
Babu wata data fita daga Musulunci zuwa Kirista>>Gwamnatin Jihar Zamfara
Gwamnatin Zamfara ta karyata labarin dake cewa wata me suna Zainab ta fita daga Musulunci zuwa Kirista a jihar.
Me magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Yace sun yi bincike ta hanyar kiran Alkalin Alkalai na jihar da kiran dukkan masu ruwa da tsaki na jihar kan bangaren shari'a duk sun tabbatar musu babu wata me suna Zainab data canja addini.
Dan haka ya bayyana cewa labarin karyane wadda wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta wallafa dan neman mabiya.