
Gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya na taro kan tsaro a yankin
A ranar Litinin ɗin nan ne gwamnonin shiyyar arewa maso gabashin Najeriya suke taro a birnin Damaturu babban birnin Jihar Yobe kan matsalolin da yankin ke fama da su.
Taron na zuwa a daidai lokacin da yankin ke fama da sabin hare-haren mayakan Boko Haram.
Masana da al'ummar yankin na cewa dama ce gwamnonin suka samu domin tattauna yadda za a shawo kan matsalar tsaro da ke addabar yankin.
A ranar Talata ne dai ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kai wani harin bam da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 26 a Rann a jihar Borno.