Ganyen mangoro da amfaninsa
Ganyen mangoro na da amfani sosai a jikin dam adam.
A wannan rubutu, zamu duba amfanin ganyen Mangoro ga lafiyar dan Adam.
A dunkule, Ganyen Mangoro na maganin ciwon sugar, yana hana fata da jiki saurik tsufa, yana maganin Kumburin jiki, ana kuma amfani dashi wajan magance kuna da aka samu dalilin wuta, da kuma idan abinci baya sarrafuwa a jikin da adam.
Ganyen Mangoro na kuma taimakawa tsawon gashi kuma ana zubashi a ruwan wanka ko a hada shayi dashi saboda yana kara nutsuwa da kawar da damuwa.
Ganyen Mangoro na maganin ciwon gabobi na tsufa.
Ganyen Mangoro na maganin ciwon Ulcer da Gudawa da kukan ciki da sauransu.
Ganyen Mangoro na maganin cutar Asama.
Ganyen Mangoro na taimakawa wajan hana furfura da wuri da kuma kara tsawon gashi, idan mutum ya kone da wuta, gany...






