‘Yan Bindiga sun kashe mutane 7 da sace 150 a Munya jihar Naija saidai an kashe ‘yan Bindigar guda 25
Shugaban karamar Hukumar Munya ta jihar Naija, Malan Aminu Najume ya koka kan ayyukan ‘yan Bindiga a karamar hukumar tasa inda ya nemi a kubutar da mutanensa daga hannun ‘yan Bindiga.
Ya bayyana hakane ga manema labarai inda yace ‘yan Bindigar sun shiga garin kuci inda suka kashe mutane 7 da kuma sace 150.
Ya bayyana cewa, cikin wadanda aka kashe akwai jami’an tsaro 4 da kuma ‘yan Bijilante da wasu mutanen garin.
Saidai ya jinjinawa jami’an tsaron dake garin inda yace aun kashe guda 25 daga cikin ‘yan Bindigar.
Yace yawanci ‘yan Bindigar na zuwa ne daga jihar Kaduna inda suke musu aika-aika daga bisani su koma Kadunar.
Yace sun shiga garin da mashina kusan 100 kuma sun rika bi gida-gida suna daukar wanda suke son yin garkuwa dasu da suka hada da mata.