Saturday, May 16
Shadow

Duk Labarai

Kai malam Shekaruna 46 ba 35 ba, kuma kai na dan Adawa ne na gaskiya ba, APC ce ta turoka ka mata Munafurci>>Nafiu Bala ya gayawa Kwankwaso

Kai malam Shekaruna 46 ba 35 ba, kuma kai na dan Adawa ne na gaskiya ba, APC ce ta turoka ka mata Munafurci>>Nafiu Bala ya gayawa Kwankwaso

Duk Labarai
Nafiu Bala Gombe wanda ya kawo tarnaki a jam'iyyar ADC ya mayarwa da Kwankwaso zazzafan Martani inda yace Kwankwason ba dan Adawa bane na gaskiya. Nafiu ya bayyana cewa, Kwankwaso APC ce ta turoshi ya mata munafurci a jam'iyyar ADC. Sannan yace Shi shekarun sa 46 ba 35 ba kamar yanda Kwankwason yake fada. Sannan yace ya kamata Kwankwason yayi bincike da kyau kamin yayi magana irin waccan. Sannan yace ko da kuwa shi yarone bai kamata Kwankwason ya rainashi ba. Ya kara da cewa, Su Kwankwaso sun tsufa, kamata yayi su koma gefe su bar matasa su mulki Najeriya, yace kamata yayi su zama masu bayar da shawara. Yace Kwankwason da sauran shuwagabannin da yawa suma a lokacinsu matasa suka fara shiga harkar siyasa. Yace a 2023 fa Dattawan Arewa sun je suka samu Kwankwaso akan ya ja...
A karshe dai: Ainahin dalilin da yasa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma jam’iyyar APC ya bayyana

A karshe dai: Ainahin dalilin da yasa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma jam’iyyar APC ya bayyana

Duk Labarai
Rahotanni nata yawo a kafafen sada zumunta inda ake bayyana ainahin dalilin da yasa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC. Rahoton yace akwai rade-radin dake yawo cewa, Kwankwaso na shirin canja Abba a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar NNPP. Dalili kenan da yasa Abban ya yi gaggawa ya koma jam'iyyar APC dan samun Tikitin takara. https://twitter.com/i/status/2041481567730622823
Kalli Bidiyon: Yanda sabon wajan tsayuwar Motoci na zamani da aka kashe Miliyoyin Naira wajan ginawa a Abuja ya lalace bayan ruwan sama

Kalli Bidiyon: Yanda sabon wajan tsayuwar Motoci na zamani da aka kashe Miliyoyin Naira wajan ginawa a Abuja ya lalace bayan ruwan sama

Duk Labarai
Wajan tsayuwar motocin haya na Kugbo dake Abuja da aka kashe Miliyoyin Naira aka gina ya lalace. Lamarin ya jawo cece-kuce inda da yawa ke cewa dama can ba da kayan aiki masu inganci aka yi aikin ba. https://twitter.com/i/status/2041542821111320647 https://twitter.com/i/status/2041541799856976308 https://twitter.com/i/status/2041539082598187009
Da Duminsa: Yayin da ake fama da Nafiu, Wani sabin tsagi ya bulla a jam’iyyar ADC inda suka ce suma sune shuwagabannin jam’iyyar

Da Duminsa: Yayin da ake fama da Nafiu, Wani sabin tsagi ya bulla a jam’iyyar ADC inda suka ce suma sune shuwagabannin jam’iyyar

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa yayin da ake fama da Nafiu Bala Gombe, wani tsagi na jam'iyyar ADC ya bayyana inda suke ikirarin cewa, sune shuwagabannin jam'iyyar na gaskiya. Tsagin wanda wani me suna Don Norman Obinna kejagoranta, sun bayyana hakane a ganawa da manema labarai da suka yi a Abuja ranar Talata. Sun ce tsohon shugaban jam'iyyar, Ralph Nwosu da ya mikawa su David Mark ragamar jam'iyyar, tun shekarar 2022 wa'adin mulkinsa ya kare, kuma dama akwai shari'a da ake yi dashi a kotu bama guda daya ba.
Da Duminsa: Kwankwaso ya fusata da abinda Nafiu Bala Gombe yakewa ADC ya bayyana matakin da zasu dauka akan Nafiu

Da Duminsa: Kwankwaso ya fusata da abinda Nafiu Bala Gombe yakewa ADC ya bayyana matakin da zasu dauka akan Nafiu

Duk Labarai
A yayin da Nafiu Bala Gombe yake baiwa su Atiku da Kwankwaso da Peter Obi ciwon kai a jam'iyyar APC, Kwankwaso yayi martani Kwankwaso yace yasa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana yin dukkan mai yiyuwa wajan ganin ya muzguna musu ya hanasu rawar gaban hantsi amma hakan ba zai sanyaya musu gwiwa ba. Kwankwaso yace hakan karfafa su zai yi kuma ba zasu bar jam'iyyar ADC ba
Rahotanni sun ce Hamisu Breaker ya auri Hafsat Idris

Rahotanni sun ce Hamisu Breaker ya auri Hafsat Idris

Duk Labarai
Bayan Shafe Tsawon Lokaci Suna Soyayya Daga Ƙarshe Dai Ana Raɗe-raɗin Mawaƙi Hamisu Breaker Ya Auri Jaruma Hafsat Idris Shahararren mawaƙin nan na masana’antar Kannywood, Hamisu Breaker ya auri jaruma Hafsat Idris (Ɓarauniya) bayan shafe tsawon lokaci suna soyayya a sirrance. Wasu rahotanni su bayyana cewa an ɗaura auren ne a makon da ya gabata. Idan ta tabbata, za a iya cewa ma’auratan sun shiga layin jaruman Kannywood da ke yin aure cikin sirri a baya-bayan nan. Wane fata zaku yi musu?
Tonon Silili: Tinubu ne ya dauki nauyin me son kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho dan ya kawowa Gwamnatin Buhari tangarda>>Inji Sowore

Tonon Silili: Tinubu ne ya dauki nauyin me son kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho dan ya kawowa Gwamnatin Buhari tangarda>>Inji Sowore

Duk Labarai
Mawallafin jaridar Sahara Reporters kuma me ikirarin fafutukar kare hakkin bil'adama, Omoyele Sowore ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya dauki nauyin me son kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa watau Sunday Igboho dan ya kawo matsala a gwamnatin Buhari. A wancan lokacin dai, lamari yayi kamari har sai da ta kai ga Sunday Igboho ya tsere daga Najeriya dan gujewa kamun hukumomi. Saidai a yanzu ya dawi gida Najeriya har ma ana damawa dashi a Gwamnatin Tinubu. Sowore ya bayyana hakane a wani shirin Podcast me suna Times a yayin da yake sharhi akan siyasar yankin yarbawa na Kudu maso yamma. Yace a kokarin Tinubu na samun mulki shine ya fitar da kudi aka kafa kungiyar ta son ballewa daga Najeriya a kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa. Yace kuma Tinubu yayi hakane saboda a wa...