Tuesday, December 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

‘Yan Kudu na koyon Hausa wai dan koda wataran zasu hadu da tshàgyèràn Dhàjì sai su rokesu

‘Yan Kudu na koyon Hausa wai dan koda wataran zasu hadu da tshàgyèràn Dhàjì sai su rokesu

Duk Labarai
Wasu 'yan Kudu sun fara koyon Hausa wai dan ko da watarana sun hadu da tsageran daji sai su rokesu su kyalesu. Sun rika tambayar Google ya fassara musu wasu kalamai musamman na rokon ko na neman afuwa. Matsalar 'yan Bindiga ta yi kamari sosai a Najeriya inda ake garkuwa da mutane dan neman kudin fansa a wasu lokutan ma mutane na rasa rayukansu. https://twitter.com/YKoluwaseun9/status/1992235636330549393?t=cP2mwH8AlSxOfFxhRfddIA&s=19
Kalli Bidiyo: Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayar da Umarnin yin Azumi a jiharsa dan Rokon Allah ya magance matsalar tsaro

Kalli Bidiyo: Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayar da Umarnin yin Azumi a jiharsa dan Rokon Allah ya magance matsalar tsaro

Duk Labarai
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayar da Umarni a jiharsa ta Borno cewa mutane su tashi da Azumi dan a roki Allah ya magance matsalar tsaro a jihar. Gwamnan yace za'a tashi da Azuminne ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamba inda yace a hada da addu'o'i musamman saboda dawowar Kungiyar Bòkò Hàràm inda take ci gaba da kai hare-hare a jihar https://twitter.com/channelstv/status/1992248596503355762?t=xFdhZnfTKx1zNNBgrO-srA&s=19 Wannan na zuwane Kwanaki kadan bayan da Kungiyar ta Bòkò Hàràm ta Khashye Janar din Soja, Muhammad Uba.
Kalli Bidiyon Dansanda cikin Dariya yana cewa, ‘yan Mata ‘yan Makarantar Jihar Kebbi na cikin Tasku dan kuwa kullun sai An aikata Alfasha dasu, Yanzu haka ma duk sun dauki ciki

Kalli Bidiyon Dansanda cikin Dariya yana cewa, ‘yan Mata ‘yan Makarantar Jihar Kebbi na cikin Tasku dan kuwa kullun sai An aikata Alfasha dasu, Yanzu haka ma duk sun dauki ciki

Duk Labarai
Wani Dansandan Najeriya ya dauki hankula bayan da aka ga Bidiyonsa yana fadar kalaman da basu dace ba akan 'yan mata 'yan makarantar jihar Kebbi da aka yi garkuwa dasu. An gan shi a wajan wani cin Abinci inda yake cewa Allah ya tsareshi kada a aikashi ya kubutar da 'yan matan. Sannan yace kullun ne sai 'yan Bindigar sun aikata alfasha da 'yan matan, yanzu haka ma duk sun dauki ciki. Wannan kalamai nasa dai sun jawo cece-kuce inda da yawa ke Allah wadai da abinda ya fada wasu ma na kiran a koreshi daga aiki. Da yawa sun bayyana cewa, Abin kunya ne irin wadannan kalamai na fitowa daga jami'in tsaro. https://www.tiktok.com/@jecintakelvin0/video/7575571312286993685?_t=ZS-91dOXqaOg4X&_r=1 https://twitter.com/AsakyGRN/status/1991998539740893634?t=b6I3FfCOsWEMIBlfJrQu6Q&a...
Farfesa Sheriff Muhammad Ibrahim ya koka da cewa, Fulani sun tura shanu sun cinye masa gonar shinkafa

Farfesa Sheriff Muhammad Ibrahim ya koka da cewa, Fulani sun tura shanu sun cinye masa gonar shinkafa

Duk Labarai
Farfesa Sheriff Muhammad Ibrahim ya bayyana cewa Fulani makiyaya sun shiga gonar shinkafarsa sun cinye masa ita. Ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook inda da yawa suka jajanta masa. Ga sakonsa kamar haka: Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun Dukkan mai bibiyata ya san irin kokarin da nake yi wajen aikin noma, mun yi duk abunda ya dace kuma gona ta yi kyau sosai, duk da cewa dagangan Gomnati ke karya manoma, hakan bai hana mu dage aikin aikin mu ba. Sai kuma yau na wayi gari da mummunan labarin cewa makiyaya sun cinye mun gona. Bara ma haka suka yi, suka jawo mun hasara mai yawa, na yi magana suka ce bana son zaman lafiya, ga shi ba na sun saka shanun su sun cinye mun gona ta cikin dare da garken shanu kusan 500. Lallai ina cikin ma su kwadaitar da mutane su yi noma, amm...
Wallahi ba da wasa nake ba, Soyayyar Matar tsohon shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari ta kamani, kuma wallahi in tace bata sona ban san yanda zan yi ba>>Inji Matashi dan Tiktok

Wallahi ba da wasa nake ba, Soyayyar Matar tsohon shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari ta kamani, kuma wallahi in tace bata sona ban san yanda zan yi ba>>Inji Matashi dan Tiktok

Duk Labarai
Wannan matashin dan Tiktok ya bayyana cewa, Soyayyar Matar Tsohon shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta kamashi. Ya bayyana hakane a shafinsa na Tiktok inda yace kuma a shirye yane ya fuskanci kowane irin kalubale akan wannan buri nasa. Matashin yace ko da za'a azabtar dashi bai damu ba. Yace zai kasance tare sa A'isha Buhari da jiya mata jin dadin Rayuwa har karshen rayuwarsa. https://www.tiktok.com/@umarpitykhalid0/video/7575501573149723911?_t=ZS-91cDYptOa4v&_r=1
Kalli Bidiyon: Ministan Tsaro Bello Matawalle ya tabbatar da kama Sojojin da ake zargi da kaucewa suka baiwa tshàgyèràn daji dama suka Dàwùkì daliban jihar Kebbi

Kalli Bidiyon: Ministan Tsaro Bello Matawalle ya tabbatar da kama Sojojin da ake zargi da kaucewa suka baiwa tshàgyèràn daji dama suka Dàwùkì daliban jihar Kebbi

Duk Labarai
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya tabbatar da kama sojojin da aka kai su bayar da tsaro a makarantar 'yan Mata dake jihar Kebbi amma suka tafi shagalinsu aka je aka dauke 'yanmatan. Ministan yace an kama sojojin ana kan Bincike kuma idan aka tabbatar da abinda ake zarginsu za'a musu hukunci daidai da abinda doka ta tanada. https://www.tiktok.com/@abdoulsheh/video/7575202184497761543?_t=ZS-91c93bjJ0bp&_r=1
Ban ji dadin Hukuncin daurin rai da rai da aka yankewa Nnamdy Khanu ba, ba hakan ne mafita ba>>Inji Peter Obi

Ban ji dadin Hukuncin daurin rai da rai da aka yankewa Nnamdy Khanu ba, ba hakan ne mafita ba>>Inji Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 a jam'iyyar Labour party, Peter Obi ya bayyana cewa, sam bai ji dadin Hukuncin daurin rai da rai da aka yankewa Nnamdy Khanu ba. Ya bayyana cewa tin farko bai goyi bayan kama Nnamdi Kanu ba. Yace irin abinda Nnamdi Kanu ya zo dashi zama ake yi a yo sulhu ba da karfi ake amfani ba. Kotun tarayya dake Abuja dai ta yankewa Nnamdy Khanu hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da laifin ta'ddanci. Rahotanni sun ce tuni aka kaishi gidan yarin dake jihar Sokoto.
Da Duminsa: Najeriya banzar kasa ce, kuma Ana Mhuzghunawa Kiristoci, idan Gwamnati bata dauki mataki ba tabbas zan kai Khari>>Trump ya sake nanatawa

Da Duminsa: Najeriya banzar kasa ce, kuma Ana Mhuzghunawa Kiristoci, idan Gwamnati bata dauki mataki ba tabbas zan kai Khari>>Trump ya sake nanatawa

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana nan kan bakansa na dakatar da tallafin da ya ke baiwa Najeriya idan ba'a daina yiwa Kiristoci Khisan Kyiyashi ba. tTrump ya bayyana hakane a wata ganawa da aka yi dashi a gidan wani Radio. Trump yace Ana kashe dubban Kiristoci a Najeriya kuma idan Gwamnati bata dauki matakan da suka dace ba zai kai hari dan gamawa da masu tsatstsauran ra'ayin addinin Islama. Trump dai ya ci gaba da nanata maganar inda yace abin yana bata masa rai sosai.
Kalli Bidiyon: Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya jaddada Fatawarsa ta cewa akwai inda aka yadda mace ta yi shugabanci duk da Sùkàr da ake masa

Kalli Bidiyon: Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya jaddada Fatawarsa ta cewa akwai inda aka yadda mace ta yi shugabanci duk da Sùkàr da ake masa

Duk Labarai
Babban malamin addinin Islama, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa, Akwai fatawowi akan shugabancin mace. Yace akwai malaman da suka ce kwata-kwata mace ba zata yi shugabanci ba, akwai wanda suka ce zata iya yin shugabanci a wasu kebantattun gurare Sannan Akwai wanda suka yadda zata iya yin kowane shugabanci. Malam yace shi a na tsakiya yake, kuma ba zai daina bayyana fatawar da ya yadda da ita ba. https://www.tiktok.com/@nurasara531/video/7575277364813286663?_t=ZS-91bwZZVvwm1&_r=1 Malam ya bayyana hakane bayan sukar da ake masa biyo bayan fatawar da ya baiwa wata mata cewa zata iya yin shugabanci