Wednesday, January 15
Shadow

Duk Labarai

Na yi mamakin sauke ni daga muƙamin minista – T Gwarzo

Na yi mamakin sauke ni daga muƙamin minista – T Gwarzo

Duk Labarai
Tsohon ƙaramin ministan gidaje na Najeriya, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce ya yi mamakin sauke shi da a aka yi daga muƙaminsa. Yayin wata hira da BBC kwanaki bayan sauke shi , T Gwarzo ya ce babu wani laifi da ya yi, wanda ya janyo aka sauke shi daga muƙamin nasa, sabod a cewarsa ya yi iya baƙin ƙoƙarinsa a muƙamin da aka ba shi. ''Batun ya zo min da mamaki, domin ba na tunanin wani abu mai kama da wannan zai faru da ni'', in ji shi. Ya ƙara da cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi la'akari da tarayyarsu tun ta da can wajen naɗa shi muƙamin. Ya ce fiye da shekara 14 suna tare da Tinubu tun a jam'iyyar ACN, shi da Nuhu Ribadu da Sanata George Akuwam - da ke riƙe da muƙamin sakataren gwamnati a yanzu. Sai dai ya ce Allah ne ke ba da mulki, kuma ya karɓe a duk lokacin da ya so, ...
Shugaba Tinubu zai tafi Saudi Arabia gobe don taron rikicin Gabas ta Tsakiya

Shugaba Tinubu zai tafi Saudi Arabia gobe don taron rikicin Gabas ta Tsakiya

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, tare da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da wasu ministoci tare da wasu shugabannin hukumomi za su bar Abuja a gobe Lahadi domin halartar taron koli na hadin gwiwa na kasashen Larabawa da Musulmi wanda za a fara ranar Litinin 11 ga watan Nuwamba, 2024, a babban birnin Saudi Arabia, Riyadh. Za a yi taron ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, bayan makamancin taron da aka yi a birnin a bara. Taron zai mayar da hankali ne kan halin da ake ciki yanzu a Gabas ta Tsakiya. Mai bai wa shugaban Najeriya shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, shi ne ya sanar da tafiyar a wata sanarwa da ya sanya wa hannu a yau Asabar. Sanarwar ta ce shugaban zai samu rakiyar mini...
Maiɗakin Tinubu ta musanta cewa za ta jagoranci yi wa ƙasa addu’a

Maiɗakin Tinubu ta musanta cewa za ta jagoranci yi wa ƙasa addu’a

Duk Labarai
Matar shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta musanta rahoton da ke cewa za ta jagoranci taron yi wa ƙasa addu'a saboda tarin matsalolin da Najeriya ke fama da su. A ranar Lahadi da ta wuce wani rahoto da aka fitar ya bayyana cewa matar shugaban ƙasar tare da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu za su jagoranci taron kwana bakwai na yi wa ƙasar addu'a kan halin da take ciki. Rahoton ya bayyana cewa Darakta Janar na Taron yi wa kasa Addu'a, Segun Afolorunikan, shi ne ya yi sanarwar a wani taron manema labarai a Abuja, ranar Lahadi da ta wuce. A waccan sanarwar Afolorunikan ya ce taron wanda aka tsara tare da jagororin addinin Kirista da Musulmi, zai buƙaci Allah Ya shiga al'amarin ƙasar kan matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da kuma tsaro....
Kalli Bidiyo: Wata Sabuwa ana rade-radin wani babban dan siyasar Najeriya dan luwadi ne, ya mayar da martani

Kalli Bidiyo: Wata Sabuwa ana rade-radin wani babban dan siyasar Najeriya dan luwadi ne, ya mayar da martani

Duk Labarai
Shahararren dan din din kudu kuma dan siyasa a jihar Legas, Desmond Elliot wanda aka bayyana cewa dan luwadi ne ya fito ya karyata wannan zargi da akw masa. Shafin Gistlover ne ya wallafa sunayen wasu 'yan Fina-finan kudu inda yace duk 'yan luwadi ne wanda lamarin ya jawo hauragiya a kafafen sada zumunta. Saidai a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na TV, Desmond Elliot ya musanta wannan zargi inda yace wasu ne kawai ke son bata masa suna. Kalli Bidiyon jawabinsa anan Yace yana da abubuwa da yawa da yake mayar da hankali akai fiye da irin wadannan gulmace gulmacen da ake yadawa akansa.
Kasar Iràn na son ta tarwatsa Najeriya>>Inji Kasar Israela

Kasar Iràn na son ta tarwatsa Najeriya>>Inji Kasar Israela

Duk Labarai
Jakadan kasar Israela a Najeriya, Michael Freeman ya bayyana cewa, ba a gabas ta tsakiya ba kadai ayyukan ashsha na kasar Iran suka tsaya ba. Yace ayyukan na kasar Iran sun shigo yankin Africa musamman Najeriya. Ya kara da cewa, kasar ta Iran ce ke son ta tarwatsa Najeriya. Ya bayyana hakane ranar Talata a Abuja wajan hada rahoton cikar harin da kungiyar HAMAS ta kauwa kasar ta Israela na October 7. Mutane 396 ne dai kungiyar ta Hamas ta yi garkuwa dasu bayan hare-haren da suka kai inda daga baya suka saki wasu daga ciki bayan shiga tsakani da kasar Amurka da Majalisar dinkin Duniya suka yi. Saidai har yanzu akwai mutane 101 a hannun kungiyar ta Israela. Freeman ya bayyana kasar Iran a matsayin shedaniyar kasa wadda yace tana amfani da karnukan farautarta irin su Hamas...
A yayin da ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa, Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Biliyan 5 wajan gyaran gidan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

A yayin da ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa, Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Biliyan 5 wajan gyaran gidan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Biliyan 5 daga cikin kudin 'yan Najeriya wajan gyaran gidan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima dake Legas. Hakan ya bayyanane a shafin GovSpend wanda shafine dake saka ido kan yanda gwamnatin Najeriya ke kashe kudaden talakawa. Shafin ya nuna cewa gwamnatin ta kashe jimullar Naira N5,034,077,063 a watan Mayun da September dan gyara gidan mataimakin shugaban kasa dake Legas. Hakanan Ministan Abuja,Nyesome Wike shima ya bayyana cewa, zasu kashe Naira Biliyan 15 dan ginawa mataimakin shugaban kasar gida a Abuja.
An kama matashi dan shekaru 19 da ya kàshè dansa me kwana 3 a jihar Adamawa

An kama matashi dan shekaru 19 da ya kàshè dansa me kwana 3 a jihar Adamawa

Duk Labarai
'Yansanda a jihar Adamawa sun kama wani matashi me suna Ali Yaro dan kimanin shekaru 19 bayan da ya kashe dansa me kwanaki 3 kacal a Duniya. Da aka tambayeshi dalili ya bayyana cewa talauci ne da matsin rayuwa ya jefashi yin wannan aika-aika. Ya kwaci danne daga hannun masoyiyarsa me suna Safiya inda ya tafi dashi ya kasheshi ya binne gawar. Lamarin ya farune ranar 7 ga watan Nuwamba, a karin Kwacham dake karamar hukumar Mubi ta Arewa. Budurwar tasa ce dai ta matsa masa akan ya rika kula da ita da dan nata inda a sanadiyyar hakane yasa har ya karbi dan ya kasheshi. Kakakin 'yansandan jihar, SP Suleiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa da cewa shine ya kashe yaron.
Wata Sabuwa: Iyalan marigayi Shugaban sojojin, Lagbaja sun yi zargin cewa kasheshi aka yi

Wata Sabuwa: Iyalan marigayi Shugaban sojojin, Lagbaja sun yi zargin cewa kasheshi aka yi

Duk Labarai
Kanin Mahaifin marigayi shugaban sojojin kasa na Najeriya, Lt. General Taoreed Lagbaja me suna Pa Tajudeen Lagbaja ya bayyana cewa, yana dana sanin sayarwa shugaban sojojin fom din shiga soja da yasan hakan zai yi sanadiyyar mutuwarsa. Wasu Dangin shugaban sojojin sun yi zargin cewa an kashe shi ne ta hanyar tsubbu wanda ya samo Asali daga wani rikicin Fili a mahaifarsa. Kanin mahaifin nasa yace mutuwar data dauki shugaban sojojin, shi ya kamata ace ta dauka. Ya yabeshi a matsayin wanda ya rika tallafawa mutane kowa da kowa.