Sunday, December 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ji Abinda ya faru da shafukan sada zumunta na Hadiza Gabon bayan da Masoya Adam A. Zango suka sha Alwashin yin Unfollow dinta

Ji Abinda ya faru da shafukan sada zumunta na Hadiza Gabon bayan da Masoya Adam A. Zango suka sha Alwashin yin Unfollow dinta

Duk Labarai
Bayan da Hadiza Gabon ta ki saka hoton Adam A. Zango a dakin da take hira da mutane wanda ya jawo cece-kuce sosai. Daya daga cikin matakan da masoya Adam A. Zango suka sha alwashin dauka shine zasu yi Unfollow dinta a shafukan sada zumunta dan nuna bacin Ransu. Tun bayan shan wannan Alwashi yanzu sama da awanni 24 kenan Hutudole yana saka ido akan shafukan na sada zumuntar Hadiza Gabon dan ganin ko zata samu raguwar mabiya. Mutane musamman a kasashen Turawa sukan dauki irin wannan mataki na Unfollow ga wani da yayi wani abinda basa so. Saidai Hutudole har zuwa yanzu ya lura cewa Hadiza Gabon bata rasa mabiya ba ko kuma mabiyanta basu ragu ba a shafukanta na sada zumunta.
‘Yan majalisar jihar Rivers 16 sun bar PDP zuwa APC

‘Yan majalisar jihar Rivers 16 sun bar PDP zuwa APC

Duk Labarai
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Rivers, Martin Amaewhule, ya sauya sheƙa tare da wasu ƙarin mambobi 15 na majalisar a ranar Juma’a, lamarin da ya ƙara dagula harkokin siyasar jihar wadda ke fama da rikice-rikicen cikin gida tun watanni da dama. Rahotanni sun nuna cewa sauya sheƙar na da alaƙa da rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar. Wannan mataki ya mayar da adadin mambobin majalisar da suka koma jam’iyyar APC zuwa 16 gaba ɗaya. Sauya sheƙar ya faru ne a wani zama na musamman da majalisar ta yi inda mambobin suka bayyana cewa sun yanke shawarar komawa APC
Kalli Bidiyon: Idan Kana da mata, zaka kara aure ka zo neman diyata, na gano kana zama a teburin Meshayi, Ba zan baka diyata ba dan kai ba adali bane>>Inji Malam

Kalli Bidiyon: Idan Kana da mata, zaka kara aure ka zo neman diyata, na gano kana zama a teburin Meshayi, Ba zan baka diyata ba dan kai ba adali bane>>Inji Malam

Duk Labarai
Wannan malamin ya bayyana cewa idan mutum na da mata kuma yana neman kara aure ya je neman diyarsa kuma ya gano mutum na cin Indomie a teburin me shayi to ba zai bashi diyarsa ba. Yace dalili kuwa shine hakan ba adalci bane. Ka bar iyalinsa a gida da garau-garau ka je Teburin me shayi cin Indomie. https://www.tiktok.com/@zaidou1taza/video/7580089084819868940?_t=ZS-91xuxXVejnV&_r=1
Kalli Bidiyon: Shi Abu idan dan Allah aka yishi menene na Nunawa Duniya? Amma idan dan Allah yayi Allah ya bashi lada>>Inji Babban Yaron Nazir Ahmad Sarkin Waka, Abba C Sale game da gina masallacin da Rarara yayi

Babban yaron Naziru Ahmad Sarkin Waka, Abba C Sale ya bayyana cewa idan Dauda Kahutu Rarara dan Allah ya gina masallacinsa ba sai ya nunawa Duniya ba. Amma duk da haka yace yana fatan Allah ya bayar da lada idan dan Allah yayi. Ya bayyana hakane a Bidiyon daya saki a Tiktok. https://www.tiktok.com/@abbacsale2/video/7580282459506461973?_t=ZS-91xqFHoRhxZ&_r=1 A yaune dai Dauda Kahutu Rarara zai bude katafaren masallacin da ya gina a mahaifarsa dake Kahutu.
Kalli Bidiyon: Bayan Kwado me hana Zarmalulun mikewa, Rashida Mai Sa’a ta kuma kawo Qaho da Dodon Kodi na mallaka

Kalli Bidiyon: Bayan Kwado me hana Zarmalulun mikewa, Rashida Mai Sa’a ta kuma kawo Qaho da Dodon Kodi na mallaka

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rashida Mai Sa'a ta sake kawo wasu magunguna na mallaka wanda aka yi da Dodon Kodi da kuma wanda aka yi da Qaho. An ga Rashidar na nunawa wata suna hirarsu. https://www.tiktok.com/@mamanmeimacollection/video/7580035395140766996?_t=ZS-91xp54SwgTZ&_r=1 Hakan na zuwane bayan da a baya Rashida ta dauki hankula sosai saboda fito da kwado wanda tace yana Zarmalulun maza masu aure tashi.
Nada Christopher Musa Ministan tsaro ya firgita Tshàgyèràn Dhàjì >>Inji Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle

Nada Christopher Musa Ministan tsaro ya firgita Tshàgyèràn Dhàjì >>Inji Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle

Duk Labarai
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana cewa, nada Christopher Musa ministan tsaro ya saka 'yan Bindiga cikin damuwa. Ya bayyana hakane yayin hirar da aka yi dashi a DCL Hausa. Yace Christopher Musa mutun ne jajirtacce me kwarewa wanda kuma yasan aikinshi Da aka tambayeshi ya zasu yi aiki tare, yace dama su ba bakin juna bane sun san juna tun suna matasa. https://www.tiktok.com/@dclhausa/video/7580088473605066006?_t=ZS-91xlMedULkO&_r=1
Ni an ce min Najeriya ba zaman Lafiya(Ana Mhuzghunawa Kiristoci) amma gashi nazo Najeriya banga wata matsalar tsaro ba>>Inji Tsohon Firaiministan Ingila Boris Johnson

Ni an ce min Najeriya ba zaman Lafiya(Ana Mhuzghunawa Kiristoci) amma gashi nazo Najeriya banga wata matsalar tsaro ba>>Inji Tsohon Firaiministan Ingila Boris Johnson

Duk Labarai
Tsohon Firaiministan Ingila, Boris Johnson ya bayyana cewa gashi cikin aminci a Najeriya duk da labaran da ya ji cewa wau ana Mhuzghunawa Kiristoci a Najeriyar. Ya bayyana hakane a wajan taron Tattalin Arziki da ya faru a jihar Imo. Boris yace ko da yake kan hanyar zuwa Imo sai da aka gaya masa akwai barazanar tsaro amma duk da haka shi sai ya je. Yace gashi kuma ya samu kansa cikin aminci. Ya tambayi wadanda ke wajan taron ko suna cikin aminci? Suka ce masa Eh.
An koma International Kalli Bidiyon: ‘Yan kasar waje Fararen fata sun fara dora hoton Adam A. Zango suna nuna masa kauna bayan da Hadiza Gabon ta ki saka Hotonsa a dakin da take hira da mutane

Lamarin ya koma Kasa da kasa inda aka ga farar fata sun fara dora hoton Adam A. Zango suna nuna masa soyayya. Hakan na zuwane bayan da Hadiza Gabon ta ki saka hoton Adam A Zango a dakin da take hira da mutane wanda lamarin ya jawo cece-kuce sosai. Masoya Adam A. Zango sun yi Caa akan Hadiza Gabon kan wannan lamarin. Wasu dai sun rika cewa wannan itace Mama da Adam A. Zago yawa waka a baya. https://www.tiktok.com/@zainab_sadiq218/video/7579934430471425292?_t=ZS-91xgeNLIOv3&_r=1
Farashin Dala a kasuwar Chanji ta yau

Farashin Dala a kasuwar Chanji ta yau

Duk Labarai
Rahotanni daga kasuwar chanji ta yau na cewa farasin dala na akan Naira N1,450.25 kan kowace dala a kasuwar Gwamnati kenan. A kasuwar Bayan fage kuwa farashin yana kan tsakanin Naira 1,455 zuwa Naira 1,460 akan kowace dala. Masu sharhi a kasuwar dai sun bayyana cewa farashin ya dan daidaita baya yawan hawa da tashi.