Saturday, January 11
Shadow

Duk Labarai

Ko an yi sulhu ba zamu daina yaki da kkashe mutanen Gaza ba>>Inji Firaiministan Israel, Benjamin Netanyahu

Ko an yi sulhu ba zamu daina yaki da kkashe mutanen Gaza ba>>Inji Firaiministan Israel, Benjamin Netanyahu

Duk Labarai
Firaiministan Israel, Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa ko da an yi sulhu tsakaninsu da kungiyar Hamas wa'adin sulhun na karewa zasu ci gaba da yaki a Gaza. Yace suna fatan a yin sulhun amma ba zasu daina yaki ba har sai sun cimma muradinsu na yin yakin a Gaza. Masu shiga tsakani dai sun bayyana damuwa akan matsayin da Firaiministan Israel ya dauka. Israel na son cimma kawar da kungiyar Hamas a matsayin kungiya me rike da makamai ko kuma kungiyar siyasa, kwato duka wadanda aka yi garkuwa dasu da kuma hana Gaza zama barazana ga Israel nan gaba. Kungiyar Hamas dai ta ki amincewa ta saki mutanen da take gasrkuwa dasu su 100 inda itama ta gindaya sharudanta.
INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: Yayin Da Ahmed S. Nuhu Ke Cika Shekara 18 Da Rasuwa A Yau, Ita Kuma Mahaifiyasa Ta Rasu A Yau Din

INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: Yayin Da Ahmed S. Nuhu Ke Cika Shekara 18 Da Rasuwa A Yau, Ita Kuma Mahaifiyasa Ta Rasu A Yau Din

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} "A daidai ranar da abokinmu Marigayi Ahmed S Nuhu yake çıka shekaru 18 da komawa ga Mahaliccinmu, ita kuma mahaifiyarsa Allah Ya yı mata rasuwa. Inda za a yi jana’izarta a garin Jos kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Muna addu’ar Allah Ya jikan ta, Ya gafarta mata kurakuranta, Ya sa Aljanna Madaukakiya ce makomarta. Idan ta mu ta zo kuma Allah Ya sa mu çıka da kyau da İmanı" kamar yadda shugaban hukumar tace finafinai, Abba El-Mustapha ya wallafa.
Mu muka koya maka siyasa har ka zama abinda ka zama yanzu>>PDP ta mayarwa Kwankwaso martani kan sukar da ya mata

Mu muka koya maka siyasa har ka zama abinda ka zama yanzu>>PDP ta mayarwa Kwankwaso martani kan sukar da ya mata

Duk Labarai
Shugaban riko na Jam'iyyar PDP, Umar Damagum ya bayyana cewa, sune suka gogar da tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso har ya zama abinda ya zama yanzu. Damagun ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da BBChausa. Yace koda duka jam'iyyun hamayya zasu hade ba zasu yi nasarar kwace mulki daga hannun APC ba tare da PDP ba. Kwankwaso a baya ya soki Jam'iyyar PDP inda ya bayyana irin rashin kyautawar da suka masa data sa ya fice daga cikin Jam'iyyar. Saidai Damagun yace duk da kalubalen da Jam'iyyar ta PDP ke fuskanta amma har yanzu tana nan da kwarjininta.
Kalli Bidiyon Zainab, Diyar Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero na gararamba a titin Legas karfe dayan dare

Kalli Bidiyon Zainab, Diyar Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero na gararamba a titin Legas karfe dayan dare

Duk Labarai
Wannan Zainab ce wadda kusan duk masu bibiyar kafafen sada zumunta sun santa. Diyace a wajen marigayi, sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero wadda rayuwarta ke cikin damuwa da rashin tabbas. A sabon bidiyon da ta yi ta bayyana cewa gata karfe dayan dare a Birnin Legas tare da mahaifiyarta da kaninta wanda kuma akanta suka dogara. Tace mahaifinta ya barta ba ilimi ba wani abu da zata iya dogaro dashi, bata da aikin yi. Tace ta gaji bata san yadda zata yi ba, babu wanda ke taimakonta. A baya dai Gwamnatocin Ganduje dana Abba Gida-Gida sun taimaka mata. A wannan karin, Hadimin tsohon shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad yayi kiran da a sake taimakawa Zainab, musamman Gwamnatin jihar Kano. Kalli Bidiyon anan
Za’a kashe Naira Biliyan 4 dan ginawa shugaba Tinubu wajan saukar jirgin sama a Legas

Za’a kashe Naira Biliyan 4 dan ginawa shugaba Tinubu wajan saukar jirgin sama a Legas

Duk Labarai
Ma'aikatar ayyuka ta ware Naira Biliyan 4 dan kashesu wajan ginawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu filin da zai rika sauka da karamin jirginsa. Tuni ma'aikatar ta saka wannan aiki na gina filin saukar jirgin a cikin kasafin kudinta na shekarar 2025. Wasu dai sun soki hakan da cewa bata kudin 'yan kasa ne musamman ganin yanda 'yan Najeriya da dama ke cikin halin ji 'yasu inda ake ganin da an saka kudin a wani fanni da sun taimaka sosai.
Asibitin koyarwa na Jami’ar ABU zai fara yin aikin dashen Koda a shekarar 2025

Asibitin koyarwa na Jami’ar ABU zai fara yin aikin dashen Koda a shekarar 2025

Duk Labarai
Asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello Zaria dake jihar Kaduna zai fara aikin dashen koda ga marasa lafiya. Hakan zai kawowa mutane sauki matuka wajan yin dashen kodar. Daraktan kula da lafiya na jami'ar, Prof. Ahmed Umdagas ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Lahadi, yace tsakanin nan da watan Maris ne za'a fara aikin dashen kodar. Yace mafi yawan kayan aikin da ake bukata suna kasa kuma ma'aikatansu an horas dasu kan yanda zasu gudanar da aikin. Ya kuma bayyana cewa suna kokarin kawo kayan aikin kula da masu cutar daji watau Cancer.
Mun bar gidan kakan mu ba gyarane saboda bamu saci kudi ba, ba zamu iya kula da gidan ba>>Inji Jikan Tsohon Shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari

Mun bar gidan kakan mu ba gyarane saboda bamu saci kudi ba, ba zamu iya kula da gidan ba>>Inji Jikan Tsohon Shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari

Duk Labarai
Jika a wajan tsohon shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari, Bello Shagari ya bayyana cewa sun kasa kula da gidan kakansu, tsohon shugaban kasar ne saboda basu saci kudi ba kuma dalilin haka yasa ba zasu iya kula da gidan ba. Ya bayyana hakane a matsayin martani ga wani dake tambayarsa me yasa suka kasa kula da gidan kakan nasu. Alhaji Shehu Shagari na daya daga cikin tsaffin shuwagabannin da akewa kallon mutanen kirki saboda basu yi sata ba.