Suma Sanatoci Mafi karancin Albashi ya kamata a biyasu>>Inji Father Mbaka
Babban malamin Kirista, Father Ejike Mbaka ya bayyana cewa, kamata yayi suma 'yan majalisar tarayya a rika biyansu mafi karancin Albashi.
Ya bayyana cewa ma'aikata dakw ainahin wahala wajan aiki amma sune ake biya kudade 'yan kadan inda yace sam hakan bai dace ba.
Yace a mayar da mafi karancin Albashin a rika biyan kowa dashi har 'yan majalisar kada a mayar da wasu bayi.
Yace saboda menene za'a rika biyan 'yan majalisar Alawus wanda ya wuce ka'ida?