kalli Bidiyon: Wannan wulakancin da ake mana, wataran ba za’a yi ba>>inji Matar ElRufai, Asia yayin da aa hanata shiga cikin kotun da ake masa shari’a

Duk Labarai
An ga matar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, Hajiya Asia a kofar kotun da ake masa shari'a inda aka hanata shiga. An ji tana fadar cewa, Rayuwace, wannan ma wataran zai wuce. Daga baya dai an shigar da ita cikin kotun ta hanyar baya. https://www.tiktok.com/@luperasom/video/7620898661421026578?_r=1&_t=ZS-94yYA7QAZyD&sp_source=7537614245375297080 A jiya ne dai ICPC suka gurfanar da tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a kotu inda ake tuhumarsa kan zarge-zargen almundahanar kudade.
Allah Sarki, Kalli Bidiyon Tauraruwar fina-finan Hausa na neman Taimakon Ali Nuhu a mata aiki saboda rashin Lafiyar dake damunta

Allah Sarki, Kalli Bidiyon Tauraruwar fina-finan Hausa na neman Taimakon Ali Nuhu a mata aiki saboda rashin Lafiyar dake damunta

Duk Labarai
Wannan wata Tauraruwar fina-finan Hausa ce da ta fito ta bayyana cewa, Qari ya fito mata a hannu sannan take neman taimakon Ali Nuhu, Abba El-Mustapha da sauransu su taimaka mata a mata aiki. An ga Bidiyon nata a kafafen sada zumunta inda ya dauki hankula da yawa sun tausaya mata. https://www.tiktok.com/@i_a_sarari/video/7620898247309102356?_r=1&_t=ZS-94yWZthM0wa&sp_source=7537614245375297080
Kalli Bidiyon: Kada mu sake zabar Wannan Azzalumar Gwamnatin ta Tinubu saboda basu son Arewa kuma ga Haraji>>Inji Tauraron  fina-finan Hausa, Sadik Sani Sadik

Kalli Bidiyon: Kada mu sake zabar Wannan Azzalumar Gwamnatin ta Tinubu saboda basu son Arewa kuma ga Haraji>>Inji Tauraron fina-finan Hausa, Sadik Sani Sadik

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Sadiq Sani Sadiq yayi kira ga 'yan Arewa kada su sake zaben gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda azzaluma ce. Sadiq ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa daya dauka a wata kasuwa inda aka ga yana magana cikin fushu. Ya zargi gwamnatin Tinubu cewa bata son Arewa, inda yace sun kawo haraji da Rashin Tsaro. Ya karkare maganarsa da cewa kada a sake zaben Tinubu a matsayin shugaban kasa inda yace idan kunne yaji.... https://www.tiktok.com/@kamalkmann/video/7620830467448720660?_r=1&_t=ZS-94y3ShKLgNF&sp_source=7537614245375297080
Ku yi hakuri da rashin wutar da kuke fama da ita, zamu gyara>>Ministan wutar Lantarki ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri

Ku yi hakuri da rashin wutar da kuke fama da ita, zamu gyara>>Ministan wutar Lantarki ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri

Duk Labarai
Ministan wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya baiwa 'yan Najeriya hakuri kan rashin wutar da ake fama da ita a 'yan kwanakinnan. Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai a Abuja ranar Talata inda yace musamman a wannan lokacin zafin da ake ciki rashin wuta akwai damuwa. Yace amma suna bayar da tabbacin nan ba da jimawa ba zasu gyara wutar.
Kwankwaso zai koma jam’iyyar ADC ranar Laraba

Kwankwaso zai koma jam’iyyar ADC ranar Laraba

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso zai koma jam'iyyar ADC nan da ranar Laraba. Rahoton yace Kwankwaso zai koma jam'iyyar ADC ne a garinsa inda ake tsammanin zai yanki katin jam'iyyar acan. Rahoton wanda ya fito daga the Whistler yace a kwanakinnan, Kwankwaso ya gana da wasu jiga-jigan jam'iyyar na ADC wanda hakan yasa ake kara kyautata zaton komawarsa jam'iyyar.
Kalli Bidiyon: Dan gidan Marigayi, Rigi-Rigi, Khalifa Sheikh Tijjani Rigi-Rigi ya gaji mahaifinsa inda ya maye kujerarsa yana bayar da karatu

Kalli Bidiyon: Dan gidan Marigayi, Rigi-Rigi, Khalifa Sheikh Tijjani Rigi-Rigi ya gaji mahaifinsa inda ya maye kujerarsa yana bayar da karatu

Duk Labarai
Dan gidan Marigayi Rigi-Rigi me suna Khalifa Sheikh Tijjani Rigi-Rigi ya gaji mahaifinsa inda aka ganshi a kujerar mahaifin nasa yana bayar da karatu. Shima dai an ga alamar yana bayar da dariya a wajan karatin nasa kamar dai yanda mahaifinsa ke yi. https://www.tiktok.com/@imam_hussain_rigi_rigi/video/7620550519567682836?_r=1&_t=ZS-94xheMlWgym&sp_source=7537614245375297080
Allah Sarki Kalli Bidiyon: Yanda kasar Nijar ta koro ‘yan Najeriya guda 708 da suka je Chirani

Allah Sarki Kalli Bidiyon: Yanda kasar Nijar ta koro ‘yan Najeriya guda 708 da suka je Chirani

Duk Labarai
' Yan Najeriya 708 ne da suka je Chirani kasar Nijar, kasar ta taso keyarsu ta dawo dasu gida Najeriya. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, (NEMA) ta karbi 'yan Najeriyar bayan da aka dawo dasu gida ranar Litinin. Shugaban Hukumar NEMA na Kano, Dr Nura Abdullahi ne ya tabbatarwa da manema labarai hakan bayan karbar 'yan Najeriyar a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano International Airport dake Kano. An kawo su ne a manyan motocin 12 da misalin karfe 4:08 pm. Inda aka fara tantancesu. Guda 292 mazane sai kuma guda 416 wanda matane da kananan yara. Kuma yawanci sun fitone daga jihohin Katsina, Kano, Jigawa, Benue, Borno, Yobe, Zamfara, Kaduna, Kogi da Niger. Ya bayyana cewa an basu abubuwan bukata na gaggawa da suka hada da abinci, kulawar lafiya da gida...