Friday, April 11
Shadow

Duk Labarai

An kulle kasuwanni da makarantu yayin da sojoji ke nema  wanda suka kashe sojoji 5 a garin Aba

An kulle kasuwanni da makarantu yayin da sojoji ke nema wanda suka kashe sojoji 5 a garin Aba

Tsaro
Garin Aba ya rikice inda sojoji suka mamayeshi bayan kisan abokan aikinsu 5. Wasu da ake kira da 'yan Bindigar da ba'a san ko su wanene ba amma ana kyautata zaton 'yan IPOB ne kawai da suke fakewa da wannan sunan suka yi kisan. Sun yi kisanne ranar Laraba bayan sun tursasa kowa ya je gida ya zauna dan tunawa da mutanen da suka mutu a yakin Biafra. Lamarin yasa hukumar sojojin Najeriya ta sha Alwashin sai ta rama wannan kisa da kakkausar murya. Rahoton jaridar Vanguard yace sojojin sun shiga kasuwanni suka tursasa mutane suka kulle shaguna da kuma a jiya, Juma'a yawanci yara basu je makaranta ba a garin. Hakanan an ga jirage masu saukar Angulu suna shawagi a sararin samaniyar wajan.
Tsananin zafi na ci gaba da kashe mutane a Indiya

Tsananin zafi na ci gaba da kashe mutane a Indiya

Duk Labarai
Rahotanni na cewa an samu mutuwar mutane da dama sakamakon tsananin zafi a Indiya. Hukumomin jihohin gabashin ƙasar, Odisha da Bihar sun ce mutane 15 ne suka rasu a ranar Alhamis, kuma suna ci gaba da bincike kan lamarin. An haramtawa ma'aikata zirga-zirga a tsakiyar rana. Ana hasashen cewa za a ci gaba da fuskantar tsananin zafi a gabashi yayin da ake hasashen za a samu sauƙin zafin a Arewa maso Yamma da kuma tsakiyar Indiya.
Ƙungiyoyin TUC da NLC za su tsunduma yajin aiki ranar Litinin

Ƙungiyoyin TUC da NLC za su tsunduma yajin aiki ranar Litinin

Siyasa
Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na TUC da NLC a Najeriya sun yanke shawarar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani sakamakon rashin cimma yarjejeniya tsakaninsu da gwamnatin tarayya. Gamayyar ƙungiyoyin sun sanar da hakan ne da yammacin ranar Juma'a bayan wani taro da suka yi inda suka tattaunawa yiwuwar tsunduma yajin aikin. A farkon makon nan ne dai manyan ƙungiyoyin ƙwadago guda biyu suka yi watsi da tayin naira 60 da gwamnatin tarayya ta yi masu a matsayin albashi mafi ƙanƙanta, biyo bayan zaman da suka yi da gwamnatin tarayya, inda a nan ne gwamnatin ta yi tayin. Da farko dai sai da gwamnatin Najeriyar ta fara kara naira dubu uku a kan tayin naira dubu 47 da ta yi a baya. Su ma ƙungiyoyin ƙwadagon sun rage dubu uku daga naira 497 da suke nema a matsayin albashi mafi ƙanƙanta....
‘Matsalar Najeriya sai a ce ka cancanta amma ba ka da kuɗi’

‘Matsalar Najeriya sai a ce ka cancanta amma ba ka da kuɗi’

Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Siyasa
Ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya zargi 'yan ƙasar a kan fifita siyasar kuɗi maimaikon zaɓar mutane masu aƙidar da za su iya kawo canji. Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce dimokraɗiyyar Najeriya ta samu koma-baya saboda wasu 'yan siyasa da kan sayi ƙuri'un mutane ta hanyar ba su atamfa ko taliya. A cewarsa, irin wannan tunani na ɗaya daga cikin abubuwan da suka jefa al'ummar ƙasar cikin halin matsin rayuwa da taɓarɓarewar tsaron da hukumomi suka gaza shawo kansu ya zuwa yanzu. Ya kuma ce rashin iya mulki ne ya haddasa taɓarɓarewar al'amura kamar tsaro da tattalin arziƙi a Najeriya. Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana haka a jerin hirarrakin da BBC ta yi da wasu ƙusoshin siyasar Nijeriya a wani ɓangare na cika shekara 25 da mulkin dimokraɗiyya karon...
Ga masu cewa basu ga dalilin dawo da tsohon taken Najeriya ba, ku sani dawo da taken Najeriyar na daya daga cikin muhimman aikin da nake son yi>>Tinubu

Ga masu cewa basu ga dalilin dawo da tsohon taken Najeriya ba, ku sani dawo da taken Najeriyar na daya daga cikin muhimman aikin da nake son yi>>Tinubu

Siyasa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, dawo da taken Najeriya na daya daga cikin muhimman abubuwan da yake son yi a mulkinsa. Ya bayyana hakane a yayin ganawa da kungiyar dattawan Najeriya, ACF. Tinubun dai ya sakawa dokar data dawo da tsohon taken Najeriya hannu wanda hakan ya jawo cece-kuce inda mutane ke cewa ba wannan ne matsalar kasar ba. Shugaba Tinubu ya kuma jawo hankali kan samun hadin kai a Najeriya.
Idan har yau, Kwanaki 3 bayan shugaban kasa yayi dokar sabon taken Najeriya baka iya rerashi ba, kai me laifine kana cin amanar kasa, kuma idan aka kamaka zaka dandana kudarka>>Hukumar ‘Yansanda

Idan har yau, Kwanaki 3 bayan shugaban kasa yayi dokar sabon taken Najeriya baka iya rerashi ba, kai me laifine kana cin amanar kasa, kuma idan aka kamaka zaka dandana kudarka>>Hukumar ‘Yansanda

Siyasa, Tsaro
Hukumar 'yansandan jihar Legas ta bakin tsohuwar kakakin hukumar, Dolapo Badmus ta bayyana cewa rashin iya taken Najeriya, kwakaki 3 bayan shugaban kasa ya saka shi a matsayin doka babban laifi ne. Ta bayyana hakane a shafinta na Instagram inda take bayar da misalin wani me makaranta data sa a kama saboda yana rera tsohon taken Najeriyar. Tace rashin iya taken Najeriyar cin amanar kasa ne. Ta baiwa mutane shawarar su samu lauyoyi su musu karin bayani. ‘’If, as at today, three days after the President of Federal Republic of Nigeria signed and assented the New National Anthem into law and you are not able to recite it in a whole, then you are a suspect I just passed through a private school and I could here them singing the old National Anthem! "Arise oh compatriots"! (We are...
Za’a kama shugaban wata makaranta saboda ya bar dalibansa na rera tsohon taken Najeriya

Za’a kama shugaban wata makaranta saboda ya bar dalibansa na rera tsohon taken Najeriya

Siyasa, Tsaro
Tsohuwar kakakin 'yansandan jihar Legas, Dolapo Badmus ta yi kiran a kama shugaban wata makaranta me zaman kanta da babban malamin makarantaar saboda rera tsohon taken Najeriya. Ta bayyana cewa, ta zo wucewa ta kusa da makarantar ne sai ta ji suna rera tsohon taken Najeriyar. Tace tuni ta yiwa 'yansanda magana kan a kamasu tare da gurfanar dasu a gaban kotu dan musu hukunci. Tace kwanaki 3 bayan da shugaban kasa ya sakawa dokar canja taken Najeriyar hannu, duk wanda aka samu bai iyashi ba, to me laifi ne. Tace kada wanda ya tambayeta laifin me suka yi, duk wanda ke da tambaya, ya samu lauya ya masa karin bayani. Tace duk wanda bai iya sabon taken Najeriya ba, to yana cin amanar kasane. ‘’If, as at today, three days after the President of Federal Republic of Nigeria sign...
Hoto:An kamashi Saboda sayar da ‘ya’yanshi har guda 6 a jihar Sokoto

Hoto:An kamashi Saboda sayar da ‘ya’yanshi har guda 6 a jihar Sokoto

Duk Labarai
'Yansanda a jihar sokoto sun kama wani mutum saboda siyar da 'ya'yansa 6. Mutumin ya sayar da jimullar kananan yara 28 ciki hadda 'ya'yan cikinsa 6. Kwamishinan 'yansandan jihar, CP Ali Hayatu Kaigama ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kubutar da 21 daga cikin yaran. Mutumin me suna, Bala Abubakar yana baiwa wasu mata, Kulu Dogon yaro da Elizabeth Ojah yaranne inda su kuma suke bashi Naira dubu dari da hamsin ko kuma Naira dubu dari biyu da hamsin. Ana cewa wai za'a kaisu Abujane wajan wani mutum da zai rika kula dasu.