Wata Sabuwa: Gwamnati na shirin kara farashin man fetur zuwa Naira 1,405 dan tatsar kudaden da zata biya bashin da ‘yan kasuwar man fetur ke binta
Wani sabon rahoton da ya bayyana na nuni da cewa za'a kara farashin man fetur zuwa akalla Naira 1000 akan kowace lita.
'Yan kasuwar man fetur din ne suka bayyanawa jaridar Vanguard hakan a wata zantawa da ta yi dasu.
Hakan na zuwane bayan da kamfanin man fetur na kasa,NNPCL ya koka da bashin da ya masa yawa na 'yan kasuwar man fetur da suke kawo man a matsayin bashi.
'Yan kasuwar dai da yawa wanda na kssa da kasa ne aun ce sun daina kawowa Najeriya mai a bashi har sai an biyasu bashin da suke bi.
Hakan yasa gwamnati zata iya kara farashin man fetur din dan ta samu kudaden da zata biya wancan bashin da ake binta.
Ko kuma ta raba ta biya rabi 'yan kasa su biya rabi, hakanan kuma hakan na nufin lallai fa sai an kara farashin man saboda a yanzu gwamnati bata da kudin da zata ci ...








