Thursday, January 9
Shadow

Duk Labarai

Maganin ciwon zuciya na Gargajiya

Ciwon Zuciya, Duk Labarai
Ciwon zuciya wanda yayi tsanani yana bukatar kulawar kwararren likita, saidai idan bai yi tsanani ba, ana iya amfani da magungunan gargajiya wajan maganceta Irin ciwon zuciyar da ake magancewa a gida shine wanda baya faruwa a kullun, watau na dan lokacine, sai kuma damuwa, da daurewar gabobi, sai da yawan gyatsa. Wasu lokutan akwai wahala wajan gane ko banbance kalar ciwon zuciyar da ya kamata a magance a gida da wanda ya kamata aje Asibiti. Idan aka ji wadannan alamu na kasa to a je Asibiti: Ciwin kirji idan ya yi tsanani yana daurewa, yayi nauyi ko yana nusar mutum. Idan mutum ya ji kamar zuciyarsa zata buga. Idan aka ji alamar numfashi na neman daukewa. Idan ba'a ji wadannan alamu na sama ba to za'a iya gwada maganin gargajiya na gida kamar haka: Ana iya samun ts...
Kalli Hoto:An kamata saboda turawa karamar yarinya me shekaru 12 icce cikin al’aura saboda zargin sata

Kalli Hoto:An kamata saboda turawa karamar yarinya me shekaru 12 icce cikin al’aura saboda zargin sata

Duk Labarai
An kama wannan matar me suna Temitope Adetanju 'Yar Kimanin shekaru 25 saboda turawa karamar yarinya me shekaru 12 icce cikin farjinta. An zargi yarinyar ne da satar Biskit na Naira 200 da Milo na 150 sai kayan marmari na Naira 300. Rahoton yace an azabtar da yarinyar sosai saboda wannan zargi. Lamarin ya farune a Isewo, Obada Oko, dake karamar hukumar Ewekoro na jihar Ogun. Kakakin 'yansandan jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace wadda ake zargin ta amsa laifinta amma suna ci gaba da bincike.
Kuma Dai: Kungiyar Kwadago, NLC tace zata iya amincewa idan gwamnati ta biya kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin(250,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Kuma Dai: Kungiyar Kwadago, NLC tace zata iya amincewa idan gwamnati ta biya kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin(250,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Siyasa
Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa bata nace akan sai gwamnatin tarayya ta biya naira dubu dari biyu da hamsin(250,000) ba a matsayin mafi karancin Albashi ba. Shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa dashi. Yace a shirye suke su amince da kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin (250,00) a matsayin mafi karancin Albashin. Gwamnatin tarayya dai bata bayyana matsayar ta ba kan mafi karancin albashin ba.
Kwamitin Majalisar Wakilai Ya Bada Shawarar Samawa Tinubu Da Shettima Sabbin Jiragen Sama

Kwamitin Majalisar Wakilai Ya Bada Shawarar Samawa Tinubu Da Shettima Sabbin Jiragen Sama

Siyasa
Kwamitin Majalisar Wakilai akan Tsaron Kasa da Tattara Bayanan Sirri ya bukaci gwamnatin tarayya ta sayawa Shugaban Kasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima sabbin jiragen sama. Shawarar kwamitin na kunshe ne a cikin rahoton da kwamitin ya fitar bayan gudanar da bincike akan lafiyar jiragen saman fadar shugaban kasa. A watan Mayun daya gabata, majalisar wakilan ta umarci kwamitin ya gudanar da cikakken bincike akan jiragen saman fadar shugaban kasar domin tantance lafiyarsu. Shawarar ta biyo bayan kudirin da Dan Majalisa Satomi Ahmad ya gabatar, wanda aka tafka mahawara akan sa. Wasu daga cikin 'yan majalisar sun bada shawarar cewar kamata yayi shugaban kasar ya rika shiga jirgin sama ko motar haya idan zai yi balaguro. Kudirin na Satomi Ahmad ya biyo bayan rahoton s...

Alamomin ciwon zuciya

Ciwon Zuciya, Duk Labarai
Ciwon zuciya ya danganta da irin zuciyar, akwaishi kala-kala. Dan haka bari mu bayyana alamomin ciwon zuciya daban-daban. Akwai wanda ake kira da Coronary artery disease: Wannan kalar ciwon zuciya ne dake taba hanyoyin dake baiwa zuciyar jini. Wannan kalar ciwon zuciya shine wanda yafi kama mutane kuma yakan kai ga Bugawar Zuciya da ke iya kaiwa ga mutuwa, Yakan kuma kai ga ciwon kirji, ko shanyewar rabin jiki. Alamomin wannan ciwon zuciya ya banbanta a tsakanin mata da maza, misali, idan ya kama maza, zasu iya fuskantar ciwon kirji, yayin da idan ya kama mata, zasu iya fuskar Ciwon kirjin da karin wasu matsaloli da suka hada da numfashi sama-sama, da yawan zazzabi da safe da kuma matsananciyar kasala. Ga dai alamomin ciwon zuciya na Coronary artery disease dake damun maza d...

Alamomin cikin wata tara

Duk Labarai, Haihuwa, Laulayin ciki
A yayin da cikinki ya kai watanni 9, abinda ke cikinki na da cikakkiyar halittar Idanu kuma za'a iya cewa ya cika mutum. A wata 9, abinda ke cikinki ya kai tsawon 12 inches ko ace 30 cm Idanun sun yi kwari sosai zasu iya kallon komai. Gashin da ya lullube jikin jaririn kusan za'a iya cewa ya gama zubewa. Hakanan fatar jikin jaririn ta yi kwari. Yayin da cikin ki ya kai wata tara, zai ci gaba da yi miki nauyi. Alamomin daukar ciki, irin su nankarwa, Rashin lafiyar safe, Kasala, kasa rike fitsari, da sauransu zasu ci gaba har zuwa a haihu. Abinda ke cikinki zai iya yowa kasa, wanda hakan zai rage miki wahalar yin kashi da zafin kirji ko zuciya. Saidai cikin wasu matan bai yo kasa har sai nakuda ta tashi.
Cutar Amai da gudawa ta barke a Najeriya, mutane 65 sun kamu, 30 sun mu-tu

Cutar Amai da gudawa ta barke a Najeriya, mutane 65 sun kamu, 30 sun mu-tu

Tsaro
Daga watan Janairu na shekarar 2024 zuwa 14 ga watan Yuni Mutane 65 ne suka kamu da cutar amai da gudana inda guda 30 suka mutu. An samu cutarne a kananan hukumomi 96 da ke jihohi 30 a fadin Najeriya kamar yanda hukumar kula da cututtuka ta kasa, NCDC ta bayyanar. Hukumar ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ranar Alhamis dan ankarar da mutane kan lamarin inda tace a yi hankali saboda zuwan ruwan sama.
Hoto: Wannan matashin ya yi garkuwa da kansa ya karbi Naira Miliyan 5 daga gurin mahaifinsa

Hoto: Wannan matashin ya yi garkuwa da kansa ya karbi Naira Miliyan 5 daga gurin mahaifinsa

Tsaro
Wannan wani matashine dan kimanin shekaru 20 wanda ya yi garkuwa da kansa. https://www.youtube.com/watch?v=QMoREHNRpDM?si=Z_vLHKGDPEAc2llB Matashin dai ya jada baki da wanine inda aka kamashi aka daure aka kuma rika dukansa. An nemi mahaifinsa ya biya Naira Miliyan 50 wanda daga baya aka ce ya biya Miliyan 5 ta hanyar Bitcoin. Bayan biyan kudin, asirin matashin ya tonu:

Alamomin cikin wata takwas

Duk Labarai, Haihuwa, Laulayin ciki
A yayin da cikinki ya kai watanni 8, abinda ke cikinki ya kai tsawon 11 inches. A daidai lokacinne wani gashi me laushi dake lullube da abinda ke cikinki zai fara zubewa. Idan namiji ne, a wannan lokacinne marainansa zasu zazzago kasa. A wannan watanne zaki rika jin gajiya, sannan zaki rika nishi da kyar. Jijiyoyi zasu iya fitowa rado-rado musamman a kafarki. Zaki iya samun nankarwa. Zafin kirji ko zafin zuciya na iya ci gaba, hakanan zaki iya ci gaba da fama da wahala wajan yin kashi. Fitsari zai iya zubowa yayin da kika zo yin atishawa ko kuma kike dariya. Wadannan abubuwanne zaki yi fama dasu yayin da cikinki ya kai watanni 8.