Friday, February 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyo: Bana jin tsoronka, Sanata Natasha Akpoti ta gayawa kakakin Majalisar tarayya bayan da yace a fitar da ita daga majalisar

Kalli Bidiyo: Bana jin tsoronka, Sanata Natasha Akpoti ta gayawa kakakin Majalisar tarayya bayan da yace a fitar da ita daga majalisar

Duk Labarai
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bukaci a fitar da sanata Natasha Akpoti daga jikar Kogi daga majalisar. Lamarin ya samo asali ne bayan da sanata Natasha ta bayyana rashin jin dadin canja mata kujerar zama ba tare da saninta ba. Ta tashi tana bayyana rashin jin dadinta ne inda anan ne Sanata Akpabio ya umarci ta fita daga majalisar. Saidai tace ba zata fita ba. Daga karshe dai sai da aka kashe abin maganarta sanan aka samu sa'ida. https://www.tiktok.com/@officialaitlive/video/7473482401713311031?_t=ZM-8u4r9xPcJXj&_r=1 Kalli Bidiyon faruwar lamarin anan:
Nan da ranar 1 ga watan Maris, Gwamnatin Tarayya zata hana motocin dakon man fetur me nauyi hawa titunan Najeriya

Nan da ranar 1 ga watan Maris, Gwamnatin Tarayya zata hana motocin dakon man fetur me nauyi hawa titunan Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da fara hana motoci masu daukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 hawa titunan Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris. Gwamnatin tace zata dauki wannan mataki ne saboda rage yawan hadarurrukan dake faruwa akan titunan Najeriya. Gwamnatin ta bayyana hakane ta bakin hukumar kula da hadadar man fetur ta (NMDPRA). Hukumar tace nan da karshen shekarar 2025 ba zasu bar mota me daukar man fetur sama da lita 45,000 ta rika hawa titunan Najeriya ba. Wakilin hukumar, Ogbugo Ukoha ne ya bayyana hakan a wajan wani taro da ya wakana a Abuja ranar Laraba. Ya kara da cewa an samu cimma matsaya tsakanin hukumar tsaron farin kaya ta DSS da hukumar kula da dokokin hanya ta FRSC, da kungiyar direbobi ta NARTO, da kungiyar ma'aikatan man fetur ta NUPENG, da saur...
Mahaifin Me bankin Access da ya mutu a hadarin jirgin sama me shekaru 90 ya kai jikarsa Kotu saboda Rabon Gado

Mahaifin Me bankin Access da ya mutu a hadarin jirgin sama me shekaru 90 ya kai jikarsa Kotu saboda Rabon Gado

Duk Labarai
Mahaifin Herbert Wigwe me bankin Access Bank wanda ya mutu a hadarin jirgin sama a shekara data gabata ya kai jikarsa, Miss Otutochi Channel Wigwe me shekaru 26 kotu akan maganar rabon gado. Mahaifin me suna Pastor Shyngle Wigwe dan shekaru 90 ya kai Otutochi da wasu kotu inda yake neman kotun data saka wani ya kula da dukiyar dan nasa. A doka ana saka wani ya kula da dukiyar mamacine idan mamacin ya mutu be bar wasiyya ba. Saidai zuwa yanzu, kotun bata amince masa akan wannan bujata ba
Iliyasu Muhammad ya gayyaci abokinsa gida ya kkàshèshì yayin da yake tsaka da cin Abinci a Abuja

Iliyasu Muhammad ya gayyaci abokinsa gida ya kkàshèshì yayin da yake tsaka da cin Abinci a Abuja

Duk Labarai
Wani matashi me suna Iliyasu Muhammad dake zaune a Dantata Village a babban barnin tarayya Abuja ya kashe abokinsa ta hanyar datsashi da adda. Iiliyasu ya gayyaci abokinsa, Saifullahi Muhammad gidansa dan cin abinci inda a yayin da Saifullahi ke cin abincin ne, Iliyasu ya hau kansa da sara. Kakakin 'yansandan Birnin Tarayya, Abuja, Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace an kirasu ranar February 13, 2025 da misalin karfe 1:30 na rana inda aka sanar dasu abinda ya faru. Tace da suka je sun iske Saifullahi cikin jini inda suka kwasheshi zuwa Asibiti inda likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu. Tace an kama Iliyasu kuma ya amsa laifinsa. Ta kara da cewa, da bincike yayi tsanani, sun gano Iliyasu na tare da wasu gungun mugayene dake yiwa masu mashina kwace a Abuj...
Cutar Zazzabin Lassa ta kkàshè mutane 10 a Najeriya

Cutar Zazzabin Lassa ta kkàshè mutane 10 a Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, cutar zazzabin Lassa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 a Najeriya. Lamarin ya farune a jihohin Bauchi, Ondo, Taraba, Edo, Benue, Gombe, Kogi, da Ebonyi. A shekarar da muke ciki, cutar ta kashe jimullar mutane 80 a kananan jihohi 63 na jihohi 11. Hukumar kula da lafiya ta kasa, NCDC ce ta bayyana hakan a sanarwar da take fitarwa ta mako-mako.
Baturiya ta kai Asibiti kotu a kasar Amurka bayan data nemi a saka mata maniyyin farin namiji amma aka samu kuskure aka saka mata maniyyin bakin namiji ta haifi jariri bakar fata

Baturiya ta kai Asibiti kotu a kasar Amurka bayan data nemi a saka mata maniyyin farin namiji amma aka samu kuskure aka saka mata maniyyin bakin namiji ta haifi jariri bakar fata

Duk Labarai
Wata baturiya a kasar Amurka ta kai Asibiti kotu saboda kuskure wajan zuba mata maniyyi da aka yi. Matar me suna Krystena Murray 'yar kimanin shekaru 38 ta zabi namiji me kama da itane farar fata inda tace a saka mata maniyyinsa. Saidai an samu kuskure aka saka mata maniyyin namiji bakar fata kuma ta haifi jariri bakar fata, saidai duk da haka ta kudiri aniyar ci gaba da renon jariri. Saidai daga baya masu maniyyin ashe suma sun ajiyene dan amfani dashi nan gaba, inda suka kaita kara wanda a dole ba tana so ba ta basu jaririnsu. Saidai itama yanzu ta kai Asibitin me suna Coastal Fertility Specialists kara inda take neman a bi mata hakkinta kan wannan kuskure da suka tafka akanta. Ta shigar da karar ne a Kotun, Chatham County dake Georgia. Ta bayyana cewa, babban burinta ...
Kalli Bidiyon tsiraici na wannan ‘yar Siyasar ya bayyana, kunya ta hanata zuwa aiki

Kalli Bidiyon tsiraici na wannan ‘yar Siyasar ya bayyana, kunya ta hanata zuwa aiki

Duk Labarai
Bidiyon tsiraici na Wata 'yar siyasa me suna Mayor Nora Mahlangu ya bayyana a kafafen sada zumunta inda aka ganta tana cire kayanta sai da ta yi Tumbur haihuwar uwarta. Matar dai itace magajiyar garin Ngaka Modiri sannan 'yar jam'iyyar ANC ce ta kasar Afrika ta kudu. Rahotanni sun ce da kanta ta yi kuskuren aika wannan hoto nata na batsa a cikin WhatsApp Group na Jam'iyyarsu. Rahotanni sunce tuni ta nemi hutu ta daina zuwa aiki saboda kunya. Kasancewar tsiraicin dake cikin bidiyon yayi yawa yasa ba zamu iya wallafa muku shi anan ba.
Kalli Bidiyon yanda aka kama wasu masu Gàrkùwà da mutane aka musu tsìràrà ana duka kamar jakai

Kalli Bidiyon yanda aka kama wasu masu Gàrkùwà da mutane aka musu tsìràrà ana duka kamar jakai

Duk Labarai
Wadannan wasu masu garkuwa da mutanene da aka kama a Legas inda ake dukansu kamar jakai inda aka cire musu kayan jikinsu. Daya daga cikinsu yace daga jihar Kwara yake inda dayan yace ya fito ne daga jihar Anambra sai kuma dayan yace ya fito ne daga jihar Imo. Sun dai amsa laifinsu na cewa sun je yin garkuwa da mutanene saidai sun sha Alwashin ba zasu sake aikata hakan ba. Kalli Bidiyon anan
Akwai Tubabbun ‘yan Bìndìgà 789 da muke canjawa hali zamu kuma mayar dasu cikin al’umma su zauna>>Inji Sojoji

Akwai Tubabbun ‘yan Bìndìgà 789 da muke canjawa hali zamu kuma mayar dasu cikin al’umma su zauna>>Inji Sojoji

Duk Labarai
Shugaban sojojin Najariya, Gen. Christopher Musa ya bayyana cewa, akwai Tubabbun 'yan Bindiga 789 da suke canjawa hali kuma zasu mayar dasu cikin mutane su zauna. Musa ya bayyana hakane a wajan wani taron masu ruwa da tsaki da ya wakana ranar Talata a Abuja. Yace An samu 'yan Bindigar da yawa hakane saboda 'yan Bòkò Hàràm da yawa da ake samu suna tuba. Yace jimullar 'yan Bòkò Hàràm 120,000 ne suka tuba suka mika wuya tun bayan da aka fito da tsarin karbar tubabbun 'yan Bòkò Hàràm din dan canja musu hali. Ya kara da cewa, yanzu haka akwai guda 789 da ake shirin yayewa daga shirin na canja musu hali dan su koma cikin jama'a da zama.
‘Yar Fim Halima Abubakar ta roki mutane su tausaya mata, inda tace ta sayar da motocinta 3 ta koma kauye da zama gaba daya ta talauce bata da ko sisi

‘Yar Fim Halima Abubakar ta roki mutane su tausaya mata, inda tace ta sayar da motocinta 3 ta koma kauye da zama gaba daya ta talauce bata da ko sisi

Duk Labarai
Shahararriyar Tauraruwar fina-finan kudu, Halima Abubakar ta bayyana a wani Bidiyo tana neman taimakon jama'a inda tace ta talauce. Ta bayyana hakane a shafinta na Instagram inda tace itace da kanta ba karya ba. Tace ta Talauce ta yanda yanzu haka ta sayar da motocin ta 3 inda ta koma kauyensu da zama. Tace ta gaji da rokon mutane 'yan uwa da abokan arziki kudi shine ta fito take son jama'a su taimaka mata inda ta ajiye account Number. Tace an dakatar da ita daga harkar fim ta Nollywood dan haka yanzu bata da aikin yi.