Jadawalin Manyan ‘yan bìndìgà shida da aka kàshè lokacin Tinubu
A daidai lokacin da ake fargabar mayar da hannun agogo baya a ƙoƙarin daƙile matsalar tsaro a arewacin Najeriya, wasu na ɗiga alamar tambaya kan me ya sa ake kwan-gaba-kwan-baya a yaƙin.
A tsakanin watan Maris zuwa watan Afrilu, an fuskanci hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya, waɗanda ake zargin tsagin Boko Haram na ISWAP da kaiwa, ciki har da waɗanda suka kai sansanin sojoji.
Wannan ya sa masana suke ganin lamarin na da ɗaga hankali musamman ganin ƴan ƙungiyar suna amfani da jirage marasa matuƙa, sannan suna amfani da nakiyoyi da suke birnewa a ƙasa.
Haka kuma masana suna ganin raba hankalin sojojin da suke aikin yaƙi da matsalolin tsaro ya taimaka wajen kasa daƙile matsalar, domin an kwaso wasu manyan makamai da ma sojoji daga arewa maso gabas, aka mayar da su arewa ...







