Abu na kara Zafafa: Kalli sabon Bidiyon da Hadiza Gabon ta saki dan baiwa Magoya bayan Adam A. Zango dake sukarta Haushi
Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta saki sabon Bidiyon dan baiwa Magoya bayan Adam A. Zango dake sukarta Haushi.
Ta saki Bidiyo ne a Tiktok inda ta dora wakar Gambara da Dapboy ne suna Lokaci.
https://www.tiktok.com/@hadizaaliyugabon/video/7579685550538362134?_t=ZS-91v8pGVhlC5&_r=1
Fada tsakanin Magoya bayan Adam A. Zango da Hadiza Gabon ya samo Asali ne bayan da ta saka hotunan wasu jarumai a dakin da take hira da mutane amma ba'a ga hoton Adam A. Zango ba.
Magoya bayan Adam A. Zango sun rika kiranta da butulu.
Saidai a dazu ta musu martani a Instagram inda tace mutum da gidansa ya kamata ace zai iya yin fendin da ya ga dama.








