Friday, February 27
Shadow

Duk Labarai

Jirgin saman ‘yan Kwallon Najeriya, Super Eagles yayi saukar gaggawa bayan da gilashin jirgin ya fashe

Jirgin saman ‘yan Kwallon Najeriya, Super Eagles yayi saukar gaggawa bayan da gilashin jirgin ya fashe

Duk Labarai
Jirgin saman da 'yan kwallon Najeriya, Super Eagles ke ciki yayi saukar gaggawa bayan da gilashin gaba na jirgin ya tsage. Jirgin ya saukane a kasar Angola. 'Yan wasan na dawowa ne daga wasan da suka buga da Lesotho wanda suka yi nasara 2-1. Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, (NFF) ta tabbatar da hakan inda tace direban jirgin yayi kokari sosai wajan saukar da jirgin bayan faruwar lamarin.
Kalli Bidiyon: Ku daina min kallon Mutuniyar Banza, ni ba Qaruwa bace, kuma bana shaye-shaye, neman sunane kawai na fito yi>>Inji Matashiyarnan ‘yar Legas da tace zata Aikata Alfasha da maza 100 dan ta shiga kundin Tarihin Duniya

Matashiyar nan 'yar legas wadda ta fito tace zata aikata Alfasha da maza 100 dan shiga kundin tarihin Duniya ta bayyana cewa ita ka Qaruwa bace. Tace kuma bata shaye-shaye, wiywiy kawai take dan zuqa daga lokaci zuwa lokaci. Matashiyar da aka fi sani da sunan Mandy Kiss tuni Gwamnatin jihar Legas ta bata jakadancin yaki da miyagun kwayoyi. https://twitter.com/whatsappblog9ja/status/1977228790133629308?t=RIUqk16_u4Oganp0Zy4ybQ&s=19
Ya dauke ta ya kai ta gidansa suka kwana da Alkawarin Zai bata Naira dubu dari da hamsin, saidai ya mata Alert din karya(Fake) alert, tana ta kuka

Ya dauke ta ya kai ta gidansa suka kwana da Alkawarin Zai bata Naira dubu dari da hamsin, saidai ya mata Alert din karya(Fake) alert, tana ta kuka

Duk Labarai
Wannan wata me zama kanta ne da rahotanni suka ce wani ya dauketa ya kaita gida suka kwana da niyyar cewa, zai bata Naira 150k amma sai ya mata alert din karya. Ya fice daga inda suka kwana, daga baya data gani ta yi ta kuka. Tuni akaita watsa labarinta a kafafen sada zumunta ana ta muhawara.
Dan Kiripto ya aika kansa Lahira bayan Tafka mumunar Asara biyo bayan lalacewar kasuwar

Dan Kiripto ya aika kansa Lahira bayan Tafka mumunar Asara biyo bayan lalacewar kasuwar

Duk Labarai
Rahotanni sun ce wani dan kasuwar Kiripto me suna Konstantin Ganich ya khashe kansa bayan da ya tafka mummunar Asara. Kasuwar Kiripto ta tafka asarar da ba'a taba ganin irin ta ba data kai ta dala Biliyan 19. Rahotanni sunce a gano gawar mutuminne a cikin motarsa ranar Juma'a. Kasar Ukraine na daya daga cikin kasashen da suka rungumi harkar Kiripto musamman saboda matsin tattalin arzikin da kasar ke fama dashi.
Saidai idan mu duka za’a kama amma abinda Malam Lawal Triumph ya fada duk Ahlussunnah akan shi muke>>Inji Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau

Saidai idan mu duka za’a kama amma abinda Malam Lawal Triumph ya fada duk Ahlussunnah akan shi muke>>Inji Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau

Duk Labarai
Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa, duka 'yan Izala suna kan irin maganar da Malam Lawal Triumph ya fada. Ya jawo hankalin Gwamnatin Kano da cewa, Kada ta siyasantar da harkar Addini. Yace idan kuwa an ce za'a rika kama masu irin wannan ra'ayi to saidai idan kowa da kowa mutanen Ahlussunah za'a kama. https://www.tiktok.com/@dadee308/video/7559618850321337607?_t=ZS-90SUktqxYtl&_r=1
Kasuwar Kiripto ta yi mummunar asarar da bata taba yi ba a Tarihi, An yi Asarar da Biliyan $19.6

Kasuwar Kiripto ta yi mummunar asarar da bata taba yi ba a Tarihi, An yi Asarar da Biliyan $19.6

Duk Labarai
Rahotanni sun ce kasuwar Kirypto ta tafka gagarumar Asarar da ba'a taba ganin irinta ba a Tarihi. Rahotanni sun ce a cikin awanni 24, kasuwar ta tafka asarar dalar Amurka Biliyan $19.6. Hakan na zuwa ne bayan da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sanar da shirin kakabawa kasar China sabon haraji na kaso 100. Hakanan labarin cewa an yiwa manhajar Binance kutse ya kawo tarnaki a kasuwar ta Crypto inda daga baya mutane suka kasa amfani da Binance din da Coinbase. Saidai an ga wani sun kintaci wannan yanayi sun ci ribar makudan kudade wanda hakan yasa ake zargin cewa ko dai da gangan aka yi hakan ko kuma sun samu bayanan sirri game da karyewar kasuwar.