Hotuna: An kama ma’aikaciyar Gidan yari na lalata da me laifi
Hukukomin Gidan yari a kasar Ingila sun kama wata ma'aikaciya da bidiyonta ya bayyana tana lalata da me laifi.
Jaridar TheSun ta ruwaito cewa, an kama ma'aikaciyar me shekaru 19 ne bayan da bidiyon lalatar da ta yi da me laifi a gidan yarin ya watsu sosai.
An rika aikawa mutanen dake aiki a gida yarin bidiyon dama sauran wanda ke waje har ta kai ga ya kai ga hukumomin gidan yarin.
A kasar ta Ingila dai ana yawan samun irin wannan matsala inda mata ma'aikatan gidan yari kan yi lalata da mazan da ake tsare dasu.
A baya an kori mata kusan 29 saboda irin wannan halayya.