Saturday, December 13
Shadow

Duk Labarai

Da Duminsa: A karshe dai, Malaman Jinya(Nurse) sun janye yajin aikin da suke

Da Duminsa: A karshe dai, Malaman Jinya(Nurse) sun janye yajin aikin da suke

Duk Labarai
Rahotanni sun tabbatar da cewa kungiyar malaman jinya(Nurse) da Ungozoma ta Najeriya,(NANNM) sun janye yajin aikin gargadin da suke. Sanarwar janye yajin aikin na kunshene a cikin takardar da shugaban kungiyar, Haruna Mamman da babban sakatarenta, T.A Shettima suka sakawa hannu. Tun ranar Laraba ne dai kungiyar ta fara yajin aikin bayan karewar kwanaki 15 da ta baiwa gwamnati ta biya mata bukatunta. Yajin aikin ya zo karshene bayan ganawar da kungiyar ta yi a yau Asabar. A ranar Juma'ar data gabata, kungiyar ta yi zama na musamman da wakilan Gwamnati.
Dangote ya baiwa David Bird shugabancin matatar mansa

Dangote ya baiwa David Bird shugabancin matatar mansa

Duk Labarai
Matatar man Dangote ta nada David Bird mukamin CEO wanda zai jagoranci gudanarwar matatar. S&P Global ne suka ruwaito hakan inda suka ce David Bird zai fara aiki a Watan Yuli. Rahotanni sun ce David Bird Kwararren Injiniya ne wanda yayi aiki da kamfanin Shell na tsawon kusan shekaru 20. Saidai har yanzu Dangote zai ci gaba da zama a matsayin mamallakin matatar man.
An zargi Peter Obi da kulla yiwa Shugaba Tinubu juyin mulki, Ya mayar da martani

An zargi Peter Obi da kulla yiwa Shugaba Tinubu juyin mulki, Ya mayar da martani

Duk Labarai
Hadimin Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party, Peter Obi, me suna Valentine Obienyem ya musanta cewa Ogan nasa ya shirya yiwa shugaba Tinubu juyin Mulki. Ya zargi cewa, Wani me suna Arabambi ne ya kaiwa jami'an tsaro korafi akan Peter Obi da sauran wasu mutane irin su shugaban kungiyar Kwadago ta NLC, Joe Ajaero, da sanata Victor Umeh da 'yar majalisar wakilai, Nenadi Usman. Valentine yayi kiran a gudanar da bincike sannan a kama wanda yayi wannan yarfen dan a hukuntashi.
Gwamnatin tarayya zata baiwa ‘yan Najeriya Miliuan 8.8 tallafi dan rage musu radadin talauci, ji yanda za’a yi rabon

Gwamnatin tarayya zata baiwa ‘yan Najeriya Miliuan 8.8 tallafi dan rage musu radadin talauci, ji yanda za’a yi rabon

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta ta rabawa 'yan Najeriya Miliyan 8.8 tallafi dan rage musu radadin talauci. Gwamnatin tace zata raba wannan tallafi ne a mazabun dakw fadin kasarnan da suka kai 8,809. A ranar Alhamis ne gwamnatin ta sanar da wannan shiri sannan tace za'a gudanar dashi ne a karkashin ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki. Gwamnatin tarayyar tace, Kungiyar bayar da lamuni ta Duniya, IMF ta karfafa mata gwiwa wajan aiwatar da wannan aiki.
Kalli Bidiyon: Duk da cewar da ta yi ba zata yi ba, kalli yanda aka tursasawa Maryam Labarina yin wanke-wanke

Kalli Bidiyon: Duk da cewar da ta yi ba zata yi ba, kalli yanda aka tursasawa Maryam Labarina yin wanke-wanke

Duk Labarai
An samu wani yayi amfani da AI watau fasahar zamani na kwamfuta ko application yasa Maryam Labarina wadda tace ba zatawa mijinta wanke-wanke ba yin wanke wanken. Tun bayan data furta wadannan kalaman a wani Podcast data bayyana a ciki lamarin ya dauki hankula sosai ake ta cece-kuce a akai. Masu comment a kasan Bidiyon sun rika fadin an sa ta dai dole ta yi wanke-wanke. https://www.tiktok.com/@yusufdahiru81/video/7533706665451900165?_t=ZS-8yXYjwgPbF2&_r=1
Akwai alkawarin cewa Obasanjo Atiku zai baiwa mulki idan ya kammala amma yaci Amanarsa>>InJi Dele Momodu, ji yanda lamarin ya faru

Akwai alkawarin cewa Obasanjo Atiku zai baiwa mulki idan ya kammala amma yaci Amanarsa>>InJi Dele Momodu, ji yanda lamarin ya faru

Duk Labarai
Mawallafin jaridar Ovation Magazine, Dele Momodu ya bayyana cewa, akwai alkawari tsakanin Atiku Abubakar da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo kan cewa, Obasanjo zai yi mulkin wa'adi daya ne ya sauka ya baiwa Atikun. Saidai Obasanjo be cika wannan alkawari ba. Dele Momodu yace duk da wannan Atiku bai daina baiwa Obasanjo girmansa ba duk da cewa yana da goyon bayan gwamnoni a wancan lokacin. Dele Momodu yace daga karshema Obasanjo sawa yayi aka kwace abubuwan da kundin tsarin mulki suka tanada a baiwa Atiku. Yace amma Atiku sai ya mayar da hankali akan kasuwanci, kuma yayi ta samun ci gaba, yace da sauran 'yan siyasa sun kasance irin Atiku masu sana'a da Najeriya bata samu kanta a halin da take ciki yanzu ba.
‘Yan Najeriya basu taba shan wahalar da suke sha a Gwamnatin Tinubu ba>>Inji Sanata Dino Melaye

‘Yan Najeriya basu taba shan wahalar da suke sha a Gwamnatin Tinubu ba>>Inji Sanata Dino Melaye

Duk Labarai
Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa 'yan Najeriya basu taba shan irin wahalar da suke sha a gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels TV. Yace wasu har bola suke bi suna tsintar Abinci. Melaye yace mutum idan yana son ya gane irin wahalar da ake ciki, ya je kauye, mutane na ta mutuwa saboda tsananin rashin abinci. Da yake magana akan jam'iyyar PDP, Sanata Dino Melaye yace APC ta rika ta saye jam'iyyar PDP da hakan PDP ba jam'iyyar dogaro bace.