Saturday, December 13
Shadow

Duk Labarai

Ba zamu yadda kasar Iran ta mallaki makamin kare dangi ba>>Inji Kasashen G7

Ba zamu yadda kasar Iran ta mallaki makamin kare dangi ba>>Inji Kasashen G7

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Canada inda aka yi taron kasashe 7 mafiya karfin tattalin Arziki wadanda ake kira da G7 sun bayyana cewa, ba zasu amince kasar Iran ta mallaki makamin kare dangi ba. Kasashen sun ce suna son a samu zaman lafiya a gabas ta tsakiya kuma sun amince kasar Israyla na da damar kare kanta. Sun bayyana cewa kasar Iran itace ummul aba isin rashin zaman lafiyar da ake fama dashi a yankin na gabas ta tsakiya. Dan haka suna jaddada matsayarsu ta cewa ba zasu amince kasar Iran ta mallaki makamin kare dangi ba. Kasashen G7 da shuwagabannin su sune kamar haka: Donald J Trump (The USA)Keir Starmer (The UK)Friedrich Merz (German Chancellor)Giorgia Meloni (Italy PM)Emmanuel Macron (France)Shigeru Ishiba (Japan PM) Wasu kasashen Duniya da aka gayyata zuwa wannan taro su...
Kotu ta ki amincewa da bukatar Gwamnatin tarayya ta kama Sanata Natasha Akpoti

Kotu ta ki amincewa da bukatar Gwamnatin tarayya ta kama Sanata Natasha Akpoti

Duk Labarai
Kotun tarayya dake Abuja ta ki amincewa da bukatar Gwamnatin tarayya ta kama dakatacciyar sanata Natasha Akpoti. Gwamnatin na son a kama Sanata Natasha Akpoti ne saboda kun ta ki bayyana a kotu wajan shari'ar da ake yi ta zarginta da bata suna. Mai shari'a, Justice Muhammed Umar ne ya yanke wannan hukunci bayan da lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe, ya nemi a kama Sanata Natasha Akpoti saboda kin halartar kotun duk da cewa an baiwa Lauyanta Sammace. Saidai Mai Shari'a Muhammad Umar ya bayyana cewa, tunda ba Sanata Natasha Akpoti da kanta aka baiwa samacen ba ba za'a iya cewa lallai ta samu sammacen ba. Dan haka ya daga ci gaba da sauraren shari'ar zuwa ranar 30 ga watan Yuni.
Dukan da aka so a Lakadamin a jihar a jihar Gombe abin kunyane kuma na yi Allah wadai dashi, irin wanan abu na iya jawo yàkìn basasa>>Shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje

Dukan da aka so a Lakadamin a jihar a jihar Gombe abin kunyane kuma na yi Allah wadai dashi, irin wanan abu na iya jawo yàkìn basasa>>Shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Shiga tasharmu ta WhatsApp dan samun labarai: https://whatsapp.com/channel/0029VbA9rBN1SWt61nQZUj1g Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi Allah wadai da yunkurin dukan sa da aka so yi a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Gombe. Ya bayyana cewa abin rashin kishin kasa ne kuma abune na rashin da'a. Sannan yace hakan zai iya dagula lamarin siyasar kasarnan. Ganduje ya bayyana hakane ta bakin hadiminsa na musamman dake taimaka masa kan w...
An daure magidanci daurin rai da rai bayan da yawa diyar makwaucinsa me shekaru 8 fyàdè

An daure magidanci daurin rai da rai bayan da yawa diyar makwaucinsa me shekaru 8 fyàdè

Duk Labarai
Wani me aikin gini me suna Azeez Shoderu wanda aka fi sani da Chisco ya gamu da daurin rai da rai bayan da aka kamashi yama yiwa diyar makwaucinsa me shekaru 8 fyade a bandaki. Kotu ta musamman dake jihar Legas wadda aka samar domin hukunta irin wadannan laifuka ce ta yanke masa wannan hukunci. Mai shari'a, Rahman Oshodi ce ta yanke masa wannan hukunci bayan samunsa da laifi bisa dogaro da shaidu da hujjoji. Wanda ake zargin dai ya ki amsa laifinsa inda yace kawai yace yarinyar ta kawo masa ruwane a bandakinsa. Saidai Yarinyar tace ta shiga bandaki dan yin fitsarine sai ya kamata ya rufe mata baki ya mata fyade. Kotu tace ta gamsu da maganar yarinyar musamman bayan da binciken likitoci ya tabbatar da an mata fyade.
Da ya dauki bìndìgàr mahaifinsa dansanda ya harbe mahaifin ya mùtù

Da ya dauki bìndìgàr mahaifinsa dansanda ya harbe mahaifin ya mùtù

Duk Labarai
Wani abin takaici ya faru a garin Awka, na jihar Anambra inda yaro dan shekaru 10 ya dauki Bindigar mahaifinsa Dansanda, AK47 ya dirka masa harsashi ya mutu. Mahaifin na da mukamin Inspector ne kuma sunansa Okolie Amechi. Lamarin ya faru ne a gidan marigayin inda kuma harsashi ya samu dayan dan nasa me suna Emmanuel a hannu. Rahoton yace yaron na wasa da Bindigar ne inda bisa tsautsai ya harbata, ta samu mahaifin nasa a baya sannan harsashin ya wuce ya samu dayan dansa a hannu. Kakakin 'yansandan jihar, SP Tochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kai gawar mahaifin asibiti inda shi kuma dayan da nasa na can ana bashi kulawa ta musamman. Ya bayyana cewa, hukumar 'yansandan jihar ta yi alhinin wannan abin da ya faru.
ABIN TAUSAYI: Tun Yaron Yana Dan Watanni Hudu Da Haihuwa Suka Rabu Da Mahaifiyarsa, Hakan Ya Sa Bayan Girma Yake Fita Da Shi Aikin Achaba Saboda Babu Mai Kula Masa Da Shi

ABIN TAUSAYI: Tun Yaron Yana Dan Watanni Hudu Da Haihuwa Suka Rabu Da Mahaifiyarsa, Hakan Ya Sa Bayan Girma Yake Fita Da Shi Aikin Achaba Saboda Babu Mai Kula Masa Da Shi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} ABIN TAUSAYI: Tun Yaron Yana Dan Watanni Hudu Da Haihuwa Suka Rabu Da Mahaifiyarsa, Hakan Ya Sa Bayan Girma Yake Fita Da Shi Aikin Achaba Saboda Babu Mai Kula Masa Da Shi