Thursday, January 9
Shadow

Duk Labarai

‘Yan Sanda Sun Kwato Motar Sata, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Jigawa

‘Yan Sanda Sun Kwato Motar Sata, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Jigawa

Tsaro
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani mutum mai suna Mahmud Adam mai shekaru 43 da laifin satar mota, tare da gano motar kirar SUV da aka sace a karamar hukumar Gwaram. DSP Shiisu Adam, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jigawa, ya sanar da hakan a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni, cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar, 15 ga watan Yuni. A cewar Shiisu, kama barawon ya biyo bayan rahoton sace wata mota kirar Honda CRV mai lamba DKD 10 AG mallakin Wani Abba Yahya daga garin Gano da ke karamar hukumar Dawakin Kudu ta jihar Kano. Ya ce motar tana kan hanyar zuwa Maiduguri jihar Borno. Ya bayyana cewa, jami’in ‘yan sanda (DPO) na Gwaram tare da tawagarsa sun tare motar kirar SUV akan hanyar Sara zuwa Darazo. SHiisu ya ce tuni aka mika wanda ake zargin da ...
Wannan ai Shedanne, mutane suka rika cewa yayin da aka ga wannan matashi ana sallah shi kuma yana daukar hoto

Wannan ai Shedanne, mutane suka rika cewa yayin da aka ga wannan matashi ana sallah shi kuma yana daukar hoto

Duk Labarai
Wannan hoton ya dauki hankula sosai a shafukan sada zumunta inda aka ga wani matashi yana daukar hoto yayin da ake Sallar Idi. https://twitter.com/ibrahimtashboi/status/1802439160084759037?t=F6_AUnKPRIIrE9PpVca8Aw&s=19 https://twitter.com/EmesDos1/status/1802417436966174863?t=OPElzhGrtqNv7JhtzFBY9A&s=19 https://twitter.com/Abbakr_Abbaty/status/1802376022802702542?t=LVT3XMoZKbhlpN7KJPeI5Q&s=19 https://twitter.com/jiddah_mk/status/1802402291959373960?t=0fx1YU9ewy-FK_it8Mat9w&s=19 https://twitter.com/ummer_zeee/status/1802375684930589145?t=k1LWW10JPU0euYreEMjOqg&s=19 Hoton ya nuna maza da mata a yamutse a waje daya ana Sallah sannan wasu na cewa ma ba'a daidaita sahu ba. Hoton ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta.
“Mataimakin Gwamna A Najeriya Kamar Ba Ka Da Aiki Ne” — Tsohon Mataimakin Gwamna

“Mataimakin Gwamna A Najeriya Kamar Ba Ka Da Aiki Ne” — Tsohon Mataimakin Gwamna

Siyasa
Yanzu haka dai wani tsohon ministan lantarki kuma tsohon mataimakin gwamna a jihar Yobe, ya ce babban sirrin zama mataimakin gwamna da gwamnan kansa shi ne yin gaskiya da riƙon amana da kuma biyayya. Injiniya Abubakar D. Aliyu ya ce duk da yake tsarin mulkin Najeriya ne ya tanadi muƙamin mataimakin gwamna, amma kuma bai tanadar masa wani taƙamaiman aiki ba, don haka “in dai kana so ka yi, ka zauna kawai. Abin da gwamna ya ce ka yi, ka yi. In ya ce kar ka yi, ka bari”. A cewarsa: “Ba zancen kai Mataimakin gwamna (ne ba), ai tare muka je mu kai kamfen, ai tare muka je! Ai gwamnatin, tsarin mulki ne yake ajiye ta, to kai kuma tsarin mulki ba abin da ya ba ka”. Tsohon Ministan ya Bayyana hakan ne a jerin hirarrakin da BBC ta yi da wasu jiga-jigan ‘yan siyasar Najeriya albarkacin cikar...
Ƴan bindiga sun sace mutane masu yawa ranar sallah a ƙauyen Dudun Doki na ƙaramar hukumar Gwadabawa ta jihar Sokoto

Ƴan bindiga sun sace mutane masu yawa ranar sallah a ƙauyen Dudun Doki na ƙaramar hukumar Gwadabawa ta jihar Sokoto

Sokoto, Tsaro
ANA BIKIN SALLAH YAN BINDIGA SUN TAFKA MUMMUNAN BARNA A SOKOTO. Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kai hari wani kauye a jihar Sokoto, inda suka kashe kuma suka sace mutane da dama da sanyin safiyar Lahadi Maharan sun farmaki kauyen Dudun Doki a karamar hukumar Gwadabawa ta jihar, suka kashe mutane sama da goma, kamar yadda aka ruwaito An ruwaito cewa, har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan lamarin ba. Allah ta'ala yakawo mana zaman lafiya alfarmar Al-qur'ani.
Ya kamata a wayar da kan Mutane: Irin yanda yawan mutane ke karuwa a Najeriya na damuna>>Shugaba Buhari

Ya kamata a wayar da kan Mutane: Irin yanda yawan mutane ke karuwa a Najeriya na damuna>>Shugaba Buhari

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, irin yanda yawan mutane ke karuwa a Najeriya lamarin na damunshi. Ya bayar da shawarar cewa, ya kamata a wayar da kawunan mutane game da hakan. Shugaban ya bayyana hakane bayan kammala sallar Idi a jiya, Lahadi. Ya kuma bayyana farin cikinsa kan yanda mutane da yawa suka rungumi harkar Noma. Shugaban yace nasarar kasa ta dogara ne akan zamun shuwagabanni masu nasara akai-akai.