Sunday, June 28
Shadow

Author: Bashir Ahmed

A farashin 898 muka sayi man fetur daga matatar man Dangote>>NNPCL

A farashin 898 muka sayi man fetur daga matatar man Dangote>>NNPCL

Duk Labarai
Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya bayyana cewa, a farashin Naira 898 suka sayi man fetur daga matatar man fetur ta Dangote. A yau ne dai kamfanin na NNPCL suka fara daukar man fetur din daga matatar man ta Dangote bayan shan dambarwa tsakanin Gwamnati da matatar man. Masu sharhi da yawa na ganin cewa, sayen man fetur din a wannan farashin daga matatar Dangote na nufin bata canja zani ba. Inda wasu ke zargin cewa, Gwamnati ce ta yi kaka gida a lamarin shiyasa man yayi tsada haka. A baya dai ana tsammanin matatar man fetur ta Dangote zata kawo saukin Man fetur a kasarnan amma hakan da kamar wuya.
Kalli Bidiyon yanda mataimakin shugaban kasa ya yanke jiki ya fadi yana tsaka da jawabi

Kalli Bidiyon yanda mataimakin shugaban kasa ya yanke jiki ya fadi yana tsaka da jawabi

Duk Labarai
Mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu, Paul Mashatile ya yanke jiki ya fadi yana tsaka da jawabi. Bidiyon faruwar lamarin ya yadu a kafafen sada zumunta sosai. Lamarin ya farune a garin Tzaneen dake Limpopo na kasar. https://www.youtube.com/watch?v=ueg3tH9HQPo?si=6TJ8xuSioycqCIlS Rahotanni sunce mataimakin shugaban kasar ya fadi ne saboda tsananin zafi da ake yi. Ba dai a kaishi Asibiti ba dan lamarin bai yi muni ba.
Sojan da ya daure Abbas tsawon shekara 6 saboda ya je Sallah na shan Tofin Allah Tsine

Sojan da ya daure Abbas tsawon shekara 6 saboda ya je Sallah na shan Tofin Allah Tsine

Duk Labarai
Sojan Najeriya, M.S Adamu wanda ake zargin ya daure karamin soja, Abbas na shan Allah wadai da kiran a hukuntashi saboda hukuncin da yawa Abbas yayi tsauri. Matar Abbas ce dai ta je kafar Berekete Family inda ta bayyana cewa an daure mijinta bayan da yaje Sallah ya dawo ba tare da neman izini ba. Sannan ogansa na magana shima yana magana. An daureshi dai bayan da kansa ya daku ya rika fitar da Jini wanda hakan yasa kwakwalwarsa ta tabu ya samu tabin hankali. Daga baya dai an kaishi Asibiti aka masa magani.
Matar soja Abbas mai suna Husaina Iliyasu ta cika gwarzuwa kuma jarumar da samun irin ta sai an tara mata 1000

Matar soja Abbas mai suna Husaina Iliyasu ta cika gwarzuwa kuma jarumar da samun irin ta sai an tara mata 1000

Duk Labarai
TSANTSAR RASHIƝ IMÁNI DA TAÚSÁYI Matar soja Abbas mai suna Husaina Iliyasu ta cika gwarzuwa kuma jarumar da samun irin ta sai an tara mata 1000. Mijinta soja ne Mųsưlmi wanda daga zuwa yin Sálląh yayin da ake bakin aiki shine ogansa ya sa shi a gaba shekara da shekaru a garƙame sai da ya haukatar da shi. Tsantsar tsagwaron rashin imani ya ƙare a wannan labarin. Shin ina manyan Musulmi dake aikin soja a ƙasar nan? Shin wa ya ce a keta alfarmar ɗan adam saboda bambancin addini a aikin soja? Ina kungiyoyin kare hakkin mata? Ina kungiyar kare hakkin dan Adam? Ina kungiyar manyan Arewa? Ina kungiyar lauyoyi Musulmi? Ina kungiyar Malaman mu? Ina kungiyar yan jaridun kasar nan? Mutun ya sadaukar da rayuwar sa don ya kare ƙasa amma a ƙarshe saboda son zuciyar wani a mayar da...
Wannan an ce shine sojan da ya kashe ƙasurgumin ɗan bindigar nan Halilu Sububu, da wasu gaggan yaran ɗan bindigar

Wannan an ce shine sojan da ya kashe ƙasurgumin ɗan bindigar nan Halilu Sububu, da wasu gaggan yaran ɗan bindigar

Duk Labarai
Wannan an ce shine sojan da ya kashe ƙasurgumin ɗan bindigar nan Halilu Sububu, da wasu gaggan yaran ɗan bindigar. Waɗanda suka addabi al'ummar jihar Zamfara da sauran jihohin Arewa. An tabbatar da jarumi ne na yankan shakku, domin ance harda hannu yake kama ƴan bindiga. Allah ya ƙara kare shi a wannan aiki da yake yi. Ya kuma ƙara bashi nasara da sauran abokan aikinsa. Daga Zakari Y Adamu Kontagora
Ji Farashin da Dangote zai sayar da man fetur dinsa

Ji Farashin da Dangote zai sayar da man fetur dinsa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa farashin man fetur daga matatar man Dangote zai iya kaiwa Naira 857 zuwa 865. Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya bayyana cewa, zai dauki man daga matatar man Dangote a farashin Naira 960 zuwa 980 akan kowace lita inda zai sayarwa da 'yan kasuwa akan farashin 850 zuwa 840. Saidai babu tabbacin ko za'a samu farashin bai daya a duka gidajen man sayar da fetur din a Najeriya. Me kula da yada labarai na kamfanin na NNPCL Olufemi Soneye ya tabbatar da cewa a ranar 15 ga watan Satumba ne zasu fara dakon man fetur din daga matatar man Dangote.

Kalli Bidiyo: Motocin dakon man fetur sun fara jigilar man daga matatar Dangote

Duk Labarai
Kamfanin matatar man fetur ta Dangote ta wallafa Bidiyon da ya nuna motocin jigilar Man fetur da suka fara jigilar man a matatar man fetur din. https://www.youtube.com/watch?v=Y9Lj_0YGDW8?si=X1CwcZDsQq5n6CW_ An fara jigilar man fetur dinne daga matatar man fetur ta Dangote bayan Dambarwar da aka sha ta cece-kuce tsakaninsa da Kamfanin mai na kasa NNPCL da kuma Gwamnatin Tarayya.
Kalli bidiyo: Yanda Wata Nurse ta yankewa likita Azzakarinsa yayin da yayi yunkurin yi mata fyade

Kalli bidiyo: Yanda Wata Nurse ta yankewa likita Azzakarinsa yayin da yayi yunkurin yi mata fyade

Duk Labarai
Wata ma'aikaciyar Jinya,Nurse dake aiki a wani Asibiti dake Bihar me suna RBS Health Care Centre ta gamu da barazanar fyade. https://www.youtube.com/watch?v=hzBaAm1qLmM?si=0YtpIarh3h_63I4R Likitan Asibitin da take aiki da wasu 3 ne suka so yi mata fyade amma basu yi nasara ba. Likitan me suna Dr Sanjay Kumar da abokan aikinsa, Sunil Kumar Gupta da Awadhesh Kumar ne suka aha giya suka yi mankas. Suka kulle kofofin shiga Asibitin inda suka afka mata. Nan dai Allah ya bata sa'a ta kama azzakarin babban likitan ta yanke da wukar fida. Ta samu ta fita da gudu kamar yanda kafar Livemint ta ruwaito. Ta samu wani waje ta labe inda ta kira 'Yansanda suka zo suka kama likitocin. Likitan dai yana can yana karbar kulawa ta musamman inda ake ci gaba da bincike.
Matar shugaban kasa,Remi Tinubu ta kashe Naira Miliyan Dari bakwai wajan yawon zuwa kasashen Duniya a cikin watanni 3 kacal

Matar shugaban kasa,Remi Tinubu ta kashe Naira Miliyan Dari bakwai wajan yawon zuwa kasashen Duniya a cikin watanni 3 kacal

Duk Labarai
Matar Shugaban kasa,Remi Tinubu ta kashe Naira Miliyan 701 a zagayen da ta yi a kasashen Duniya guda 5. Ko da a shekarar 2023 sai da fadar shugaban kasa ta warewa ofishin matar shugaban kasar Naira Biliyan 1.5 dan saya mata motoci na Alfarma. An gano hakanne a kundin tattara bayanai na gwamnatin tarayya na yanar gizo. Bayan wannan kuma, Gwamnatin ta kashewa Matar shugaban kasar Naira Miliyan 314 wajan shirya taruka a cikin gida Najeriya.