Rahotanni sunce sabon shugaban sojijin Ruwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nada watau Rear Admiral Idi Abbas, dan Asalin Jihar Filato ne domin a can aka haifeshi.
A lokacin da ya so shiga makarantar Horas da sojoji ta NDA dake Kaduna, ya je karamar hukumar sa inda ya nemi a bashi takardar shaidar zamansa dan karamar hukumar.
Amma sai aka ki bashi saboda Addininsa da kuma kabilarsa ta Hausa.
Sai ya tafi garin mahaifinsa, watau Kano kuma a can aka bashi takardar ya kai aka daukeshi aikin sojan.
Yau gashi ya zama shugaban sojojin Ruwa na Najeriya.
Zakaran da Allah ya nuna da chara....
Tauraron Tiktok, Hassan Make-Up ya bayyana a Bidiyo yana kuka saboda kama kawarsa Khadija MaiNumfashi.
An ji hassan na cewa yanzu a Ina Khadija tasan wasu 'yan daba?
https://www.tiktok.com/@officielhassanmakeup227/video/7565558701084380428?_t=ZS-90sQtSa6Op7&_r=1
A jiya ne dai 'yansanda suka kama Khadija MaiNumfashi suka wuce da ita zuwa Legas inda ake zarginta da batawa wani me suna Kabiru Lagos suna.
Daga cikin karin zarge-zargen da ake mata hadda cewa ta nemi halakashi ta hanyar daukar 'yan daba su farmaki rayuwarsa.
Tauraruwar Tiktok Abasiya 'YarGuda itama ta fito ta tabbatar da maganar cewa babu aure tsakaninta da Maiwushirya.
Ta bayyana hakane a wani Bidiyo inda take cewa Maiwushirya taimakonta yake.
Tace Ko da ta amsa a Kotu cewa zata aureshi ba da gaske take ba.
https://www.tiktok.com/@pharooq_/video/7565550522065767701?_t=ZS-90sPvJMyw1A&_r=1
Bayan hukuncin kotu da kuma tsayawar shirin da suke yi ita da Idris Maiwushirya, 'yan uwan Habasiyya 'YarGuda sun je Kano daga jihar Zamfara dan mayar da ita Gida.
A Bidiyon an ga daya daga cikin 'yan uwan nata na bayyana cewa, Bakin ciki ake musu saboda Maiwushirya yana taimakon rayuwarta ne da abubuwan da ba'a rasa ba.
Ta bayyana cewa matsalar 'yan Bindiga ta damesu a garinsu.
Saurarin jawabinta a Bidiyon kasa:
https://www.tiktok.com/@pharooq_/video/7565543245309152533?_t=ZS-90sOSmk9WC1&_r=1
Idris Maiwushirya ya bayyana bacin ransa kan abinda yace Abba EL-Mustapha ya masa inda yace ya shirya abinshi amma saboda bakin ciki aka sa yayi sarar Naira Miliyan 3.
Maiwushirya yace Abba El-Mustapha bai isa yasa a masa auren dole be sannan kuma shi da ya kama Chairlady a ni sai ka goyani wa yace sai ya aureta?
Ya kuma bayyana magungunan da ya saya saboda rashin lafiyar da ya kwanta duk saboda wannan matsalar.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya watsu sosai inda aka ganshi a kwance.
Ya kara da cewa da yana so ya auri 'YarGuda ai da ba sai an tursasa shi ba.
https://www.tiktok.com/@pharooq_/video/7565543951642496277?_t=ZS-90sKFJ5TOmv&_r=1
Dan majalisar Wakilai, Hon. Abdussamad Dasuki me wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal daga jihar Sokoto ya bayyana cewa ba zai tsaya takara a shekarar 2027 ba.
Yace ya barwa matasa 'yan kasa da shekaru 40 su tsaya takarar dan kawo sauyi da ci gaba a mazabar tashi.
Yace yayi hakanne ba dan ya gaji ko gazawa ba inda yace har yanzu shi matashi ne amma ya haura shekaru 40.
Yayi godiya ga mutanen mazabatarsa da iyayen gidansa a siyasa da suka bashi dama a shekaru 14 da yayi yana siyasar.
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta kama mutane 25 dake shirin kulla auren Namiji da Namiji.
An kamasu ne a Fatima Event Center dake Hotoro ranar Lahadi.
Mataimakin Kwamanda na Hisbah, Mujahedeen Aminudeen ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Yace daga cikin wadanda aka kama akwai maza 18, mata 7.
Yace sun samu bayanan sirri ne kan daura auren 'yan Luwadin.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Yahya ta saki sabbin zafafan Hotuna saidai a yayin da wasu ke yabawa, wasu tambayarta suka rika yi ina rigar mamanta.
Wasu kuwa sun rika mata Addu'ar shiriya.
Wasu na ganin wannan shigar bata dace da diyar Hausawa ba.
Tauraron mawakin Hausa, Ali Jita ya bayyana cewa idan ya je yayi waka a wajan taro ko a wajan Biki akan Bashi Naira Miliyan 10.
Jita ya bayyana hakane a wata Hirar Tiktok Live da suka yi shida Soja Boy.
A cikin hirar dai, Jita yace Shi bai dauki waka a matsayin Haramun ba amma duk randa ya gano cewa waka Haramun ce zai daina yi.