Saturday, April 25
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kayan Masarufi zasu yi tsafmda kuma Talauci zai karu, Inji Shugaba Tinubu

Kayan Masarufi zasu yi tsafmda kuma Talauci zai karu, Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi gargadin cewa rikicin gabas ta tsakiya zai iya shafar Najeriya ta hanyar da kayan masarufi zasu yi tsada sannan karancin kudi a hannun mutane zai yi kamari. Shugaban ya bayyana hakane a Legas yayin da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da wasu gwamnoni 23 suka je masa gaisuwar Sallah. Shugaban yace zuwansa Ingila abinda suka fi baiwa muhimmanci shine hadaka da samarwa Najeriya kayan aiki dan magance matsalar tsaro. Shugaba Tinubu yace ya kuma yi magana da shugaban kasar Faransa shima yayi alkawarin baiwa Najeriya kayan aiki dan magance matsalar a tsaro. Yace kuma yana nan yana kara tuntubar sauran wasu shuwagabannin.
Kalli Bidiyon: Idan kuna da wanda ya zamar muku ala kakai, Qadangaren Bakin Tulu, Wanda kuke ga kamar ba za’a iya tureshi ba to ku dage da Addu’a>>Inji Sheikh Mansur Yelwa

Kalli Bidiyon: Idan kuna da wanda ya zamar muku ala kakai, Qadangaren Bakin Tulu, Wanda kuke ga kamar ba za’a iya tureshi ba to ku dage da Addu’a>>Inji Sheikh Mansur Yelwa

Duk Labarai
Sheikh Mansur Isa Yelwa ya bayyana cewa idan akwai wanda mutane suke ganin ya zamar musu Alakakai, wanda suke ganin kamar ba za'a iya Tureshi ba. Yace wanda ake ganin ya shirya, yace to mutane su tashi a yi ta addu' da gaske. Yace ko dai ya sauka da kansa, ko kuma Allah ya saukeshi, yace kuma Allah zai saukeshine ba a doron kasa ba, a kabari. https://twitter.com/i/status/2035842882297356391
Kalli Bidiyon: A Musulunci aka haifeni amma na yi mafarki Jesus na ce min in tafi coci Shiyasa na yi ridda>>Inji Inusa Sa’idu

Kalli Bidiyon: A Musulunci aka haifeni amma na yi mafarki Jesus na ce min in tafi coci Shiyasa na yi ridda>>Inji Inusa Sa’idu

Duk Labarai
Wani me suna Inusa Sa'idu yayi ikirarin cewa a Musulunci aka haifeshi. Yace amma daga baya yayi Mafarki da Jesus yana ce masa ya tafi coci inda yace dalili kenan yayi ridda inda a yanzu ma shi malami ne a kiristanci. Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa daya watsu sosai a kafafen sada zumunta. A wani sashe na Bidiyon nasa, an ganshi yana karatun Qur'ani dan ya tabbatarwa da mutane cewa shi Musulmi ne a da. https://twitter.com/i/status/2035067575483474260
An kama wasu mata masu zaman kansu bayan da sukawa matashi dan bautar kasa taron dangi har ya rigamu gidan gaskiya

An kama wasu mata masu zaman kansu bayan da sukawa matashi dan bautar kasa taron dangi har ya rigamu gidan gaskiya

Duk Labarai
An kama wasu mata masu zaman kansu da sukawa wani matashi dan bautar kasa taron dangi har sai da ya rigamu gidan gaskiya Rahoton yace matashin ya je gidan matan masu zaman kansu ne inda ya dauki daya suka shiga daga ciki. Suna ciki ne sai wasu 4 suma suka shiga suka samesu, anan dai har abinda ya faru ya faru shi kuma ya garzaya barzahu. Sun yi kokarin bashi glucose amma ina. Rahoton yace an kama matan masu zaman kansu dan bincike. https://twitter.com/i/status/2035673262005338301
Kalli Bidiyon: Kyamarar Filin wasa ta Nuno Ali Jita bayan da ya je kallon wasan Sevilla vs Valencia

Kalli Bidiyon: Kyamarar Filin wasa ta Nuno Ali Jita bayan da ya je kallon wasan Sevilla vs Valencia

Duk Labarai
Kyamarar daukar kwallo a wasan da aka yi tsakanin Sevilla vs Valencia ta nuna tauraron mawakin Arewa, Ali Isa Jita rike da Tutar Najeriya. Ali jita yace ya je kallon wasan ne saboda abokinsa, Sadiq. https://www.tiktok.com/@realalijita/video/7620073247471652117?_r=1&_t=ZS-94uBEb4iXom&sp_source=7537614245375297080 https://twitter.com/i/status/2035649223178236045
Hotuna:An yi ganawa tsakanin shuwagabannin tsaron Najeriya dana kasar Ingila

Hotuna:An yi ganawa tsakanin shuwagabannin tsaron Najeriya dana kasar Ingila

Duk Labarai
Ministan tsaro na Najeriya, Janar Christopher Musa ya gana da takwaransa na kasar Ingila, Vernon Coaker. Sun yi ganawar ne a Lancaster House, dake London a yayin ziyarar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zuwa kasar. Sannan sun tattauna maganar tsaro da dangantaka tsakanin kasashen biyu. Musa ya bayyana aniyarsu ta kawar da matsalar tsaro a Najeriya inda kuma ya godewa kasar Ingila bisa taimakon da take baiwa Najeriya wajan magance matsalar tsaro.
Kalli Bidiyon: Wannan magidancin ne yayi Bidiyon da ya fi daukar hankali a wannan sallar

Kalli Bidiyon: Wannan magidancin ne yayi Bidiyon da ya fi daukar hankali a wannan sallar

Duk Labarai
Wannan magidancin shine yayi Bidiyon da rahotanni sun bayyana ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta. Bidiyon nashi an ganshi tare da 'ya'yansa da matarsa suna cin naman sallah suna wata kalar waka da ba'a san me suke cewa ba. Saidai wasu hankalinsu ya kai kan 'ya'yansa inda suke cewa shin wai duka 'ya'yansa ne? https://www.tiktok.com/@bangissmaiwaka/video/7619269284388195604?_r=1&_t=ZS-94tg4qZ0fNR&sp_source=7537614245375297080
Kalli Bidiyon: Yanda wasu Turawa suka shiga matsallaci dake kasarsu ana tsaka da sallah suka jira a kammala sallah su karbi Kalmar Shahada

Kalli Bidiyon: Yanda wasu Turawa suka shiga matsallaci dake kasarsu ana tsaka da sallah suka jira a kammala sallah su karbi Kalmar Shahada

Duk Labarai
Wannan yanda wasu Turawa ne suka shiga masallaci a kasarsu yayin da ake tsaka da sallah. Sun tsaya a baya inda suke jiran a kammala sallar su Karbi Kalmar shahada. Lamarin ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta. https://www.tiktok.com/@islam4u_44/video/7618655784926186783?_r=1&_t=ZS-94tcgVqRXhR&sp_source=7537614245375297080