Thursday, January 16
Shadow

Duk Labarai

Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara turawa mutane bashin Naira Miliyan 1, karanta yanda zaku nema

Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara turawa mutane bashin Naira Miliyan 1, karanta yanda zaku nema

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, ta fara turawa mutane bashin Naira Miliyan 1 da aka nema a baya. Bashin dai ana bayar dashi ne ga mutane wanda kamfanoninsu ko kasuwancinsu ke da rijistar CAC. Gwamnatin tarayya ta ware Naira Biliyan 75 dan baiwa mamfanoni ko kasuwanci masu rijista bashin Naira Miliyan 1 kowannensu. Bashin dai baya bukatar ka bayar da jingina saidai akwai kudin ruwa na kaso 9 cikin 100. Ana bayar da bashinne ta hanyar bankin Bank of Industry. Babban me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar samar da ayyuka da kananan masana'antu Temitola Adekunle-Johnson ne ya bayyana haka a yau Laraba. Tuni dai aka fara wannan shiri a jihohin Ogun, Bauchi, Enugu, Kaduna.
Ya kamata Gwamnonin Arewa su canja matsaya akan kin amincewa da kudirin dokar Haraji da Shugaba Tinubu ya kawo,abu ne me kyau da zai karawa gwamnati hanyar kudaden shiga>>Inji Sanata Shehu Sani

Ya kamata Gwamnonin Arewa su canja matsaya akan kin amincewa da kudirin dokar Haraji da Shugaba Tinubu ya kawo,abu ne me kyau da zai karawa gwamnati hanyar kudaden shiga>>Inji Sanata Shehu Sani

Duk Labarai
Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna ya bayyana cewa, yana jawo hankalin Gwamnonin Arewa da su canja matsaya akan kin amincewa da kudirin gyaran haraji da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ke son yi. Yace kudirin abu ne me kyau da zai karawa gwamnati hanyoyin kudaden shiga. Sannan yace yana baiwa Gwamnonin shawarar su karanta kudirin dokar dan su fahimceshi. Sanata Shehu Sani dai ya bayyana cewa, babu inda aka ce za'a kara yawan harajin da ake karba a kudurin kuma babu inda aka ce kudirin zai sa a samu raguwar ayyukan yi ko kuma cutar wani yanki na kasarnan. The Tax reform Bill is not inimical to the North or any part of this country.Its in fact economically beneficial and fair to all parts.People should keep aside sentiments and read the Bill carefully.Its a comprehensive and...
Dogarin Sanata Barau Jibrin ya rasu

Dogarin Sanata Barau Jibrin ya rasu

Duk Labarai
Sanata Barau I. Jibrin yayi alhinin rasuwar daya daga cikin hadimansa me suna Corporal Barde Nuhu da ya rasu a hadarin mota. Corporal Barde Nuhu ya rasune a yayin da yake kan hanyar zuwa gida jihar Naija dan ganawa da iyalansa. Yana kan hanyar zuwa Kauyen Shata ne dake karamar hukumar Bosso a jihar ta Naija yayin da hadarin ya rutsa dashi. Sanata Barau a sanarwar da ya fitar ta bakin kakakinsa, Ismail Mudashir yace Barde hazikine sosai wajan aiki. Yace yana mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin da kuma hukumar 'yansandan Najeriya.
Hoto: Davido ya nuna yanda yayi zabe a kasar Amurka, Saidai ‘yan kasar Africa ta kudu sunce karya yake a bola ya dauki kuri’ar yayi hoto da ita dan ace shi dan America ne

Hoto: Davido ya nuna yanda yayi zabe a kasar Amurka, Saidai ‘yan kasar Africa ta kudu sunce karya yake a bola ya dauki kuri’ar yayi hoto da ita dan ace shi dan America ne

Duk Labarai
Shahararren mawakin Najeriya, Davido ya nuna kuri'arsa bayan yayi zabe a kasar Amurka. Saidai lamarin ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta. Yayin da 'yan Najeriya ke yaba masa, 'Yan kasar Africa ta kudu kuwa zolayarsa suke inda wani yace karya yake a bola ya dauki kuri'ar ya dauki hoto da ita kawai dan yayi karya.
Najeriya ta kashe Naira Tiriliyan 4.4 wajan biyan bashi

Najeriya ta kashe Naira Tiriliyan 4.4 wajan biyan bashi

Duk Labarai
Babban bankin Najeriya ya nuna cewa,Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Triliyan 4.4 wajan biyan bashi a watanni 3 na biyu na wannan shekarar watau tsakanin watannin April, May da June. Jimullar kudaden da gwamnatin tarayya ta kashe a cikin wadannan watanni 3 Naira Tiriliyan 6.8 ne gaba daya wanda daga ciki ne aka cire Naira Tiriliyan 4.4 aka biyawa Najeriyar bashi watau dai Naira 2.4 ne suka yi saurawa gwamnati ta gudanar da sauran ayyukan kasa dasu. Hakan na nufin kaso 64.7 cikin 100 ne gwamnatin ta kashe wajan biyan bashi daga cikin kudaden shigarta. Hakan kuma na nufin Najeriya ta kashe fiye da abinda take samu a tsakanin wadannan watannin. Jimullar bashin da ake bin Najeriya dai ya kai Naira 121.67.