Wednesday, March 11
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ji abinda Mataimakin Gwamnan Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo yayi kan komawar Abba Kabir Yusuf APC da ya jawo masa yabo

Ji abinda Mataimakin Gwamnan Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo yayi kan komawar Abba Kabir Yusuf APC da ya jawo masa yabo

Duk Labarai
Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo ya bayyana goyon baya ga Kwankwaso a bayyane a yayin da Gwamna, Abba Kabir Yusuf ke shirin komawa APC. An ga Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo a gidan Kwankwaso ranar Laraba a yayin da wasu 'yan kwankwasiyyar suka kaiwa Kwankwaso ziyara a gidansa dake Kano. Ya zauna a kusa da Kwankwaso yayin ganawar wanda da yawa 'yan Kwankwasiyya suka bayyana cewa hakan alamar nuna yana tare da Kwankwaso ne.
Gwamnatin tarayya ta sanar da sabon harajin VAT da ‘yan Najeriya masu amfani da banki zasu biya

Gwamnatin tarayya ta sanar da sabon harajin VAT da ‘yan Najeriya masu amfani da banki zasu biya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bukaci bankuna su fara karbar sabon Harajin VAT na kaso 7.5 akan duk wani amfani da masu hulda da banki suke yi. Za'a rika cire harajinne akan aika kudi, karbar katin ATM, duba balance da sauransu. Kuma Harajin zai fara aiki ne nan da ranar 19 ga watan Janairu, watau Ranar Litinin me zuwa. Tuni dai bankunan suka aikawa masu hulda dasu sanarwar fara karbar Haraji.
Wai dama har yanzu akwai irin wannan Rafalin?>>Dan wasan Najeriya Bright Osayi-Samuel ya tambaya

Wai dama har yanzu akwai irin wannan Rafalin?>>Dan wasan Najeriya Bright Osayi-Samuel ya tambaya

Duk Labarai
Dan wasan Najeriya, Bright Osayi-Samuel yayi tambayar cewa shin wai dama har yanzu akwai irin wannan Rafalin? Ya bayyana hakane bayan wasan Najeriya da Morocco wanda Moroccon ta fitar da Najeriya. Ya bayyana cewa ba wai yace Rafali ne ya fitar dasu ba amma maganar gaskiya ba'a musu Adalci ba. https://twitter.com/i/status/2011601494760444006
Kalli Bidiyon: Wata magana da Kwankwaso yayi da tasa ake ta cewa ko zai koma APC ne

Kalli Bidiyon: Wata magana da Kwankwaso yayi da tasa ake ta cewa ko zai koma APC ne

Duk Labarai
Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa shi fa bai ce ba zai koma APC ba. Yace amma kamin ya koma sai an gaya masa me za'awa Talakawa. Sannan sai an gaya masa shi wane matsayi za'a bashi. Sannan sai an gaya masa matsayin gwamnatin jihar Kano da 'yan majalisarsu. Yace amma har yanzu babu wani da ya sameshi akan hakan. https://twitter.com/i/status/2011530907920806366