Karin farashin man fetur zai nunkawa ‘yan Najeriya wahalar da suke ciki>>Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta gayawa Tinubu
Kungiyar kishin Yarbawa ta Afenifere ta koka kan karin farashin man fetur da kamfanin mai na kasa,NNPCL yayi.
Kamfanin NNPCL ya kara farashin man fetur din daga Naira 617 zuwa Naira 897 akan kowace lita.
Kakakin Afenifere Mr Jare Ajayi yace ta yaya kamfanin na NNPCL da bai dade da cewar ya samu riba ba amma a yanzu zai ce wai ana binsa bashi.
Kungiyar tace tana baiwa shugaban kasar shawarar da ya yiwa NNPCL magana a maida man farashinsa na baya idan kuwa ba haka ba,wahalar da za'a shiga zata shafe duk wani ci gaban da aka samu a karkashin gwamnatinsa.