Thursday, January 16
Shadow

Duk Labarai

ƊAN DUNIYA: An kori mutumin da ake zargi da keta haddin matan aure kusan 400 a kasar Equatorial Guinea daga aiki

ƊAN DUNIYA: An kori mutumin da ake zargi da keta haddin matan aure kusan 400 a kasar Equatorial Guinea daga aiki

Duk Labarai
An kori mutumin da ake zargi da keta haddin matan aure kusan 400 a kasar Equatorial Guinea daga aiki Shugaban kasar Equatorial Guinea Obiang Nguema Mbasogo, ya sanar da korar Baltasar Ebang Engonga daga shugabancin hukumar kula da binciken kudi ta kasar biyo bayan zargin fitar wasu faya-fayan bidiyo na keta haddin wasu matan manyan mutane a kasar. Shugaban kasar ya sanar da nada Zenón Obiang Obiang Avomo a matsayin sabon shugaban hukumar bayan sallamar Baltasar.
‘Yansanda a jihar Katsina sun dakile yunkurin gàrkùwà da mutane inda suka kubutar da mutane 21

‘Yansanda a jihar Katsina sun dakile yunkurin gàrkùwà da mutane inda suka kubutar da mutane 21

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya ta sanar da cewa ta dakile yunkurin garkuwa da mutane a karamar hukumar Jibia dake jihar Katsina inda ta kubutar da mutane 21. Kakakin 'yansandan jihar, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitr ga manema labarai inda yace sun samu wannan nasara ne a aikin da suka yi tare da sojoji da kuma 'yan Bijilante. Yace sun dakile yunkurin garkuwa da mutanen ne a Ka’ida, Unguwar One Boy, da Danmarke quarters duka a Jibia ranar 7 ga watan Nuwamba. Yacw maharan sun kai harinne inda su kuma suka kai dauki cikin gaggawa inda aka shafe awa guda ana bata kashi. Yace 'yan Bindigar sun tsere daga wajan ba shiri. Yace sun kubutar da mutane 16 saidai 5 daga ciki sun samu raunukan bindiga. Yace jami'in Bijilante daya da jami'in hukumar t...
Muna tabbatar da ingancin man fetur din da ake shigo dashi Najeriya>>Gwamnati ta mayarwa da Dangote Martani

Muna tabbatar da ingancin man fetur din da ake shigo dashi Najeriya>>Gwamnati ta mayarwa da Dangote Martani

Duk Labarai
Hukumomin SON, da NMDPRA sun mayarwa Dagote Martanin cewa duk man fetur din da za'a shigo dashi Najeriya sai sun tabbatar da ingancinsa. Hukumomin sun bayyana hakane bayan da Dangote yayi zargin cewa 'yan kasuwar man fetur na zuwa kasashen waje dan siyo man fetur da bashi da inganci cikin kasarnan mai makon su sayi na matatar man fetur dinsa. Dangote dai ya kai 'yan kasuwa da suka hada da A.A Rano, AY Shafa,da kamfanin man fetur na kasa NNPCL kotu inda yake neman kotu ta hanasu shigo da man fetur cikin kasarnan har sai idan matatarsa ta kasa samar da man fetur din. Saidai A.A Rano da AY Shafa sun zargi Dangote da kokarin kare kasuwancinsa.
Sojojin Najeriya sun tabbatar da bullar sabuwar kungiyar ‘yan tà’àddà a kasar

Sojojin Najeriya sun tabbatar da bullar sabuwar kungiyar ‘yan tà’àddà a kasar

Duk Labarai
Mai magana da yawun rundunar Manjo Janar Edward Buba ya ce 'yayan wannan sabuwar kungiyar sun fito ne daga kasashen Nijar da Mali, kuma ya zuwa yanzu ba'a iya sanin manufar kungiyar ba. Buba yace wannan sabuwar kungiyar wadda ta bullo bayan juyin mulkin da akayi a Nijar, ta haifar da matsala a yakin da ake yi da 'yan ta'adda a iyakokin Nijar da Najeriya. Buba yace dakarun kasashen 2 na ci gaba da daukar mataki domin tabbatar da tsaro a kan iyakokon yankin. Idan baku manta ba, a ranar litinin da ta gabata, RFI Hausa ya gabatar muku da rahoto a kan bullar wannan kungiya daga Sokoto. Bullar wannan kungiyar ya dada tabbatar da karuwar matsalar tsaron da ake fuskanta a yankin arewa maso yammacin Najeriya da rikicin 'yan bindiga ya daidaita wajen hallaka jama'a da kuma raba dubban mu...
Farashin abinci ya sauko a jihar Yobe da ke arewacin Najeriya

Farashin abinci ya sauko a jihar Yobe da ke arewacin Najeriya

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wannan dai ana ganin zai rage radadin da jama'ar yankin ke fuskanta, yayin da kasar da ke yammacin Afirka ke fama da hauhawar farashin kayayyaki. Matakin shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu, na cire tallafin man fetur lokacin da yake karbar rantsuwar kama aiki, ta haifar da tsadar rayuwa da kuma tsadar man a sassan kasar.
Osinbajo ya baiwa Tinubu shawarar ya tallafawa talakawa dan ana cikin matsi

Osinbajo ya baiwa Tinubu shawarar ya tallafawa talakawa dan ana cikin matsi

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar ya tallafawa Talakawa saboda ana cikin matsi. Osinbajo ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka gudanar na mata dake harkar kasuwanci. Yace Mata kaso 67 wanda mafi yawancinsu suna Arewa ne basu da karfin tattalin arziki kuma hakan na da alaka da rashin Ilimi. Yace kasar dake da kusan rabin mutanen kasar basu da madogara a rayuwa kuma saboda rashin karfin tattalin arziki akwai matsala. Dan haka ya baiwa shugaban kasar shawarar fito da wani tsari na tallafawa mutane marasa karfi inda yace ya kuma kamata a baiwa bangaren Ilimi muhimmanci sosai.
Obaseki ya ce ba ya fargabar binciken EFCC

Obaseki ya ce ba ya fargabar binciken EFCC

Duk Labarai
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ce ya samu labarin cewa EFCC za ta kama shi da zarar ya miƙa mulki a makon gobe. Sai dai gwamnan ya ce ko kaɗan shi ba ya tsoro ko fargaba domin za a bincike shi a game wa'adin gwamnatinsa, kamar yadda jaridar Thisday ta ruwaito shi yana faɗa a taron EdoBEST da aka yi a Abuja. "Na samu labarin cewa EFCC za ta kama ni makon gobe. Duk inda suka ajiye ni, zan yi amfani da damar domin gudanar da bincike. "Mun yi aikace-aikace muhimmai, sannan mun ba mutanen jihar Edo da abubuwan da suka fi buƙata muhimmanci. Don haka me zai sa in yi fargaba? na yi abin da zan iya yi, amma za su iya zuwa su ci gaba da bi-ta-da-ƙullin da za su yi, wannan matsalarsu ce."
Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kuɗin sama da naira biliyan 500

Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kuɗin sama da naira biliyan 500

Duk Labarai
A jihar Kano, wacce ta fi yawan al’umma a arewacin Najeriya, gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kuɗin shekara ta 2025 a gaban majalisar dokokin jihar. Kasafin kuɗin na bana wanda shi ne na biyu da gwamnan ya gabatar ya kai fiye da naira biliyan 500B. Duk da kasancewar jihar cibiyar harkokin kasuwanci amma ta na sahun gaba wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, abin da ya sa gwamnati ta ware fiye da kashi 31 na kasafin ga ilimi. Ma'aikatu da kuɗin da aka ware musu: Ilimi: Naira biliyan 168.4 (kashi 31%) Lafiya: Naira biliyan 90. 6 Sufuri: Naira biliyan 12. 2 Harkokin noma: Naira biliyan 21.03 Albarkatun ruwa: Naira biliyan 27. 23 Samar da ababen more rayuwa: Naira biliyan 70.78