Tuesday, January 14
Shadow

Duk Labarai

Shugaba Tinubu ya dawo Abuja

Shugaba Tinubu ya dawo Abuja

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja daga kasar Saudiyya inda ya je wajan taron kasashen Musulmai. Jirgin na shugaba Tinubu ya sauka ne da misalin karfe 8 na darennan a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International airport. Manyan jami'an gwamnati ne suka mai maraba bayan saukarsa.
Kungiyoyin fafutuka 51 sun nemi EFCC ta kama shugaban jam’iyyar APC Ganduje kan zargin Rashawa da Cin Hanci, an samu Shaidu 143 zasu bayar da shaida akan cewa ya aikata laifin

Kungiyoyin fafutuka 51 sun nemi EFCC ta kama shugaban jam’iyyar APC Ganduje kan zargin Rashawa da Cin Hanci, an samu Shaidu 143 zasu bayar da shaida akan cewa ya aikata laifin

Duk Labarai
Kungiyoyin fafutuka 51 dake ikirarin yaki da rashawa da cin hanci sun nemi hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta kama shugaban jam'iyyar APC, Dr. Umar Abdullahi Ganduje kan zargin Rashawa da cin Hanci. Kungiyoyin sun rubuta takardar neman a kama Gandujene ranar November 4, 2024 inda ita kuma hukumar EFCC ta karbi takardar ranar November 7, 2024. A lokacin da yake rike da mukamin gwamnan Kano,an zargi Dr. Umar Abdullahi Ganduje da cin hanci da rashawa ta fannoni daban-daban. Akwaidai shaidu 143 wadanda suke a shirye su bayar da shaida akan zargin cin hanci da rashawa na Ganduje wadanda suka hada da ma'aikatan kananan hukumomi da 'yan canji da tsaffin ma'aikatan banki. Shuwagabannin kungiyoyin fafutukar da suka kai wadannan bukatu sun hada da Dr. Johnson Nebechi, Comrade...
Kalli Bidiyo Yanda wannan matar ke aikin da ake biyanta Naira Dubu 40 duk bayan awa daya

Kalli Bidiyo Yanda wannan matar ke aikin da ake biyanta Naira Dubu 40 duk bayan awa daya

Duk Labarai
Wannan wata mata ce da ta ke a kasar Amurka inda take aiki ana biyanta Naira Dubu 40 duk awa daya. https://www.youtube.com/watch?v=9HFjRK5j9mo Tace tana aiki ne a babban shagon sayayya na Amazon inda take aikin dare. Da yawa dai sun bayyana sha'awar aikin nata. Saidai wasu na ganin tsadar rayuwa da ake fama dashi a Amurka zai iya lakume kudaden da take samu.
Mutane 10 sun mùtù da dama sun jikkata a mummunan hadarin mota da ya faru a jihar Jigawa

Mutane 10 sun mùtù da dama sun jikkata a mummunan hadarin mota da ya faru a jihar Jigawa

Duk Labarai
Mutane 10 sun mutu da dama sun jikkata a wani mummunan hadarin mota da ya faru a jihar Jigawa. Lamarin ya farune a karamar hukumar Taura dake jihar. Wani Shaidar gani da ido ya gayawa manema labarai cewa hadarin ya farune a kauyen 'Yanfari dake kan hanyar Kano zuwa Hadejia a karamar hukumar Taura. Yace motar bas ce ta daki wata Tirela dake a gefen titi inda motar ta wuntsula mutane 10 suka mutu nan take. Kakakin 'yansandan jihar, DSP Lawan Shiisu ya tabbatar da faruwar lamarin. Yace lamarin ya farune ranar November 12, 2024 kuma suna samun labari jami'an su suka garzaya wajan inda yace sun tarar direban motar da mutane 9 sun mutu. Yace akwai mutum da ya da bai mutu ba a yanzu ana duba lafiyarsa. Yace suna kan bincike dan gano ko akwai laifin wani a hadarin da ya faru.
NNPC Ta Sanar Da Kammala Biyan Bashin Dala Bilyan 2.4, Tare Da Albishirin Samar Da Manyan Tashoshin CNG 12 A Shekara Mai Zuwa

NNPC Ta Sanar Da Kammala Biyan Bashin Dala Bilyan 2.4, Tare Da Albishirin Samar Da Manyan Tashoshin CNG 12 A Shekara Mai Zuwa

Duk Labarai
Shugaban rukunin Kamfanin Mai Na NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana nasarar kammala biyan bashin da ake bin kamfanin da ga kamfanonin mai na kasashen ƙetare inda ya ce a yanzu, babu mai bin kamfanin bashin sisin kwabo.Kyari ya ce, wannan babban nasara ce da aka cimma biyo bayan cire tallafin mai a Gwamnatin Shugaba Tinubu. “Mun rika karkatar da kudadenmu da dukiyoyinmu don tabbatar da komai na tafiya daidai a bangaren mai na PMS mai wuyar sha'ani, abinda ya rika janye hankalin NNPC daga biyan basussuka" Mele ya ci gaba da cewa“ Sai dai yanzu wannan matsala ta kau, za ku ga cewa ba mu da wani bashin da ake bin mu, kuma don mu tabbatar da dorewar hakan, ya zama wajibi a kawar da duk wata matsala don masana'antar ta iya samar da makamashi mai dorewa da arha da ake buƙata a ƙasar nan." Sh...
An samu fargabar dasa Bàm a Jos, Jihar Filato

An samu fargabar dasa Bàm a Jos, Jihar Filato

Duk Labarai
Hukumar 'yansanda a Birnin Jos na jihar Filato ta tabbatar da fargabar dasa bam a birnin. Saidai ta musanta wannan jita-jita. Kakakin 'yansandan jihar, DSP Alfred Alabo ya tabbatarwa manema labarai cewa maganar dasa bam din ba gaskiya bane. Yace ranar Talata ne aka fara yada jitajitar kuma jami'an su da suka kware wajan kula da bam sun isa wajan inda suka tabbatar da babu bam a inda ake rade-radin.